New Post

Friday, 26 May 2017

YAR MAFIYA 21

�� *'YAR MAFIYA*��
Sanah S Matazu
Rash Kardam.
*21*
Kwanci tashi suka gama zana jarrabarwarsu masha Allahu komai lafiya aka sallamesu suka koma gidajansu zaman jiran sakammako.
Tsakanin Najwa da Yasiraht kuwa abun yakai intaha domin ta zame musu karfan kafa, tun dawowarta gida Samari kemata tururuwar zuwa amma babu wanda take saurara sai Samar shi kadai kawai ta bawa gurbi a zuciyarta.Kwatsam tai karo da soyayyar Muhseen dan aminiyar mahaifiyarta, lokaci daya ya kwanta mata a zuciyarta nan da nan suka amincewa juna ta tattara Samar ta watsar hakan yai bala'in kona ran Samar ya rasa hanyar da zai bi dan kauda Yasiraht ganin babu dama sai ya soma bibbiyar Muhseen.....

Muhseen da daya ne tilo tsoka guda a miya ga Alhaji Lawali mai akwai, asalin mahaifinsa bafulatanin garin Kurfi ne mamansa balarabiyar Egypt hakan yasa Muhseen ya dauko kyau gaba da baya kyakkyane na gaban kwatance.Tun tasowarsa bai san kwaba ba balle harara sangartacan yarone kaf karatunsa a waje yayi hakan yasa ya budi ido da harka da Mata over.Ko kadan mahaifansa basa son laifinsa, yasha yiwa yaran jama a cikkuna da fyade.Tunda Samar ya gama gano waye Muhseen ya cika da farin ciki domin ya samu hanyar gumawa Yasiraht a sadaka.Hanya ta farko daya soma bi neman shiri da Najwa nan da nan suka koma kamar da sannan ya bijiro da bukatarsa dake tayi shirin fansa babu jinkirtawa ta amsa bukatarsa nan da nan ta soma shirin fuskantar matsalar.
Ranar Asabar da yammaci Muhseen ya fito daga Shanawa club, harya gota tarin wasu gun-gun matasan yan Mata ya hangi Najwa a gefe tana taunar cingum daga ganinta babu musu ya tabbatar yan good evening ne in kiya yai mata sarai ta gani sun hada ido ta kanne ta cigaba da hidimar gabanta.Bai yi kasa a guiwa ba ya karasa da fari ta kalleshi ta watsar, daga bisani tabi yarima akasha kida basu wani jimaba ya ribaceta yajata cikin club din ya kama mata daki.

Tsayin kwanaki uku suna tare, Najwa na hillatasa ko kiran Yasiraht bata bashi damar yi ranar kwana na uku ne ta samu suka fita yawo tare, cikin ikon Allah sukaiwa JIFATU tsinke anan sukai kici6us da Yasiraht,Najwa ta kalleta ta watsar Muhseen kuwa ko kallonta bai yi ba a haka suka gama siyayyarsu suka fita suna tayar da mota da gudu tai wa motarta key wadda ta aro wajan Yasar ta rufa musu baya.

Tunda Najwa ta hangi tahowar Yasiraht tai wa Muhseen wayau ta amshi tukin, tuki suke na fitar hankali ko gabansu basu duba a haka sukaiwa cikin gari nisa.Najwa ta saki murmushi ganin tarkonta ya kama kurciya.Cikin rashin zato tai ribos motarta tayo baya take motar Yasiraht ta wuntsula ta kife ta kama hayaki bata hakura ba tasake turata tai gaba ta fada rami ta kama da wuta.Tai juyi taja motar  tana kallon Muhseen tana murmushi wanda yakasa hanata kudurinta.Sunyi tafiya mai nisa sun shigo gari ta shammaci Muhseen ta nufi wata katuwar mota cikin hanzari ta danna zobanta ta bace take motar ta murkushe Muhuseen sai gawa.Tana daga gefe tana kallon mutane kowa na budurunsa, nan da nan tabar wajan.Batai nisaba taji jikinta na shock, tsoro ya shigeta tuni ta bayyana wajan motar Yasiraht.

Gabanta ya tsananta faduwa lokacin da tai arba da Samar,idonsa jajjur yana huci kamun tai wani yunkuri ya kaimata cafka ya dinga azabtar da ita tana ihu, ihun tane ya farkar da Yasiraht daga dogon suman da tayi.

Murmushi ta saki lokacin da tai arba da Najwa nacin azaba wajan Samar kafin su farga ta bace bat, wani hadiminsu tasa ya dauko mata motarta zuwa kofar gida da dingishi ta shiga gidan, nan ta riski tashin hankali labarin mutuwar Muhsun.Kara ta saki ta zube a sume.
Sanah
Rash

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts