New Post

ABUBUWA BAKWAI (7) ABIN KULA GA DAN'ADAM

1. Duniyar da za a barta, me ya kawo hadama? 2. Dukiyar da za a lissafa daya bayan daya, me ya kawo tarata? 3. Rayuwar da zata kare, ina wani farin ciki? 4. Yarintar da tsufa zai zo mzta, me ya kawo takama? 5. Ana sauraren mutuwa, ina wata walwala? 6. Jikin da zai zama gawa, me ya jawo dagawa? 7. Karshe dai makomarsa kabari, me zai sa alfahari? Wanda ya manta da wadannan a ina ya bar hankalinsa? Allah yasa mu dace, yayi mana kyakkaywan karshe. Ameen!

KADA KA RAMA CUTA GA WANDA YA CUCEKA!

Kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka, kai kayi hakuri. Zaka samu abu biyu sakamakon hakan; * Na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. * Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

KADA KA BARI ZUCIYARKA TA ZALUNCEKA!

Kada ka sale zuciyarka ta zalunceka, tabbas zaluncin zuciya ga gangar jiki yake komawa, idan akayi wasa ya zamanto ya shafi rayuwa. Assasa bak'in tunani, yawan zargi da rashin tabbas akan wani aiki, zato, shakku ko kokwanto akan wani al'amari batare da tantance gaskiyarsa ba, shine zaluncinzuciya akan dan Adam. Maza ka hana zuciyarka don akwai hadurra dubu akan hakan.

MAHAKURCI MAWADACI

Tabbas ba kowane dandanon magani ne ke da dadi ba, amma babu shakka shine abu mafi dacewa ga dukkan mara lafiya. A lokuta da dama rayuwa takan dakeka da guduma ta jefaka acikin wani mawuyacin hali, kayi ta fama amma tayi maka tutsu. Amma idan kayi hakuri sannu ahankali zata kwaranye. Hakika ba duk abinda rai yake so yakan samu ba, amma bukata bata taba sauyawa ba kuma bata taba karewa ba. Don haka ka shirya bukatunka da kyau ka bisu daya bayan daya sannu a hankali, kayi gwa- gwarmaya, sannan kayi juriya. Tabbas mafarkinka zai zama gaskiya.

KO KA SAN?

Rayuwa bakin alqalami ce tana bukatar kaifi sannan tana son tsini. Kaifin don ka yanki magauta, tsinin kuwa don ka soki makiya. Haka zalika rayuwa kamar randar ruwan sanyi ce ta kasa tana bukatar tanaji da adani, kodn wata rana ka shayar da masoyanka. Da kyau ka lura da abu biyu a rayuwa; 1. Ka lura da mai zaginka mai aibantaka wata kila wata rana zai iya zama masoyinka mai yabonka 2. Ka lura da masoyinka na kusa mai yawan ambaton alkhairinka, wata kila wata rana zai iya zama makiyinka mai zaginka.

Friday, 26 May 2017

YAR MAFIYA 21

�� *'YAR MAFIYA*��
Sanah S Matazu
Rash Kardam.
*21*
Kwanci tashi suka gama zana jarrabarwarsu masha Allahu komai lafiya aka sallamesu suka koma gidajansu zaman jiran sakammako.
Tsakanin Najwa da Yasiraht kuwa abun yakai intaha domin ta zame musu karfan kafa, tun dawowarta gida Samari kemata tururuwar zuwa amma babu wanda take saurara sai Samar shi kadai kawai ta bawa gurbi a zuciyarta.Kwatsam tai karo da soyayyar Muhseen dan aminiyar mahaifiyarta, lokaci daya ya kwanta mata a zuciyarta nan da nan suka amincewa juna ta tattara Samar ta watsar hakan yai bala'in kona ran Samar ya rasa hanyar da zai bi dan kauda Yasiraht ganin babu dama sai ya soma bibbiyar Muhseen.....

Muhseen da daya ne tilo tsoka guda a miya ga Alhaji Lawali mai akwai, asalin mahaifinsa bafulatanin garin Kurfi ne mamansa balarabiyar Egypt hakan yasa Muhseen ya dauko kyau gaba da baya kyakkyane na gaban kwatance.Tun tasowarsa bai san kwaba ba balle harara sangartacan yarone kaf karatunsa a waje yayi hakan yasa ya budi ido da harka da Mata over.Ko kadan mahaifansa basa son laifinsa, yasha yiwa yaran jama a cikkuna da fyade.Tunda Samar ya gama gano waye Muhseen ya cika da farin ciki domin ya samu hanyar gumawa Yasiraht a sadaka.Hanya ta farko daya soma bi neman shiri da Najwa nan da nan suka koma kamar da sannan ya bijiro da bukatarsa dake tayi shirin fansa babu jinkirtawa ta amsa bukatarsa nan da nan ta soma shirin fuskantar matsalar.
Ranar Asabar da yammaci Muhseen ya fito daga Shanawa club, harya gota tarin wasu gun-gun matasan yan Mata ya hangi Najwa a gefe tana taunar cingum daga ganinta babu musu ya tabbatar yan good evening ne in kiya yai mata sarai ta gani sun hada ido ta kanne ta cigaba da hidimar gabanta.Bai yi kasa a guiwa ba ya karasa da fari ta kalleshi ta watsar, daga bisani tabi yarima akasha kida basu wani jimaba ya ribaceta yajata cikin club din ya kama mata daki.

Tsayin kwanaki uku suna tare, Najwa na hillatasa ko kiran Yasiraht bata bashi damar yi ranar kwana na uku ne ta samu suka fita yawo tare, cikin ikon Allah sukaiwa JIFATU tsinke anan sukai kici6us da Yasiraht,Najwa ta kalleta ta watsar Muhseen kuwa ko kallonta bai yi ba a haka suka gama siyayyarsu suka fita suna tayar da mota da gudu tai wa motarta key wadda ta aro wajan Yasar ta rufa musu baya.

Tunda Najwa ta hangi tahowar Yasiraht tai wa Muhseen wayau ta amshi tukin, tuki suke na fitar hankali ko gabansu basu duba a haka sukaiwa cikin gari nisa.Najwa ta saki murmushi ganin tarkonta ya kama kurciya.Cikin rashin zato tai ribos motarta tayo baya take motar Yasiraht ta wuntsula ta kife ta kama hayaki bata hakura ba tasake turata tai gaba ta fada rami ta kama da wuta.Tai juyi taja motar  tana kallon Muhseen tana murmushi wanda yakasa hanata kudurinta.Sunyi tafiya mai nisa sun shigo gari ta shammaci Muhseen ta nufi wata katuwar mota cikin hanzari ta danna zobanta ta bace take motar ta murkushe Muhuseen sai gawa.Tana daga gefe tana kallon mutane kowa na budurunsa, nan da nan tabar wajan.Batai nisaba taji jikinta na shock, tsoro ya shigeta tuni ta bayyana wajan motar Yasiraht.

Gabanta ya tsananta faduwa lokacin da tai arba da Samar,idonsa jajjur yana huci kamun tai wani yunkuri ya kaimata cafka ya dinga azabtar da ita tana ihu, ihun tane ya farkar da Yasiraht daga dogon suman da tayi.

Murmushi ta saki lokacin da tai arba da Najwa nacin azaba wajan Samar kafin su farga ta bace bat, wani hadiminsu tasa ya dauko mata motarta zuwa kofar gida da dingishi ta shiga gidan, nan ta riski tashin hankali labarin mutuwar Muhsun.Kara ta saki ta zube a sume.
Sanah
Rash

YAR MAFIYA 20

�� *'YAR MAFIYA....*��

*Rash Kardam*
        *Sanah S Matazu*
*N. W. A*
Page
*20*

Cikin salon tsafi da sihiri Yasiraht tayi gir-giza ta dawo wani irin hallita kamar kada ta tayi kan Shany gadan-gadan, Shany ta ciro sanda tsafinta ta nuna kadar amma ina sai sandan da ya narke ya koma ruwan wuta ya zube a k'asa Yasiraht ta fashe da wani matsanacin dariya bakin ta yana fitar da aman wuta sai hayaki yake yi ta ce“kee Shany ai kun makara don yanzu sai kun raina kan ku sai kunyi nadaman jawoni cikin ku do  zan zame muku k'adangare bakin tulu hahahaha!!!…".

Ta kece da dariya sai da tayi mai isarta ta tun k'aro Shany tana fesa wuta a bakinta Shany ta soma ja da baya Yasirah ta yi wasu surkule ta ke wajan yasoma juyawa Shany tasoma ihu, Yasiraht ta na isowa ta fara fesa mata wuta Shany na ihu sai da ta bata wahala tukun ta kece da dariya ta ce“Shany ba zan kashe ki yanzu ba sai na baki d'an lokaci ki kuma kai ma Najwa labari in har ta kuskura tashiga gonata to sai wata ba ita ba".

Yasiraht na gama fad'an haka ta b'ace bat Shany jiki ba kwari ga shi duk taji ciwo zobenta ta murza take itama ta b'ace sai a gidansu Najwa ta bayyana.

Najwa duk tayi kuka har ta gode ma Allah masu aikin gidan ta kira ta shaida musu mutuwar kakanta a dare aka gyarata aka mata wanka washe gari da safe aka mata sallaha aka kai ta makwancinta Najwa duk ta dawo wani iri ta na tunanin kalan fansan da zata d'auka Shany ta bayyana a hankali ta taka har zuwa kusa da Najwa ta dafata nan ta soma bata hak'uri ta kuma shai da mata abunda ya faru wani gwauro numfashi ta sauk'e a fili Najwa ta furta “tabbas Yasirah ta mana nisa amma ko ta halin k'ak'a sai na rama sai na d'au fansa. A haka akayi kwana bakwai tukun Najwa suka soma shirin komawa makaranta.

Yasirah tana b'acewa bata bayya na ko ina ba sai cikin dajin makarantansu tana dariya nasara wai ita ke da wannan zobe da matsafa da dama duke nimansa sai da ta sai ta kanta tukun ta koma cikin hostel.

Najwa ko da ta dawo tana bibiyan Yasirah amma a b'oye don yanzu Yasirah tsoro take bata ko a gun mitin Samar yanzu yana d'an shakkar Yasirah don yanda take da zoben hannuta.

A haka su Yasirah da Najwa suka fara jarabawansu ta gama makarantar gaba da primary yanzu Yasirah ta samu 'yanci gashi duk ranan mitin sai ta kawo musu tun d'aya ko biyu an shayar da jininsa.

Ku biyo mu.

Tuesday, 9 May 2017

'YAR MAFIYA...19

�� *'YAR MAFIYA*��

Sanah S Matazu
   Rash Kardam.
*N.W.A*
Page
*19*
Bakinsa ya cigaba da rawa tamkar mazari, tilas ya hakura zuciyarsa na kuna tamkar garwashi a haka aka dauki Yasmin zuwa gida akai mata sallah zuwa makwancinta. Yasiraht kwananta uku a asibiti duk ta kade ta rame tamkar mai cutar wata da watanni. A haka suka koma makaranta zuciyarta cike da kudurin daukar ransa.

Tun komawarsu take neman hanyar fanshewa, kwatsam ranan tana zaune ta nufi kafteriya cin abinci ta tsinkayi muryar Najwa tana bawa Shany labarin daya faranta zuciyarta.
"Walahi shany inason kakus, dole in je jos yau cikin dare in ga lafiyarta, ita kad'ai ta ragemun bani da kowa"."Gaskiya ya dace ki dubota Najwa ko zan rakaki? " "a'a ta fada cikin ci da zuci. Cikin sauri Yasiraht ta yi baya tana murmushin mugunta zuciyarta wasai. Tun daga lokacin take bibbiyar motsin Najwa har dare ya tsala misalin daya taga fitowar wata katuwar tsuntsuwa daga hostel dinsu take tai girgiza ta rikida zuwa suffar tsuntsuwar sama ta lula tabi Najwa.

Cikin tsananin gudu suke keta gajimare, tsafi gaskiyar maishi cikin awa daya zuka isa garin tafiyar awa hudu a awa guda lallai sai tsafin. Yasiraht ta samu waje ta labe a tsakar gidan tana hangen Najwa ta koma ainihin suffarta ta shiga wani kayatacan fallo ta ratsa zuwa bedroom gidan ya kawatu komai akwai can ta hangi Najwa na neman kurewa ganinta sai ta rikida zuwa suffar wata mage data hanga a harabar gidan tai wuf ta fada dakin baccin ta window ta riga Najwa shiga tai kwance jikin tsohuwar tai linkim.

Da hanzari Najwa ta shiga jin motsi sai dai bata ga komai ba idanunta sukai wani haske walai tauuuu!  Tai jim tana karewa magen kallo ta saki ajiyar zuciya ta shafi kafaffun tsohuawar.
Mikewa Dattijuwar tayi, tana mutsittsika ido tai murmushi"yar Momah kece yanzu a daran nan,ban hanaki tafiyar dare ba? ""Momah so nake in ganki shiyasa nazo amma da safe zan wuce gida koma ki kwanta nima ruwa zan watsa".Komawa tai ta kwanta tace"Pussy na nan da halin ta nanike jikinki?" bata tanka ba ta kwanta Najwa tai waje tana fita harabar fallon gabanta ya fadi, ta dake kawai karaf idonta yakai kan Pussy kwance tana baccinta da yayanta uku.Cikin tashin hankali gabanta ya doka das!  Tai sashin Momah da gudu, turus ta tsaya sakammakon ganin Yasiraht da wuka tana digar da jini ta kyalkkyale da dariya tace "fansa Najwa jinin Yasmin 'yantace ne".

Sama da kasa ta nemi Yasiraht ta rasa,durkushewa tayi tana gunjin kuka kamar mahaukaciya ta mike tai girgiza tana wasu surutai.cA firgice ta bayyana tsakiyar dakinsu tana rangaji Shany ta mike tana jijjigata Emeka na gefe tana dariya a ranta tace"ai dama na fada Najwa sai ta fitineku" lallabawa tai ta fice daga dakin ta nufi mahadarsu riskar Najwa tayi tana numfashi ta dafa kafadarta. Bata juyoba itama bata damu ba"sannunki jaruma, ga wannan zoban ki saka ko Samar bai isa ja dake ba balle Najwa asalin zoban na kakana ne".Cikin sauri ta warci zoban tasaka wata kara Emeka ta saki Yasiraht na juyawa taga Shany ta dabamata wukar tsafi ta fadi mataciyya "karshan maci amana kenan" Shany ta furta.

Ku biyo mu

'YAR MAFIYA..18

�� *'YAR MAFIYA....*��

*Rash Kardam*
        *Sanah S Matazu*
*N. W. A*
Page
*18*
Yasar yayo kansu cikin rud'ewa ya d'aga Yasmin ganin yanda jini ke zuba wasu mutane ne suka taimaka masa suka d'aukesu sukai mota cikin rudu ya shiga ya ja motar suka nufi T.H ko da sukaje emergency aka shiga da su likitoci sun dad'e akansu kafin babban su ya fito fiskansa ba alamar murmushi, Yasar ya taso da sauri yazo gun Likitan ya ce"Likita ya jikin su jinin da ke zuban ya tsaya?". Cikin sanyin jiki Likita ya dafa Yasar ya ce"Babban ta farfad'o yanzu haka". Yasar ya ce"Alhamdulilah!". Likita ya sake duban Yasar ya ce"kai musulmi ne kuma ko da yaushe ana so musulmi ya kasance mai hakuri da juriya da amsan kaddaransa, sannan Ubangiji yana mana kyauta wanda zamu saba mu shaku da kyautarsa rana d'aya shi da yafi muson abunsa sai ya d'auke".

Likita ya nisa ya cigaba da ce wa"inason kayi hakuri Allah yayi rasuwa ma k'araman...". Take bakin Yasar yasoma b'ari ji yayi duk wani hanyan tafiyan jininsa ya tsaya da aiki kujeran da ke gefen sa ya zauna tare da furta"Innalilahi wa inna ilaihi raji'un ya Allah ka jik'an Yasmin". Sai da ya d'au mintuna likita na kwantar masa da hankali kafin ya ciro waya ya sanar da su Abba suna Asibiti yazo yanzu.

Jikin Yasar a sanyaye ya ce"Doctor zan iya shiga na gansu?". Doctor ya ce"eh ba matsala zaka iya shiga". Da kyar Yasar ya iya d'aga k'afarsa ya shiga d'akin gun Yasmin ya nufa ya sanya kunnesa a k'irjinta yaji ba alamar numfashi ya d'aga hannuta ma haka ya saki jikinsa a sanyaye yana furta"Innalilahi wa inna ilaihi raji'un". Ya juya gadon da Yasiraht ke kwance nan ya ga idonta  a rufe amma tana wasu surutu a hankali wanda sai ka kai kunneka kusa da bakinta ka iya jin mai take fad'a.

Da sauri ya isa gadon ya sunkuya dai-dai bakinta ya ji tana fad'i " bazan tab'a yarda ba ku bada jinin Yasmin d'ina, Najwa kece jagoran d'auko ta har ki yanka ta da hannu ki to tabbas sai na d'au fansa da ga yau ba mutunci a cikin k'ungiya yanda kuka bada jinin Yasmin ma dodon tsafi duk wanda yake da hannu a cikin abun sai yayi na dama sai na fitini kowa a k'ungiyan nan wannan alk'awari na d'auka ma.

Abba ne suka shigo Hajiya Nafisatu sai kuka takeyi a asai likita ya musu bayani a waje suna shigowa Yasar ya d'ago da sauri ganin su Abba ne ya niyyan fad'a musu Yasiraht ce tayi sanadin mutuwar Yasmin take bakinsa ya rik'e ya kasa furta komai sai b'arin da bakin ke yi.

Ku biyo mu

'YAR MAFIYA..17

�� *'YAR MAFIYA*��

Sanah S Matazu.
Rash Kardam
*17*
Haka Yasiraht ta cigaba da rayuwa tsakanin mafarki da zahiri, a haka suka gama jarrabawar gwajin shiga aji shida sukai hutu suka koma gida. Komawarta gida babu abinda ya ragu tsak'aninta dasu Samar kullum iyayanta na ganinta amma da zarar dare yayi Samar kan zaagayo ya d'auketa.

Tsakanita da Yasar kuwa babu jituwa ko kad'an,shi yana mata kallon azalluma ita kuma kallon ya takura mata. Hakan ya jawo sab'anin ra'ayi sossai tsakaninsu ko gun cin abinci sun dingi fad'a kenan tamkar mage da kare a haka taci hutunta saura sati biyu ta koma wani mummunan lamari ya auku gareta wanda ya tsaya mata arai.

Kwance suke kan makeken gadon da yake mallakinta.Tun dawowarta tare suke kwana da Yasmin, misalin k'arfe biyu na dare Samar ya bayyana a gefan gadon yana murmushi. Gabanta ya tsananta fad'uwa ta aro juriya ta yafa ta kalleshi. Murmushu sukai wa juna cike da tsantsar kulawa. Bai wani d'auki lokaci ba ya dubeta"Yasiraht zuwa nai in gaya miki muna buk'atar jinin Yasmin nan da gobe kiyi tunani". A fusace ta mik'e "ban yadda ba Samar" "ba damuwata bace yardarki ko akasinta".Fu! Ya bar wajan yana huci.

Washegari haka ta yini sukuku da'ita babu abinda take asassawa kanta Hajiya Nafisa ta lura da yanayinta tai ta janta a jiki amma bata gaya mata damuwarta ba. Yasar ne ya daukesu zuwa shooping bayan magarba suka nufi hanyar G.R A Cikin nutsuwa yake tuk'in har suka k'arasa, kwata-kwata hankalinsu nakan siyayyar da suke yi sai jin k'arar Yasmin sukai ta fad'i ta kakkafe jini na bin kofiffin hancinta. Karaf ta hangi wulgawar Najwa ta bacewa ganinta, wata giggitafiyar kara ta saki tai kan Yasmin bata ko numfashi take Yasiraht ta zube sumammiya.

Ku biyo mu

'YAR MAFIYA..16

�� *'YAR MAFIYA....*��

*Rash Kardam*
        *Sanah S Matazu*
*N. W. A*
Page
*16*
Ganin Najwa a hannu Samar yasa Yasiraht ta sakar masa wani shu umin kallo ta b'ace, bata bayya na a ko ina ba sai a bayan hostel d'insu  gindin bishiyar d'aurawa ta zauna ta had'a kai da gwiwa tana kuka mai tsuma zuciya sam ta rasa mai yasa take jin wani abu game da Samar duk lokacin da ta gansa da Najwa sai ta ji zuciyarta na mata zafi. Labb'an bakinta ta ciza a fili ta ce"Najwa ni Yasiraht sai na koya miki hankali duk wani hanyan da zan bi na nuna muku kwarewa ta sai nabi kuma sai na fitini kowa a gun sai na zama mai bada umarni abi nice nan zan dawo mai jiran kujeran Samar". Murmushin mugunta ta saki sai kuma taci gaba da kuka.

Najwa tana far-fad'owa ta ganta hannu Samar sai taji sanyi a zuciyarta tazo juyawa taji wuyanta ya rik'e sai da ta saki k'ara kad'an Samar cikin sauri ya k'ara rik'e ta tukun ya fara wasu surkulle sai ga kwarya ya bayyana a gabansa nan take ya sanya hannusa ya d'ebi garin magani ya shafa mata tare da wasu sirutai wanda ba musan ko na miye ba take waje ya goge kamar ba ta tab'a jin ciwo ba Najwa sai murmushi takeyi fiskanta d'auke da annuri yau tana jin wani sanyin dad'i ya mamayeta wai ita ce a hannu Samar lalle yau jin kanta take tafi kowa, cikin yanga ta mik'e tare da zuwa kusa da Samar ta tsaya sai da ya aika tama da kalon mai d'auke da tuhuma kafin ya ce"Najwa mai yasa bakiji na ce ki fita a hark'an Yasiraht amma kin k'i ji kinga irin ta nan ko in baki mai da hankali ba zata fara mayar miki da martani kaman yanda tayi yau". Najwa ko ajikinta bata kuma ce da shi k'ala ba sai murmushin da takeyi nan ran Samar ya k'ara b'aci take ya bada umarni da a watse a mitin d'in yana gama fad'a ya bace...

Bai bayya na ko ina ba sai gun da Yasiraht take ta had'a kai da gwiwa tana kuka a hankali Samar yazo ya dafa ta a hankali Yasiraht ta d'ago idonta tab da hawaye cikin sanyin murya Samar ya ce" Yasiraht ki dai na kuka ban son ganin hawayenki na zuba ko kad'an". Cikin fushi ta d'ago dara-daran idonta da sukayi ja ta sauk'esu a kansa da niyar masifa amma sai me kwarjininsa yasa ta fasa Samar ne ya sanya hannusa ya share mata hawaye ya rik'o hannuta suka mik'e tsaye suka nufi hanyan hostel.

Sai da ya kai ta har d'aki ya rarrasheta suna tad'i har tana dariya kafin ya tafi, tun daga wannan rana Yasiraht ta soma canza salo don Najwa bata isa ta tab'ata ba ta share ga salon tsafi da sihirin da Yasiraht takeyi abin har na ba ma Najwa tsoro kuma ko a gun mitin nan danan zakaji ta kawo mutane hakan yasa suka k'ara girmamata.

Ku biyo mu

'YAR MAFIYA..15

�� *YAR MAFIYA*��
Sanah S Mstazu
    Rash Kardam
         *15*
Cikin fushi yake nunata da yatsa, "wato Najwa bakya jin magana ko?  Ina kaucewa sab'amiki kina k'ok'arin k'untatamin to walahi zanyi maganinki".Wata giggitaciyar dariya ta saki, tana hucci mai zafi ta dubeshi.
"Samar ni zaka wulakanta saboda ina bibbiyarka?Walahi kabani mamaki k'warai da gaske, zan nuna maka sharin mace sai kayi nadamar cin amanata".....bata k'arasa ba ya nunata da hannu tuni wani sirririn haske kore ya fito ta tsintsiyar hannunsa ya daki fuskarta take ta saki wata giggitaciyar k'ara data kid'ima dajin.Namun dajin suka dinga gudu suna neman mafaka,yaraf ta zube k'asa babu numfashi.'Daukar Yasiraht ta yi suka bar wajan.

Cikin tsananin gudu suka dinga keta dazzuzuka, a hankali ya sauketa cikin labry d'in ya kama yatsanta yasa mata wani zobe.Zoban yana da tsananin haske in ka kalleshi, jikinsa tambarin kan skelaton ne a jiki daga tsakiya an masa ado da gwal yanata k'yali b'at ya b'ace.A hankali idonta ya soma washewa ta saki ajiyar zuciya kanta yai nauyi sossai a jigace ta nufi hostel saboda gajiya.Turus ta tsaya lokacin data fito, sakammakon ganin d'alibai dandazo guda sun zagaye Najwa cikin galabaitaccen yanayi.

A sanyayye ta karasa wajan tana tambayar abinda ya faru, wata muguwar shak'a Shany ta kawomata wani shock da hannunta ya yi yasa ta sakin Yasiraht bata shirya ba tai baya tana muzurai.Ita dai Yasiraht rakata ta yi da idanu zuciyarta k'war cike mamakin ganin Najwa a wannan yanayi.Take abinda ya faru ya dawo mata, kanta ya sara ras!  Ta dafe ta wuce area d'insu jikinta na rawa.Emeka dake gefe ta kwashe da dariya, cikin gurbataciyyar hausarta tace "yaro bai san wuta ba".

Wani rikitaccen kallo Shany ta aika mata, a daddafe ta wuce hostel  tana zuwa ta zube kan gadonta tana numfarfashi.Ta dafe kanta da yake juya mata sossai, a haka ta yini kwance.Najwa sai da tai kwana biyar kwance sannan ta dawo hayyacinta.

Tun daga lokacin wata gaba ta k'ulu tsakanin Najwa da Yasiraht, kwata-kwata basa ga miciji idan hanya ta had'asu sun dinga hararre-hararre kenan.Abinda yake tada hankalin Najwa yadda duk yadda taso cutar da Yasiraht sai zoban hannunta ya zamo shamaki wajan afkuwar hakan, haka take hakura kiri-kiri kwatsam aka nemesu taron gaggawa a k'ungiya.

Harabar wajan cike take da manyan motoci ababban kalo, abin sai wanda ya gani an kawata fillin ra jajjayan furani da bak'ak'k'e komai na wajan ja da bak'i ne har  kayan jikinsu.A hankali aka soma darewa ana bashi waje yana rik'e da hannunta har suka samu waje suka zauna.Nan aka saki kida sossai taro ya soma gudana, an gama gabatarwa an ci an sha Najwa da Shany na gefe suna kus-kus.Can Samar ya mike ya gabatar da jawabin godiya ga mahallata taron,ya juya yana murmushi ya kali Yasiraht hannunsa ya mika sama yana karanta wasu dalamusan tsafi take wasu kwarre guda biyu suka bayyana kan hannunsa.

Cikin kasaita ya tsareta da ido"karbi kisha" jikinta ko ina rawa yake take ta kafa kai ta hausha wajan ya rude da shewa"kinzama sarauniya!  Kinzama sarauniya!!  Kin zama sarauniya!!! ".Wata giggitaciyar kara Najwa  ta saki tai kanta da wata takobi mai tsananin haske, take Samar ya dakawa Yasiraht tsawa itama tai kanta tana shafa zobanta takobi ta bayyana irin ta Najwa nan da nan wajan ya hautsine sai karar k'arafa kake ji na tashi can Yasiraht tai nasarar yankar Najwa a gefan wuya take ta kwala kara tai lau zata fado kasa. Caraf Samar ya rikota Yasiraht ta diro kan kafafunta tana murmushi ganin Najwa a hannun Samar yasa ta jefa masa wani shu umin kallo ta danna zobanta b'at ta b'ace....

KUBIYO MU.

'YAR MAFIYA..14

�� *'YAR MAFIYA....*��

*Rash Kardam*
        *Sanah S Matazu*
*N. W. A*
Page
*14*
Matsawa tayi kusa dashi Samar kalon yake mata mai cike da so da kauna hannusa ya kalli wani zobuna guda uku a jere manya dasu da kuma rubutu a jiki ta baya kuma alamar kan mutum ne wannan zobe ya danna nan take wani irin hallita ya bayyana a gaban sa tare da rusunawa ya ce"ya shugabana ban umurni na bi". Murmushi Samar yayi cikin k'asaita da mulki ya ce"aljani d'an duguzu ina so ka kai mu dajin k'are dugunka zan huta a gun".

Kafin ka ce mai ta ke gurin ya gauraye da iska nan take Yasiraht ta fara kakkarwa da tsoro nan wata dadduma ta bayyana tare da matasai na alfarma ko da ta duba ta gani d'an duguzu ne ya ke rik'e da dadduman a kansa nan tsoro ya k'ara kamata. Samar ne ya kama hannuta kaman walkiya suka hau kan dadduman nan taga su tsaga bango suka fito gashi tana gani suka wuce mutane amma da alaman su basa ganin su a hankali suka haura sararin samaniya sai keta hazo sukeyi suna tafiya cikin kwanciyar hankali.

Yasiaht ta rasa mai yasa in Samar ya mata magana bata iya masa musu kuma in ta kalli kwayan idonsa yana mata kwarjini bana wasa ba a han kali ta sauk'e sassanya anjiyar zuciya.

Najwa da ta nufo library (gurin karatu) taga wulgawan su Samar nan take wani bak'in ciki ya lulub'eta ga mutane a gun bare ta tanza hallita ta bisu da sauri ta nufi cikin library a girgiza ta dawo wata tsun-tsuwa ta fito daga library ta bisu zuciyar ta na mata k'una sai sake-saken wani irin abu zatayi ma Yasiraht.

Samar suna zuwa dajin nan dadduman ya sauk'o dai-dai bakin ruwa suka sauk'a wani abun ban mamaki ga manyan namun daji suna shawagi a gun ba wanda ya kulasu ko ta inda suke basa bi. Samar ne yasake murza zobe nan wata mata fara da farare kaya ta bayyana ba'a ganin k'afarta sabida fararen kaya ya rufe k’afafunta, ta rusuna ta ce"Ranka shi dad'e 'Dan Sarkin Matsafa jikan matsafa mai kake buk'ata a maka sai da ya d'au lokaci kafin ya ya ce"kayan marmari nake buk'ata". Kafin kace me  wani tire na alfarma kamar na zinari sai kyalli yakeyi tare da d'auke ido kayan mar-mari aciki irinsu Tuffa(Apple), Inabi Ayaba, Abarba, d.s.s.

Yasiraht sam tak'i ci Samar ne ya ce"bazaki ci ba ko sai na baki ya d'auko yankake tufa zai sa mata a baki kawai suka ga wani irin abu ya tun k'aro su da gudu ya buge Yasirah ta fad'i k'asa, nan abun ya fito da wani tsini da niyar zuwa ya cakka ma Yasiraht a cikinta, cikin sauri Samar ya bud'e hannusa sai ga wani sanda ya fito da sauri ya nuna wannan tsun-tsuwar sai ga Najwa ta dawo halittanta na asali ta fad'i a gun tana mai da nufashi. Cike da mamaki Samar ke kallonta a hankali ya tako zuwa inda Yasiraht take ya d'agata tukun ya kalli Najwa nan yaji wani haushinta ya kamasa a hankali yasoma takawa zuwa gun Najwa cikin fushi.

Sanah
Rash
Ku biyo mu.

'YAR MAFIYA...13

�� *YAR MAFIYA* ��

Rash Kardam.
  Sanah S Matazu.
*N.W.A*
   Page
    *13*
Kwanakin Yasiraht uku a gida gaba d'aya hankalinta ya soma tashi saboda mafarkan da take yi tare da tsoratata da ake yi. Kwata-kwata yanzu kallon mudubi ya gaggareta saboda zahiri in ta kalli mudubi mugayan gane-gane take yi. Ahaka suka cinye kwanakin su suka koma makaranta,sai dai tunda suka koma ta fuskanci canje-canje daga gun Najwa sossai ko harkarta bata shiga balle magana me tsayi ta had'asu.

Kwatsam ranar Juma'a da azahar sun dawo masallaci, taga shigowar k'awayan Najwa su uku bayan su Najwa ce d'aya bayan d'aya ta kallesu Shany ce 'yar asalin garin ebira sai Merry ita kuma Ibadan sai kuma Emeka 'yar Undo bata tanka ba ta cigaba da bibbiyar littafin dake hannunta fizgar littafin yasata d'agowa kafin tai magana Emeka ta tsinkamata mari. Najwa tai murmushi ta jin-jina hannu alamun jin dad'i Yasiraht kasa magana ta yi suka kad'a kai sukai waje, ranar yini ta yi sukukku ko karbar abinci bata je ba.

Wata sabuwa sai Najwa ta tsiri sata aiki hakan yana bata mamaki matuk'a,amma babu yadda zatai ta fahimci hata Malamansu shakarta suke. Kwatsam rana nan tana zaune a labry tana karatu, ta jiyo shewar su Najwa can taji sautin Emeka"ke wai ya kuka yi da prince a kan tsamin yarinyar can?"."Hmm! Kedai bari sisty Samar na neman had'awa kowa jalalla walahi zanyi sanadin tona asirin k'ungiya saboda Yasiraht, shekaruna nawa tare da shi han samu matsayin da yake son d'orata ba sai ita daga zuwanta. Wace wuya ce banci ba wajan kawota duk zatona zan samu matsayin da take kai amma shi ne zai rainamun wayau? ".

"Laifin kine".
Cewar Shany, cikin k'ufula ta furta"kamar ya laifina ban gane ba walahi? ".
"Hmm! Nagaya miki kawai mugama dashi kin wani tsaya ja mana rai, wai ke so ai sai ki ci so bagara ku biyu babu ba ko kigama da Yasiraht d'in".
"Keeeee!  Dakata in gama da Samar? Wa zan kama? " Ta fad'a a zafaffe itama cikin zafinta ta maida martani.
"Ki kama sabon zuwa".
Kyakkyawan mari ta shimfid'amata, ta cigaba"saboda baki da mutunci Samar din zan gama da shi? Kin san waye shi a gareni? ".
"Waye fa Najwa?  Banda wanda ya samu a hanyar banza ya cuccuce mu ko kin manta Samar ne yasa kika bada jinnin mahaifanki duka biyun ga doddon tsafi? Kin manta shi yasa kika rasa masoyinki na gaskiya kika bada k'annanki har uku ki gayamun yanzu wa kike dashi a danginki da zaki nuna matsayin jininki duk Samar ya k'arar da su.Shi ne kike so itama Yasiraht ta fad'a, to kisani ada ina tare dake,amma a yanzu nayi d'amarar janye muku zan kasance tare da Yasiraht kun yi galabar kawota cikin ku amma sai nayi sanadin da zata zame muku masifa dalilin marin da kikai mun bana yafiya".

Fuuuu! Tabar wajan, kan Yasiraht yai nauyi tanasan gasgata batun Emeka ta kasa, kawai saita shasshantar da batun ta cigaba da abinda take.Kamar almara Samar ya bayyana yana murmushi,cikin tsoro ta soma da baya amma suna hada ido sai taji wani abu na fuzgar zuciyarta zuwa gareshi matsawa tayi kusa dashi.

Rash
Sanah
Ku biyo mu

'YAR MAFIYA.. 12

�� *'YAR MAFIYA....*��

*Rash Kardam*
        *Sanah S Matazu*
*N. W. A*
Page
*12*
Kafin Yasiraht ta fita har ya tako yazo ida take hannu ya mik'o mata bata iya yin masa musu ba sai ta kama hannu al'amarin da ya ba ma kowa nacikin gurin mamaki, sai da ya janyota k'usa da shi yana kallon kwayar idonta suna iya jin numfashin juna Samar ya kasa d'auke idonsa gada gareta itama haka duk sun shagala da kalon junansu kalon mai d'auke da sak'onni kala-kala a cikinta.

Najwa da ta tsaya zuciyarta na matuk'ar tafarfasa wannan wani irin abu Samar keyi ma Yasiraht duk irin abunda nake masa ai yaci ya gane irin k'aunar da nake masa amma ko sassauta murya bai tab'a min ba irin yanda yayi ma Yasiraht yau tabbas dole na d'au mataki bazai yiwu ta shiga zuciyar da na dad'e ina muradi.

Cikin zafin nama tare da sihiri ta bi iska ta iso gaban su da sauri ta finciko Yasiraht tare da shiga tsakaninsu tana wani irin kalo ma d'auke da alamomin tambaya Samar da har zai yi magana ko me ya tuna sai ya nuna kujeransa da yatsa nan tabi iska ta iso gabansa tayi kasa-kasa tukun cikin isa da mulki ya taka kan matakalar ya zauna a kan kujeran tukun ta tashi da shi sama ta tsaya a sararin samaniya.

Hajiya Nafisatu ganin dare yayi gashi Uwani zata kawo mata ruwan zafi da sauri taje kitchen (madafi) taga ko ruwan bata d'aura ba ga kuma abincinta bata ci ba, gass ta kunna ta d'aura ruwa sai da yayi zafi ta juye ta d'auko zata tafi wata zuciya ta ce"anya Uwani yau lafiya tunda muke da ita bata tab'a mana haka ba barin kai ruwan nan inzo in duba ta.

'Dakin Uwani ta nufa nan ta sameta a k'asa dai-dai k'ofar fita a kwance a k'asa idonunta a sama duk sun kafe, ganin haka ba k'aramin razana tayi ba ta kira sunanta Uwani! Uwani!! Uwani!!! Ido ta zaro tare da d'aga hannuta ta ga ya saki da sauri ta juya tayi d'akin Abba da gudu ta shiga tana fad'in "Alhaji Uwani! uwani!!". Sam bata cikin hayyacinta sai da ya rik'ota ya soma mata addu'a ya ce"lafiya me ya samu Uwanin?.

Hannuta ya kama suka nufi d'akin yana zuwa ya ganta nan ya d'aga hannuta ya ga ya saki nan Abba ya saki salati don ya gane Uwani ta rigamu gidan gaskiya hannu yasa ya rufe mata idanunta tare da d'auko zanin ya rufe ta ya gyara ta a gefe d'aya hannu Hajiya Nafisat ya kama yana bata kalamai masu dad'i da kwantar da hankali ya kai ta d'aki ya fita ya kira Yasar ya masa bayani tare sukaje aka kira Limamin unguwansu tare da wasu makwabta, a dare aka nimi dangin Uwani aka suturta ta tayi kwanan keso.

Yasiraht sai da safe da ta tashi taga gidansu a cike nan ta tambayi hajiyarta me ke faruwa nan ta fad'a mata take taji wani zufa na keto mata ta razana sosai wato jiya ba mafarki takeyi ba asai da gaske abunda jiya ta gani a bacci ya faru nan ta fara hawaye duk wani tsoro tafaraji a haka aka fita da Uwani aka mata sallah aka kai ta gidanta na gaskiya Allahi Akbar rayuwa kenan.

Rash
Sanah
Ku biyo mu.

'YAR MAFIYA..11

�� *YAR MAFIYA...*��

Sanah S Matazu
   Rash Kardam
*N.W.A*
  Page
  *11*
Cikin firgita taci gaba da kallon fuskarta ba kowa bace face Najwa, hankalinta ya dugunzuma saboda kalamanta dake ratsa dodon kunnuwanta.
"Walahi Samir baka isa ba, ni zaka yaudara? Dama saboda haka ka matsa in jawota k'ungiya? Kasani kasan halina sarai zan iya kauda Yasiraht a kan ka walahi bana jurar had'aka da wata......."bata k'arasa ba ya kaimata wata muguwar shak'a a zafaffe.

"Ni zakiyiwa iskanci? Kinja mana asara, kin sani sarai dodon tsafi yace mudin ta hau kujerar nan matsayinmu zai hau-hawa a ko'ina saboda baki da mutunci muna dab da cika burinmu na samun *MATSAFIYA* ki wargaza mana shiri".Kakari ta shiga yi aka rasa wanda zai karb'eta.........Turo k'ofar d'akin ya katse hotan komai, Yasiraht ta soma waige-waige karaf suka had'a ido da Uwani mai aikinsu murmushi tayi.....sai dai murmushinta ya kashe sakammakon jiyo sautin muryar Samir a kunnuwanta"Sarauniya ki bamu wannan"ji tayi bakinta ya furta"na baku".Daga nan dif! Sautin ya d'auke Uwani ta ajiye mata abinci ta fita. Shudewar mintuna goma ta soma jiyo koke-koke cikin gidan,da gudu tai waje zuwa sashin da ta jiyo kukan.

Abinda ta gani ya girgizata da sauri ta juya ta koma d'akinta tana shiga ta kulle d'akin nan hoton fadan da ta gani d'azu ya bayyana a gabanta har yanzu suna kan Uwani mai aiki tana ihu suna yankan naman jikinta jiniko wani d'an rami yake taruwa a ciki sai da ya gama taruwa kamar wani iji ko zance cikin salon Sihiri da *TSAFI* wani hanya k'arami ya fito nan jinin uwani ya bi ramin har ya isa zuwa gun wani irin mumunan halitta mai jan ido sannan cikin kwayan idon ruwan ganye yana da dogayen hak'ora jikinsa ba fata sai wani gashi mai tsayi da bai gama rufe jikinba da inda muke muna hango yanda ya ke sanya harshensa yana shan jinin nan.

Yasiraht ganin haka kuma gata a tana kalon ta cikin mutanen sai ta soma ja da baya Samar ne cikin yanayin da ni kai na bazan iya gane ko me ke k'unshe a fuskansa ba ya soma mik'o mata hannu yana kad'a kai alamar k'arta gudu itakuma tana ja da baya al'amari da yaba ma kowa na gun mamaki don Samar yana matuk'ar ji da kansa ga shikuma d'an *SARKIN MATSAFA*  wanda duk ya ke cikin gunyiyan daga maza har mata bai sakar musu fiska bare har suga murmushinsa.

Sanah
Rash

'YAR MAFIYA... 10

�� *YAR MAFIYA...*��
Rash Kardam
Sanah S Matazu.
*N.W.A*
   Page
    *10*
Suuuuu! Yai tafiyar burgu zuwa cikin ramin, wata giggitaciyar kara ya saki daidai lokacin ya farka cikin tsananin firgita yana sambatu. Bakinsa na furta kalmar _"Hasbunallahu wani'imal wakeel"_cikin tsoro ya soma dube-dube sai motsi yake ji tare da alamun tafiya yai ta maza ya duro daga kan gadon jikiinsa yana rawa tamkar mazari.Kai tsaye band'aki ya shiga ya d'auro alwala ya tayar da sallah.

Ya jima zaune kan dardumar yana kaiwa ubangiji kukansa, bai tashi ba sai misalin biyu da rabi zuciyarsa ta yi sanyi sossai ya kwanta.

Washegari da safe dukkansu suka hadu a wajan break, gwanin sha'awa Yasiraht ta kallesu daya bayan daya ta lumshe ido a filli ta furta"gaskiya Daddy i really miss u".Dariya suka sa mata su duka Yasar cikin zolaya yace"rayuwar kwaki da k'arago".Cikin shagwa6a ta cunno baki"Daddy kaji shi ko?" "Kyaleshi diyar Daddy tuzurun kawai"dariya sukai baki daya.
Bayan sun gama bresk fast (karin safe) Yasiraht ta langa6e kai tace"Daddy inason zuwa shooping kace Yah Yasar ya kai ni", suna hada ido ta kanne ido ta daga gira "yes kai" ta furta da tsonakana. Ya gimtse fuska"kin raina ni ko? " "Yo raini kuma na nawa? ".Ta fad'a tana yi masa gwalo "to ai saiki nemi mai kai ki"saurin zubewa tayi "pls Yayana na daina"dariya sukai mata yace "ki bari sai zuwa yamma".Da haka sukai sallama Daddy da Yasar suka wuce aiki, Yasmin aka tafi kaita makaranta Hajiya ta nufi sashinta haka ma Yasiraht.

Shiru tana zaune kad'aici ya adabeta, ta juya can ta juya can. Tana zaune taga bangon d'akinta ya dare ta mik'e a tsorace ya cigaba da darewa wata irin fadace ta bayyana mai cike da kayan alatu a tsakiyarta wata kijera ce bisa dukkan alamu ta gwal ce. Gefanta Maza da Mata ne jingim sun kai su d'ari sun zagayeta cikin shiga wasu kaya jajjaye.Gaba d'aya kansu s sunkuye alamun girmamawa kujerar tsakiyar babu kowa,daga wani bango wani kyakkyawan saurayi ya bayyana dogo mai tsayi da cikar fadin k'irji.Fuskarsa doguwa yana da manyan idanu, hannu ya bud'emata "munai miki barka da zuwa Yasiraht zoki zauna"kawai saita samu kanta da rashin musu wa umarninsa gadan-gadan ta nufi fadar......... wata giggitaciyar k'ara aka saki daga gefansu hakan ya dakatar da'ita saboda razanar abinda ta gani.

Sanah
Rash
ku biyo mu

'YAR MAFIYA.. 9

�� *'YAR MAFIYA....*��

*Rash Kardam*
        *Sanah S Matazu*
*N. W. A*
Page
*9*
Jikinsa ba k'arfi ya mik'e ya nufi d'aki bayi ya shiga ya watsa ruwa tukun ya d'auro alwala yayi sallah ko abinci bai tsaya ci ba kasancewa lokacin bayan sallah azahar ne, kan katifansa ya fad'a ruf da ciki yayi ya baje k'atifansa sai bacci ne ya d'auke sa mai nauyin gaske.

Yasiraht kuwa tana shiga d'aki ta ajiye Yasmin ta rage kayan jikinta ta d'aura towel ta shiga wanka, sai da ta dirje jikinta sosai bayan ta d'auraye sannan ta k'ara yin wankan acewarta yau ta dawo gida dole tayi wanka na musamman, tana gamawa ta d'aura tawul ta fito tana goge jikinta da d'an k'arami tawul sai da ta goge jikinta tukun ta jawo k'aramin kujeran da ke jikin madubin ta zauna, sai da ta shafa mai tukun ta matso sai tin madubin don yin kwaliya.

Wak'an ta takeyi ta had'a kayan gu d'aya ta d'ago da zumar kalo cikin madubi da sauri ta mik'e tawul d'inta har na fad'uwa a kasa hakwara ta gani ta madubi suna zubar da jini tare da dariya, cikin sauri ta juya taga Yasmin na wasanta kalon madubi ta sakeyi bata ga komai ba, fauda ta shafa kawai ta fasa kwaliyan ta d'auko riga da skirt d'inta tasaka suka nufi falo don cin abinci.

Gudu ya ke zuba wa tamkar k'afafunsa zai fita ihu ya keyi yana niman agaji amma ko alaman wani babu a cikin dajin ga wasu manyan hallitu hak'waransu a waje suna gudu suna fisgan naman mutane wasu ko k'ok'on jinine a hannusu suna sha yana zubowa bakinsu sai da yayi gudu duk ya gama galabaita ya iso bakin wani k'aton rami wanda in kafad'a sai dai wani ba kai ba ko k'arshe ramin baya gani wani irin iska yaji mai had'e da guguwa a razane ya juya bayansa.

Hahaha sautin wani dariya da yaji cikin hanzari ya kali sararin samaniya inda yaji dariyan gudan kai ya gani a saman kujera yana yawo ga wani rin hayakin da ya turnuk'e kujeran sai da kujeran ta ju-juya a sararin samani tare da tsawa da walkiya takeyi ta soma matsowa gunsa gani haka yasoma ja da baya ba tare da ya kalli bayansa ba dai-dai lokacin ya kai bakin ramin suuuu ya tafi tare da sakin wani razanane k'ara.

Rash
Sanah

'YAR MAFIYA... 8

�� *'YAR MAFIYA.....*��
*Rash Kardam*
     *Sanah S Matazu*

*N.W.A*
     *8*
Wata giggitaciyar k'ara ta saki tana ja baya, a hankali haske ya gauraye komai ya dawo mata dai-dai. A rikice Yasar ya juyo hakan ya haifar da sub'ucewar sitiyarin hannunsa motar ta kaucewa titi ta nufi daji. Wata k'atuwar bishiya ta daka cikin ikon Allah gaban motar ne ya lotsa, da sauri ya fito ya bud'e sashin da take ciki. Sai sauke ajiyar zuciya take, hannunta ya kama jinsa ya yi yayi sanyi k'alau das! Gabansa ya fad'i sakammakon ganin yadda idanunta ya sauya cikin rikicewar murya yace.
"Yasiraht lafiyarki kuwa? ".
Ya fad'a da tsorataciyar murya,

Muryar tace ta sauya tare da bud'ewa, "me ka gani ne?" take ya soma ja da baya a tsorace binsa take launinta ya cigaba da sauyawa wasu hak'ora suka bayyana zak'wazak'wa jini na zuba daga idanunta k'ara ya saki ya yi cikin daji da matsanancin gudu take dajin ya kaure da wata hatsabibbiyar dariya ta cigaba da kuwa da karad'e kunnuwansa. Gaba daya ya rikice can tunanin adu'a ya ziyarci zuciyarsa, take ya soma karanta ayatulkirsiyyu.Wata hajijjiya aka yi dashi ya bugu da bishiya take kansa ya fashe ya fadi babu numfashi.

Shud'ewar rabin awa ya farfado ji yayi kansa ya yi nauyi, ya bude ido a hankali shasshek'ar kukanta ta karade kunnuwansa ya shafa goshinsa babu ciwo sai dai jikinsa ya tsamamma sossai. Ga mamakinsa sai ya riski kansa a bigiran da suka bar motarsu lamarin ya girmi kansa an janyo motar zuwa kusa da hanya. Ya bud'e baki zai yi magana,suna hada idanu wani matsanancin tsoro ya ziyarce shi ji ya yi yaka katabus.
"Tashi mu tafi gida".
Ta fada babu walwala,tayi gaba bin bayanta ya yi tamkar rak'umi suna isa tace "shiga muje".Jiki a sanyaye ya shiga yana tada motar ta tashi suka dauki hanya. Kansa ya yi zafi da yawa, a haka suka karasa gida babu um babu um um.

Ganin yanayin su ya tashi hankalin iyayansu, cikin damuwa suke tambayarsu abinda ya faru haka kawai Yasar ya samu kansa cikin kasa magana Yasiraht ce tayi bayanin cewar hatsari suka yi mamaki ya kashe Yasar amma ya kasa magana saboda fitinan nan kallon da take jefa masa a sace wanda yake hautsina kwanyarsa. Sun jajjanta musu sossai kai tsaye Yasar ya nufi sashinsa bakinsa a nauyayye zuciyarsa cinkushe babu damar magantuwa. Yasiraht taja hannun Yasmin suka nufi sashinta, take akasa masu aiki suka fita da motar bayan an fitar da kayan Yasiraht.

Yasar yana shiga sashinsa ya zube a kan gado, mamakin Yasiraht yake sossai, ji yayi inama ya fad'a abinda ya faru amma daya yi yunkurin hakan sai yaji bakinsa yayi nauyi. Kansa ya sara yana tsananin ciwo.

Rash
Sanah

YAR MAFIYA..7

�� *YAR MAFIYA.....*��

*Rash Kardam*
        *Sanah S Matazu*
*N. W. A*
Page
*7*
Tana dawowa daga sallah jakarta ta d'auka ta nufi night prep tana zuwa ajinsu ta zauna ta ciro takardunta tasoma nazarinsu  can zuwa wani lokaci kamar daga sama sai taji wani abu na zagaya k'afarta da sauri ta kalli k'asa bata ga komai ba, a hankali ta d'an matsa da k'afar taci gaba da k'aratu kamar ance juya ki kalli wajen tagan ajin sai ganin wani kujera yana yawo a sama ga kwarangal suna kewaye da gun wani ruwa jini da ke bin ta gefen kujeran yana sauka a kasa sai aka masa hannu da kayukan mutanane a firgice ta mik'e tare da runtse idonta tana hawaye.

Senior da ke ajinne ta daka mata tsawa ta ce"ke Yasiraht lafiyar ki kuwa mai ke damun ki kwana biyu?". Yasiraht ta sunkuyar da kai tare da zubar da hawaye ta ce"Sister nima ban sani ba". Kai Senior ta jin-jina ta ce"zauna to", haka sukayi prep d'in har aka tashi ta nufi hostel tana zuwa ta cire kayanta ta sanya na bacci ta kwanta a gadonta tana tunane tunane kala-kala idonta ta lumshe tana tunano abubuwan da suka faruwa da ita a 'yan kwanakin.

Najwa ne tazo ta dad'e tana tsaye a kanta tana murmushi Yasiraht da idonta ta d'an rufe sai taga kamar wani irin hallita shi ba cikaken mutum ba sannan shi ba dabba halitta mai ban tsoro cikin sauri ta bud'e idonta sai ta ga Najwa wani sassanyan ajiyar zuciya ta saki tare da mik'ewa ta zauna ta ce"Najwa  ya kike? Ban san shi gowarki". Najwa tayi murmushi ta ce"na dad'e anan ai", nan suka zauna suna hira sai kusan goma Najwa ta mik'e ta ce"barin tafi d'akin mu", Yasiraht ta mik'e ta ce"nagode sosai fa muje na rakaki". Suna tafiya suna hira har ta kai ta d'aki ta dawo.

Kwanaki sun tafi abubuwa da yawa sum faro Yasiraht ce na hango cikin murna tana had'a kayanta a trolley d'inta sabida gobe zasu tafi hutun zango k'arshe na karatu(thirt term) sai da tagama kimtsawa ta hau gadonta ta kwanta tana tunanin Yasimar a zuciyarta Najwa ne ta shigo nan ta tashi ta zauna suka fara hiran rabuwa sun dad'e suna hira Najwa ta tazo ta fiya  har sunyi nisa ta juyo ta kalli Yasiraht ta ce" yauwa k'awata ga chocolate(alewa) nan d'azu naje school shop na sai mana". Cike da murna Yasiraht ta amsa tayi godiya da kyar suka rabu.

Washe gari da safe suka gyara hostel sannan suka nufi assembly suka jeru sukayi layi sai zuwa can principal tazo ta ke d'alibai suka mik'e sai da suka gabatar da national anthem kafin suka zauna aka bud'e taro da addu'a bayan sun gama shugaban makaranta tayi bayani tare da cewa hutunsu zai kasance sati shida tana gama jawabi aka sallami d'alibai da murna suna ihu kowa ta fito gate d'im makaranta.

Yasiraht tana fitowa ta sami su Yasar sun zo d'aukarta jikinta a sanyayae ta gai dashi sai da yayi ta tsokana nanta sannan suka shiga mota suka d'au hanya sunyi tafiya mai nisa Yasmin har tayi bacci can ta tuna da chocolate d'in da Najwa ta bata da sauri ta d'auko ta b'are zata saka abakinta Yasar ya ce"abun 'yar haka ne wato rowa zaki min ko", cikin fara'a ta ce"wacce ni na isa na maka rowa..." Fiskansa d'auke da murmushi ya ce" bazaki min dad'in baki na yarda ba", can idon ta ya kai kan ledar chocolate da sauri ta d'auko ta ce"la ga naka ai kai ka fara min rowama ai.

Chocolate d'inta ta saka a baki ta fara taunawa ta had'iye take tafara ganin wani irin walk'iya da tsawa tamkar saukar aradu nan ta bar ganin haske sai duhu can ta hango wasu kwarangwal tare da wani irin suffar halittu suna cewa"Yasiraht muna miki murna da shigowa k'ungiyar mu muryoyi ne da yawa nan gashi sai gani abubuwan ban tsoro da firgici.

Ku biyo mu.
Rash
Sanah

'YAR MAFIYA...6

�� *YAR MAFIYA.....*��
*Rash Kardam*
    *Sanah S Matazu*
*6*
Tun daga wannan lokacin aka shiga tsorata Yasirsht, tana gayawa Yasar musamman in yazo mata visiting amma data ayyana hakan sai wani gaggarumin tsoro ya dumfari zuciyarta. Lamarin daya haifar da tarin k'alubale cikin lamuranta na yau da kullum ta soma bak'i da rama ga yawan kad'aici da san kusantar wajan da babu hayanniya musamman dajin cikin makaranta, Lokuta da dama can take tafiya, tai ta shawagi tana yawace-yawacenta.

Abin ya soma ta'azara a gareta, musamman in zata ci abinci ko ruwa sai taga sun sauya launi zuwa jini. Gashi met d'inta sun fara damunta idonta yana tsoratasu saboda rikid'ar da yake yi. Ana haka kwatsam wata rana Yasar ya kawo mata ziyarar bazata shi da Yasmin tayi murna sossai. Suna tsaye suna hira,Yasiraht ta hango abinda yasa ta dinga jan baya..........

Wani k'adangare ta hango suffarsa irin ta mutane ya mik'e yana tafiya zuwa wajan da suke. Dariya yake mata sossai ya bud'e hannayansa yana fad'ar"maraba da mataimakiyar shugaba ki zo garemu zamui miki kyakkyawan masauki".Wasu hallitu masu kawuna suka bayyana gefansa, suna masu biyo bayansa bakunansu biy-biyune wata giggitaciyar k'ara ta saki tai baya. Yasar yai saurin kai mata cafka, lau ta fad'o jikinsa babu numfashi babu alamunsa.
Hankalinsa ya tashi sossai, da sauri ya bude motarsa yana neman ruwan da zai yayyafa mata da kyar ya dai-daita nutsuwarsa ya samo yana zuba mata ta saki  ajiyar zuciya ta dawo hayyacinta.Zuba mata ido ya yi yana nazarinta.

"Lafiya Yasiraht? "
"Babu komai".
Ta bashi amsa tana inda-indar rashin gaskiya kai ya jinjina kawai suka cigaba da hira jikinsa a sanyayye.

Sun dad'e suna hira kafin ya bata sayyya sa suka mata da 'yan kud'ad'e suka mata sallama cike da kewar juna suka tafi, ita kuma ta dawo hostel tana kewan gida kayanta ta jera a locker tana gamawa ta kwanta a kan gado tare da lumshe ido tana tunanin gida don yanzu duk makaranta ya isheta baran ma da Shukura ta bar makarantar sai da lokacin sallah magriba yayi sannan ta tashi tayi alwala ta nufi masallacin makaranta.

Ku biyo mu
Rash
Sanah

'YAR MAFIYA.. 5

�� *YAR MAFIYA.....*��

*Rash Kardam*
        *Sanah S Matazu*
*N. W. A*
Page
*5*

Makaranta Mata da ke garin Kano ta dabo tumbin giwa aka kai ta S Marafa da Yasar su sukaje tare da ita aka gama komai aka bata JSS1A su Abba da Yasar basu bar makarantar ba sai da suka tabbatar da an had'ata da Senior (Na sama da ita) kafin suka mata sallama tana hawaye Yasar na hawaye yana rik'e da hannunta da kyar Abba ya raba hannusu suka shiga mota suka bar makaranta.

Rayuwan Yasiraht haka ya cigaba da gudana aciki kwalejin mata da ke garin kano tana karatu dai-dai gwar-gwado sam bata faye yawan kawaye ba sai k'awarta d'aya wato Shukura Adam ita 'Yar cikin garin Kano ne nasu yazo d'aya komai tare sukeyi wasu har suna musu lak'ani da 2stars(taurari biyu) don itama Shukura ba baya bace gurin kyau amma ita bak'a ce.

Seniors da yawa suna kawo musu farmaki akan suna son su da School daughter(d'iyar makaranta) duk wacce ta tsare su sai suce mata a gida an hanasu yin School Mummy(uwar makaranta) wasu daga lokacin da sukak'i amincewa musu zasu fara gallaza musu da tsangwama.

Yau take Visiting day (ranar ziyara) duk wani d'alibin da ke makarantar yayi kitso tare da wanke uniform d'insa na makaranta kowa ya fito tsaf sabida zuwan iyaye da yayu/kanne, hakan yake a gun Yasiraht don gayu tayi tana jiran iyayenta can taji wata 'yar ajinsu tazo tana cewa wai ana kiran Yasiraht S Marafa a bakin gate(gareji) yihuhuhu!!! Tayi wani tsalle tare da rawa Shukura sai dariya ta ke mata ta ce"kai Yasiraht irin wanan murna haka?". Yasiraht ta juya ido ta ce"ya bazanyi murna ba yau My Yasar d'ina ya zo tare da Abba na da Ummi na ga swt Yasmin d'ina". Shukura tayi murmushi suka mik'e suka sanya kaya suka fita tare.

Ko da sukaje gunsu Abba da gudu taje gun fa rik'e hannusa tare da fad'i i miss you my Yaya na(nayi kewar ka ko rashin ka)Yasar sai dariya ake mata tukun tazo ta rusuna ta gaida su Abba kayan abinci suka kawomata tare da girki mai dad'i haka sukayita hira har lokacin tafiyansu yayi wanda da kyar sukarabu.

BAYAN SHEKARA UKU.......

Wata kyakwan Yarinya muka hango sanye cikin uniform d'in makaranta  ta fito sai zun b'ure baki takeyi, Yasar ne ya kalleta ya ce"My sisi dole yau ki koma makaranta tunda ke ki ka zab'a da kanki". Yayi maganar cikin tsokana tare da yi mata gwalo biyo shi tayi da gudu zata kwad'a masa jaka dake hannuta ya tsere, Abba ne ya fito wanda hakan yasa suka nutsu mota suka shiga suka d'au hanyar kano tun a mota take kumbura har suka iso makaranta ko sallamar kirki bata musu ba sabida fushin da takeyi, ta saka junior (na k'asa da ita) suka tayata d'iban kayan ta ta tafi hostel.

Sam yanzu bata jin dad'in makarantar sabida an cire Shukura a makarantar yanzu bata da k'awa sai wata Najwa da ke damunta akan suyi kawance dole ba yanda ta iya ta fara bin Najwa sabida Najwa ta faye naci, wani saran da Yasiraht ta samu sam yanzu bata yawan addu'a komai yin shi take batare da ta nimi kariya daga gun Allah ba.

Wata rana ta kwanta cikin mafarkinta ta ganta a cikin dokar daji sai jin tayi ana kiran suna ta kuma muryan bibbiyu yake fita ga daji ba haske ko tafin hannuta bata gani sai daga can nesa ta hangi wani haske cikin sauri ta k'arasa nan taga wasu irin halita tare da jajayen kaya ajikinsu suna cewa" Yasirah mu na gayyatar ki cikin mu ki zo zamu baki matsayi babba". Muryan mutane dayawa takeji take ta toshe kunnenta aiko sai guri ya fara tsawa rugugugu!!! Tamkar zai zaga kasa ta shiga ciki ko ina na jikinta b'ari yakeyi.

Kasan gurin ne ya fara darewa gida biyu nan tasoma ja da baya tana gudu yana tsagewa ko da ta kalli cikin k'asan da ya tsage ba komai ciki face kogon jini da kwarangwal suna kiranta. Cikin ihu da k'araji ta farka sai gumi takeyi sam ko addu'a ta kasa bare tasamu nutsuwa Sanah ta ce"ni ko anya Yasiraht tana addu'a?". Can na tsaya tunani na ce" ni dai ganina da ita na k'arshe da tayi addu'a tun tana JSS2 aji biyu a zango karatu na farko(first term) Sanah ta jin-jina kai(lalle tana sakaci da addu'a kamar yanda wasu acikin mu suke wasa da addu'a ma kansu bare 'Ya'yansu dan Allah mu kula muringa addu'a don neman kariya Allah ya kare mu da iyalan mu ameen).

Ku biyo mu.
Rash
Sanah

'YAR MAFIYA.. 4

�� *'YAR MAFIYA.....*��

*Rash Kardam*
*Sanah S Matazu*

*®N.W.A*
    Page
     *4*

Ranar suna yarinya taci sunan Yasiraht, kulawa sossai Yasar yake bata. Goyo wankinta har kayan kashi tun Hajiya Nafisat na hanashi harta zuba masa ido in yai wani abun sai dai tai murmushi tace "yarinta".

Kwanci tashi Yasiraht ta isa yayye aka yayyeta, ranar ansha kuka da rigima sossai dan Yasar kusan kuka ya yi saboda ganin hawayanta. Shekarun Yasiraht uku cif tayi girma sossai ga kyau ga surutu, dungui-dungui Yasir ke koya mata A B C D.........nan da nan ta iya kamun kace kwabo ta'iya zuwa Z. Hakan yasa Hajiya Nafisat ta shawarci mahaifinta ya sata makarsnta. Makaranta mai tsada ya sakata,boko had'e da islamiyya in an tashi boko sha biyu da rabi, ake shiga tahafiz sai shida. Karatu sossai ake a makarantar, Yasir ya tsaya mata wajan lesson da bitar karatu. Tana primary four ta haddace izubi sha biyar mahaifanta sunji dad'i tare da shirya mata k'ayataciyar walima.

Manyan Malamansu da dama sun hallata, tare da jinjinawa iyayanta. Haka akeso idan yaro yayi kokari a yaba masa basai kin kashe kudi ba koda biscuit kikai masa kyauta zai ji dad'i ya samu karfin guiwa. Kwanci tashi al'amura suka cigaba da gudana.

Tunda Yasiraht ta shiga aji biyar Hajiya ta haifi kyakkyawar diya wadda taci sunan Yasmin,ba laifi kyakkyawa ce amma bata kama koda yatsan Yasiraht ba. Shigarta aji biyar ta soma adabar gidansu da batun boarding school, lamarin daya daga hankalin kowa a gidan ssboda basa son nisa da ita.Tun suna lallab'ata har suka soma yi mata fad'a lamarin daya jawo kukanta sossai. Yasar shi ne sarkin lallashi,  a hakan suka zana jarrabawar gama primary tana da shekaru tara cif, abin kaddara result ya fito Yasiraht taci bording school lamarin daya kawo musayar ra'ayi sossai akan tafiyar. Mahaifinta na ganin tayi kan-kanta, babu yadda zai yi haka ya barta ta tafi saboda farin cikinta Yasar daya jagoranci tafiyar yafi kowa jigatuwa.

SILAR KOMAI LOADING..........
RASH
SANAH.

'YAR MAFIYA.... 3

�� *'YAR MAFIYA.....*��

*Rash Kardam*
        *Sanah S Matazu*
*N. W. A*
Page
*3*

Durk'ushewa tayi take yanayin halitarta ya soma sauyawa daga yadda take zuwa wata suffar......

TUSHEN LABARI......

Alhaji Sani Marafa haifafen d'an garin Bauchi ne, iyayensa fulanin ne gaba da baya, ya kasance d'an boko ne sosai yayi karatun boko amma hakan bai sa ya kauce ma hanyar Allah ba, ya kasance mai zafin nima tun yana matashi duk da aikin k'arfin da yakeyi hakan bai hanasa karatu ba.

Cikin ikon Allah Alhaji Sani Marafa ya kammala degrees d'insa na farko a kan Business Administration yana kammalawa bai dad'e ba ya samu aiki a Ministry of Housing(ma'aikatar kula da gidaje) inda aka bashi Accounter (mai kula da kud'i) na gurin.

Bai dad'e da samun aiki ba yayi aurensa na farko inda ya auri matarsa Nafisatu. Nafisa macece mai kirki da girmama mutunane tana matuk'ar girmama iyayensa da 'Yan uwasa wanda hakan bak'aramin dad'i ya ke masa ba suma 'Yan uwansa suna sonta.

Yau ta kasance safiya da ta sanya iyalan gidan Marafa kuka wanda sukayi rashin 'Yarsa guda d'aya mai Suna Maryam, Maryam ta rasu ta bar Yaro kwaya d'aya mai suna Yasar wanda akala ya kai shekara biyar aduniya, Yasar yaro ne mai shiga rai gashi da hankali amma ya taso cikin gata don duk abunda yakeso shi za'a masa sabida ubansa yana da kud'i dai-dai gwar-gwado.

Bayan zaman bakwai Yasar yak'i zama gun kowa sai Alhaji Sani hakan yasa suka d'aukesa ya dawo hannusu da zama, duk wani gata da mahaifiya zatayi wa d'anta Hajiya Nasatu tana k'ok'arin gwada masa sun sanya shi a makaranta *ANSS* makarantar da ake ji dashi a cikin garin bauchi Yasar ya fara karatun sa cikin kwanciyar hankali, amma sam baya son zuwa Islamiya sai da kyar gashi yana da k'ok'ari sosai yana da hazaka da saurin d'auk'an karatu.

Yau Hajiya Nafisatu ta tashi da zazzab'i sosai wanda har sai da aka kai ta Asibiti ko da likita ya gwada ta ya tabbatar ma Alhaji Sani Marafa tana d'auke da juna biyu ohoho masu karatu kar kuso kuga murna a gun S Marafa haka sukayita kula da cikinta tare da ta abubuwan da akeso mai ciki tana ci.

BAYAN WATA TAKWAS..

Yau Hajiya Nafisa ta tashi da matsanacin ciwon mara da baya kasancewan Alhaji na gida bai tsaya b'ata lokaci ba suka kaita Asibiti, suna zuwa likita ya shai da masa haihuwa ne take aka shiga da ita labour room (d'akin haihuwa) sai da ta sami kusan awa guda tana nak'uda cikin ikon Allah ta haifo d'iyarta fara sol da ita, ko da aka sanar da S. marafa Hamdala yayi tare da gode ma Allah ko da aka gyarata suka nufo gida, tun da Yasar ya dawo daga makaranta ya samu Hajiya Nafisa ta haihu Yasar ya tasa 'Yar gaba ko 'Yan barka in sun zo a hannusa suke ganinta da kyar wani zubin ke bada ita a ganta, Hajiya Nafisatu da S Marafa suyi ta yi ma Yasar dariya don suna jin dad'in yanda yake nuna ma 'Yarsu k'auna.

Ku biyo mu.
Rash
Sanah

'YAR MAFIYA 2

�� *'YAR MAFIYA....*��

*Rash Kardam*
        *Sanah S Matazu*
*N. W. A*
Page
*2*

Cikin matsanancin tashin hankali ya cigaba da ja da baya. Cigaba tayi da bibbiyarsa bakinta yana hayak'i"kayi kuskure Yasar na shiga komar matsafiya, bazan ragama kaba bana yafiya bana mantuwa saina kassara rayuwarka da duk wanda ya bibbiyi rayuwar god'iyata."Cikin muryar tashin hankali yake fad'in "wacce ce ke? Meye alak'ata da ke? ".

Wata shu'umar dariya tayi,ta huro iska mai tsananin zafi da k'arfi take ta d'agashi sama ta wulwula ta dokashi da bango. Kansa ya tsage, ya soma zubar jini lau ya fad'i k'asa yaraf! 'Dif! Numfashinsa ya d'auke.

Ammar ne ya taho cikin wak'e-wak'ensa kamar an ce dubi can idonsa yakai kan Yasar kwance cikin jini. Wata giggitaciyar k'ara ya saki hakan ya jawo hankalin mutan gidan da gudu sukayo shashin. Ganin halin da yake ciki ya d'aga hankalin kowa, nan da nan aka sashi a mota aka nufi asibiti da shi. Cikin gaggawa aka karb'eshi zuwa emergency (wajan taimakon gaggawa).Likitoci sun duk'ufa a kansa, harzuwa lokacin bai dawo hayyacinsa ba, mahaifiyarsa banda kuka babu abinda take. Sai da sa'a uku ta shud'e sannan ya dawo hayyacinsa, an masa k'arin jini sannan aka hana kowa zuwa inda yake saboda suna san auna k'wak'walwarsa.

Cikin tsoro naja hannun Rash cwt muka bar wajan.
Wata shu'umar dariya aka saki, "hahahahahaha! Munyi nasara,munyi nasara".Aka fad'a da wata rikitaciyyar murya gaba daya wajan ya amsa amo suka saki dariya. Sanye suke da jajjayan kaya mazansu da matansu, idanunsu wani irin launi tamkar Rainbow (bakan gizo) akaifarsu zak'o-zak'o tamkar horaye, hak'ora sun zazzago duk gashin kansu ya mimmik'e tsaye dukkansu kayansu jajjayene kowanansu rike da k'ok'on jini suna sha.

Kwanan Yasar uku a asibiti aka sallame shi, sai dai an bashi magunguna tare da gargad'i a kan ya kiyayye buga kansa saboda saura k'iris ya rage yayi loosing memory d'insa.
Duk tsayin kwanakin da ya yi a asibitin babu Yasiraht babu alamunta wajan zuwa dubiya, lamarin daya tunzura zuk'atan 'yan uwa da dama harya haifar da kace nace a ciki.
Tsayin kwanakin yana samun sauk'i sossai, har ya koma wajan aiki.
"Yasira gaskiya da sake"cewar Samir dake zaune kan mota fuskarsa babu alamun walwala. Tayi ajiyar zuciya tana dubansa ranta duk a cakud'e hawaye ya ciko ido taf tasa hannu ta share. "Samir bansan ya zamui ba, Baba ya dage kan lamarin sossai.Gashi shugaba kullum cikin gargad'ina take bisa kaucewa dokar k'ungiya".Ta k'arasa maganar cikin raunin murya.

Cikin kaushin murya yace"zanyi hukunci"cikin sauri ta tari hanzarinsa "nasan hukincinka bahagone Samir karkayi pls na rokeka."Bai jira cewarta ba ya kwashi mota da tsananin gudu yabar harabar gidan. Durkushewa tayi take yanayin halitarta ya soma sauyawa daga yadda take zuwa wata suffar..........

TUSHAN LABARIN......

Ku biyo mu.
Rash
Sanah

Popular Posts

 
]]>All content on thisblog are copyright protected and cannot be reproduced on other websites without permission.