*YAR MAFIYA.....*
*Rash Kardam*
*Sanah S Matazu*
*N. W. A*
Page
*7*
Tana dawowa daga sallah jakarta ta d'auka ta nufi night prep tana zuwa ajinsu ta zauna ta ciro takardunta tasoma nazarinsu can zuwa wani lokaci kamar daga sama sai taji wani abu na zagaya k'afarta da sauri ta kalli k'asa bata ga komai ba, a hankali ta d'an matsa da k'afar taci gaba da k'aratu kamar ance juya ki kalli wajen tagan ajin sai ganin wani kujera yana yawo a sama ga kwarangal suna kewaye da gun wani ruwa jini da ke bin ta gefen kujeran yana sauka a kasa sai aka masa hannu da kayukan mutanane a firgice ta mik'e tare da runtse idonta tana hawaye.
Senior da ke ajinne ta daka mata tsawa ta ce"ke Yasiraht lafiyar ki kuwa mai ke damun ki kwana biyu?". Yasiraht ta sunkuyar da kai tare da zubar da hawaye ta ce"Sister nima ban sani ba". Kai Senior ta jin-jina ta ce"zauna to", haka sukayi prep d'in har aka tashi ta nufi hostel tana zuwa ta cire kayanta ta sanya na bacci ta kwanta a gadonta tana tunane tunane kala-kala idonta ta lumshe tana tunano abubuwan da suka faruwa da ita a 'yan kwanakin.
Najwa ne tazo ta dad'e tana tsaye a kanta tana murmushi Yasiraht da idonta ta d'an rufe sai taga kamar wani irin hallita shi ba cikaken mutum ba sannan shi ba dabba halitta mai ban tsoro cikin sauri ta bud'e idonta sai ta ga Najwa wani sassanyan ajiyar zuciya ta saki tare da mik'ewa ta zauna ta ce"Najwa ya kike? Ban san shi gowarki". Najwa tayi murmushi ta ce"na dad'e anan ai", nan suka zauna suna hira sai kusan goma Najwa ta mik'e ta ce"barin tafi d'akin mu", Yasiraht ta mik'e ta ce"nagode sosai fa muje na rakaki". Suna tafiya suna hira har ta kai ta d'aki ta dawo.
Kwanaki sun tafi abubuwa da yawa sum faro Yasiraht ce na hango cikin murna tana had'a kayanta a trolley d'inta sabida gobe zasu tafi hutun zango k'arshe na karatu(thirt term) sai da tagama kimtsawa ta hau gadonta ta kwanta tana tunanin Yasimar a zuciyarta Najwa ne ta shigo nan ta tashi ta zauna suka fara hiran rabuwa sun dad'e suna hira Najwa ta tazo ta fiya har sunyi nisa ta juyo ta kalli Yasiraht ta ce" yauwa k'awata ga chocolate(alewa) nan d'azu naje school shop na sai mana". Cike da murna Yasiraht ta amsa tayi godiya da kyar suka rabu.
Washe gari da safe suka gyara hostel sannan suka nufi assembly suka jeru sukayi layi sai zuwa can principal tazo ta ke d'alibai suka mik'e sai da suka gabatar da national anthem kafin suka zauna aka bud'e taro da addu'a bayan sun gama shugaban makaranta tayi bayani tare da cewa hutunsu zai kasance sati shida tana gama jawabi aka sallami d'alibai da murna suna ihu kowa ta fito gate d'im makaranta.
Yasiraht tana fitowa ta sami su Yasar sun zo d'aukarta jikinta a sanyayae ta gai dashi sai da yayi ta tsokana nanta sannan suka shiga mota suka d'au hanya sunyi tafiya mai nisa Yasmin har tayi bacci can ta tuna da chocolate d'in da Najwa ta bata da sauri ta d'auko ta b'are zata saka abakinta Yasar ya ce"abun 'yar haka ne wato rowa zaki min ko", cikin fara'a ta ce"wacce ni na isa na maka rowa..." Fiskansa d'auke da murmushi ya ce" bazaki min dad'in baki na yarda ba", can idon ta ya kai kan ledar chocolate da sauri ta d'auko ta ce"la ga naka ai kai ka fara min rowama ai.
Chocolate d'inta ta saka a baki ta fara taunawa ta had'iye take tafara ganin wani irin walk'iya da tsawa tamkar saukar aradu nan ta bar ganin haske sai duhu can ta hango wasu kwarangwal tare da wani irin suffar halittu suna cewa"Yasiraht muna miki murna da shigowa k'ungiyar mu muryoyi ne da yawa nan gashi sai gani abubuwan ban tsoro da firgici.
Ku biyo mu.
Rash
Sanah
0 comments:
Post a Comment