*'YAR MAFIYA....*
*Rash Kardam*
*Sanah S Matazu*
*N. W. A*
Page
*14*
Matsawa tayi kusa dashi Samar kalon yake mata mai cike da so da kauna hannusa ya kalli wani zobuna guda uku a jere manya dasu da kuma rubutu a jiki ta baya kuma alamar kan mutum ne wannan zobe ya danna nan take wani irin hallita ya bayyana a gaban sa tare da rusunawa ya ce"ya shugabana ban umurni na bi". Murmushi Samar yayi cikin k'asaita da mulki ya ce"aljani d'an duguzu ina so ka kai mu dajin k'are dugunka zan huta a gun".
Kafin ka ce mai ta ke gurin ya gauraye da iska nan take Yasiraht ta fara kakkarwa da tsoro nan wata dadduma ta bayyana tare da matasai na alfarma ko da ta duba ta gani d'an duguzu ne ya ke rik'e da dadduman a kansa nan tsoro ya k'ara kamata. Samar ne ya kama hannuta kaman walkiya suka hau kan dadduman nan taga su tsaga bango suka fito gashi tana gani suka wuce mutane amma da alaman su basa ganin su a hankali suka haura sararin samaniya sai keta hazo sukeyi suna tafiya cikin kwanciyar hankali.
Yasiaht ta rasa mai yasa in Samar ya mata magana bata iya masa musu kuma in ta kalli kwayan idonsa yana mata kwarjini bana wasa ba a han kali ta sauk'e sassanya anjiyar zuciya.
Najwa da ta nufo library (gurin karatu) taga wulgawan su Samar nan take wani bak'in ciki ya lulub'eta ga mutane a gun bare ta tanza hallita ta bisu da sauri ta nufi cikin library a girgiza ta dawo wata tsun-tsuwa ta fito daga library ta bisu zuciyar ta na mata k'una sai sake-saken wani irin abu zatayi ma Yasiraht.
Samar suna zuwa dajin nan dadduman ya sauk'o dai-dai bakin ruwa suka sauk'a wani abun ban mamaki ga manyan namun daji suna shawagi a gun ba wanda ya kulasu ko ta inda suke basa bi. Samar ne yasake murza zobe nan wata mata fara da farare kaya ta bayyana ba'a ganin k'afarta sabida fararen kaya ya rufe k’afafunta, ta rusuna ta ce"Ranka shi dad'e 'Dan Sarkin Matsafa jikan matsafa mai kake buk'ata a maka sai da ya d'au lokaci kafin ya ya ce"kayan marmari nake buk'ata". Kafin kace me wani tire na alfarma kamar na zinari sai kyalli yakeyi tare da d'auke ido kayan mar-mari aciki irinsu Tuffa(Apple), Inabi Ayaba, Abarba, d.s.s.
Yasiraht sam tak'i ci Samar ne ya ce"bazaki ci ba ko sai na baki ya d'auko yankake tufa zai sa mata a baki kawai suka ga wani irin abu ya tun k'aro su da gudu ya buge Yasirah ta fad'i k'asa, nan abun ya fito da wani tsini da niyar zuwa ya cakka ma Yasiraht a cikinta, cikin sauri Samar ya bud'e hannusa sai ga wani sanda ya fito da sauri ya nuna wannan tsun-tsuwar sai ga Najwa ta dawo halittanta na asali ta fad'i a gun tana mai da nufashi. Cike da mamaki Samar ke kallonta a hankali ya tako zuwa inda Yasiraht take ya d'agata tukun ya kalli Najwa nan yaji wani haushinta ya kamasa a hankali yasoma takawa zuwa gun Najwa cikin fushi.
Sanah
Rash
Ku biyo mu.
0 comments:
Post a Comment