*'YAR MAFIYA.....*
*Rash Kardam*
*Sanah S Matazu*
*®N.W.A*
Page
*4*
Ranar suna yarinya taci sunan Yasiraht, kulawa sossai Yasar yake bata. Goyo wankinta har kayan kashi tun Hajiya Nafisat na hanashi harta zuba masa ido in yai wani abun sai dai tai murmushi tace "yarinta".
Kwanci tashi Yasiraht ta isa yayye aka yayyeta, ranar ansha kuka da rigima sossai dan Yasar kusan kuka ya yi saboda ganin hawayanta. Shekarun Yasiraht uku cif tayi girma sossai ga kyau ga surutu, dungui-dungui Yasir ke koya mata A B C D.........nan da nan ta iya kamun kace kwabo ta'iya zuwa Z. Hakan yasa Hajiya Nafisat ta shawarci mahaifinta ya sata makarsnta. Makaranta mai tsada ya sakata,boko had'e da islamiyya in an tashi boko sha biyu da rabi, ake shiga tahafiz sai shida. Karatu sossai ake a makarantar, Yasir ya tsaya mata wajan lesson da bitar karatu. Tana primary four ta haddace izubi sha biyar mahaifanta sunji dad'i tare da shirya mata k'ayataciyar walima.
Manyan Malamansu da dama sun hallata, tare da jinjinawa iyayanta. Haka akeso idan yaro yayi kokari a yaba masa basai kin kashe kudi ba koda biscuit kikai masa kyauta zai ji dad'i ya samu karfin guiwa. Kwanci tashi al'amura suka cigaba da gudana.
Tunda Yasiraht ta shiga aji biyar Hajiya ta haifi kyakkyawar diya wadda taci sunan Yasmin,ba laifi kyakkyawa ce amma bata kama koda yatsan Yasiraht ba. Shigarta aji biyar ta soma adabar gidansu da batun boarding school, lamarin daya daga hankalin kowa a gidan ssboda basa son nisa da ita.Tun suna lallab'ata har suka soma yi mata fad'a lamarin daya jawo kukanta sossai. Yasar shi ne sarkin lallashi, a hakan suka zana jarrabawar gama primary tana da shekaru tara cif, abin kaddara result ya fito Yasiraht taci bording school lamarin daya kawo musayar ra'ayi sossai akan tafiyar. Mahaifinta na ganin tayi kan-kanta, babu yadda zai yi haka ya barta ta tafi saboda farin cikinta Yasar daya jagoranci tafiyar yafi kowa jigatuwa.
SILAR KOMAI LOADING..........
RASH
SANAH.
0 comments:
Post a Comment