New Post

Friday, 3 February 2017

MAYA'UDARA-PAGE-1

[6/5/6:30pm]

🌲RASH KARDAM🌲🌲
                   &
   🎋SADEEY S ADAM🎋
               WITH
💖💖BEEBAH LUV💖💖
                
      
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
           YAUDARA
    🌺🌺🌺🌺🌺🌺

(  Bismillahir Rahmani Rahim)
 
    {Allahumma Salli Ala Muhammadin Wa Sallim}

      
         Ranshi a bace yake sosai, ya rasa meke masa dadi,, duniar tayi masa zafi,, ya ciji lebe, ya ciji yatsa, duk shi kadai, yayi zagayen a daki ya koma Parlour, sai gumi ke keto masa duk da sanyin Ac,, kamar wani zautacce.
 
     Ba kowa bane illa ""AREEF""
 
       Daukan waya yayi ya kirata yafi sau 20 amman bata dauka ba,, wai me yasa Teemahluff ke mishi haka,, Kodan taga yana bala' in  sonta ne??
    Ya kuma dialing wayar frnd dinsa farouk,,bugu daya ya dauka, bayan sun gaisa ne yake ce masa, ya akai ne abokina ya gidan ya akwai labari ne?
        Yayi tsaki tare da cewa whl kasan matsala ta guda daya ce akan teemah,, nayi kiranta but  she refused  to answer my calls..
    Farouk ne ya girgiza kan shi, tare da tausaya wa aminin nashi, don kuwa yasan yana cikin matsala,,, baisan me zaice mishi ba wanda ya wuce ya bashi hakuri,, tun farkon soyayyar su da yarinyar shi daman batai masa ba,, kuma yasha bashi shawara akanta, amman yaki ji, har fada sunyi akan teemah.
 
     So daga baya sai ya yanke shawarar zuba mashi ido akanta, inya kawo masa kukanta sai dai kawai ya bashi hkr ya kwantar masa da hankali,, amman yasan yarinyar kawai cheating take ma abokinsa, yasan ba son shi take ba, sai dai yace Allah ya ganar dashi gaskia..

     Kamar kullum yanda ya saba bashi hakuri yau ma hakan ce ta faru, yace ya sake kiranta may be, bata kusa da phone din ne,, haba farouk I called her more than 20 tyms fa..
  
      Bari kawai naje gidan su,, yanzu. Ya dire wayar yana ajiyewa ya sake kiranta still no answer,, ya dauki key din motar sa ya fice daga gidan..

    
     A bangaren Teemah kuwa,, tana ganin calls din sa taki dauka, don kuwa yau batai niyar ganin shi ba,, kuma tasan shi da dan karan naci zai iya ce mata zai zo..
    
            Mstwww tayi tsaki aikin banza kawai, sai shegen nacin tsiya.

     Hmmm masu karatu last week fah ta gama tarairayar shi, ta amshe masa yan kwabban sa, wai za ai bikin kawarta nxt week,,,

    Yanxu haka wani take jira, zai zo yau kuma shi zata wanka.

     Areef bai zame ko ina ba sai kofar gidan su teemah, nan ma yayi kiran dunia taki dauka, ya kira wani yaro ya aike shi cikin gidan, ya kira mashi ita,, ai kuwa yana zuwa ta balbale shi da masifa, dallah je kace mishi bana nan na fita unguwa,, yace toh har kama hanyar tafia tace zo nan, ya dawo ta kama kunnen sa kuma sauran in kaje kace nice nace bana nan,,, whl sai nayi maka dukan tsiya in muka gamu,, kuma in ya tafi ka dawo ka gayan,, yace toh daman yasan hali.

   Bayan fitar shi ummanta tace,, anya teemah baza kima kanki fada ba ko?,, whl duk ranar da Allah ya tashi kamaki baza kiji da dadi ba.

      Bata ce komai ba tayi wucewar ta daki, tana kunkuni,, uwar tace hmmm ayi dai mu gani..

     Bayan an gaya masa bata nan,, ya dauko naira 100 yaba dan Aiken,, sannan ya zauna cikin motar yayi tagumi, ya kulla wancan ya kunce wancan  duk shi kadai,, yakai har kusan 10 to 15 mins bai tafi ba,, sai can ya tada motar shi ya tafi...

    Har yanzu bai ji ya tsaneta ba,har yanzu ji yayi kamar kara rura mashi wutar son ta ake a cikin zuciyar shi,, Allah sarki daman ance so hana ganin laifi..
      After tafian shi da 10 minute kuwa sai ga wanda take jira yazo me suna Haydar, daman tana ta Allah2  Areef ya tafin kar  su hadu...

      Nan aka chanchada kwalliya,, me jan hankali aka fito ana yatsina ita a lallai ga me saurayi..

       Teemah fara ce doguwa, amman bata da wani kyau,, tana da dukiyar fulani daidai gwargwado,, amman kuma kasan sha6al yake don kuwa sungul ta tafi,, abinda ya Cece ta farin da take dashi,, don ko gashi bata dashi, ita dai wannan farin da iya kwalliya da kwalisa  da kuma shagwa6a da kwarkwasa,, shine yake jawo mata samarin, har take samun damar yaudarar su..

     Tasan duk wata salon hanya ta yaudara da iya kwacewa samari abin hannun su,, don kuwa indai har Allah ya hada ku, toh ka shiga uku a wurinta sai tasan duk wata hanya data amshe maka kudin ka sannan ta rabu dakai....
   
     Toh masu karatu ga dai Haydar nan a gaban teemah,,, bamu san ta yanda zata bullo masa ba don shima wankar sa take son yi...
  
    Ku biyo mu don jin yanda zata karshe,,, don yanzu aka fara yanzu aka diga damba a wannan lbrn me suna YAUDARA don kuwa akwai gwagwarmaya a cikin sa sai kun jimu...

     

       Daga masu kaunar ku.   🎋S   💖 B 🌲R

  💥Marubuta Uku💥

[truncated by WhatsApp]

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts