New Post

Saturday, 11 February 2017

RUWA CIKIN COKALI... PAGE 2.

°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•°
    _(Ya ishi mai hankali wanka)_
*{BASED ON TRUE LIFE STORY}*
                  *(JULY 2016)*

                          *NA*

*®Rashida .A. Kardam*
       
*N. W. A*
Page
*2*

_Malamin ya kammala darasin sa ya fita cikin sauri Aunty Samy tazo ta kama hannu Kdeey ta ce"baby zo muje mota na taho miki da wani sak'o Kdeey ta ce"to Aunty amma ki bari mu k'arasa lectures d'in in yaso sai mu fita gaba d'aya. Kdeey ta janyo littafinta tasoma duba darasin da aka musu na lissafi kasancewar ita gwana ce a fagen lissafi ba ta dad'e ma wani Malami ya shigo awa d'aya da rabi ya d'auka yana darasi(kasancewa darasin 1 credit unit ne) ya na fita suka d'auki jakansu don yau course biyu zasuyi Aunty Samy ne ta kamo hannuta suka nufi motarta suna shiga ta d'auko wani leda mai girma a shak'e da kaya Samy ta ce"swt Kdeey gashi bayawa". Kdeey ta ce"Aunty Samy nikam ba zan karb'a ba kyautar yayi yawa kulum kina cikin d'awainiya da ni ai da kunya na sa hannu na karb'a". Samy ta had'a rai bata ce komai ba ta tada mota suka d'au hanyar unguwansu Kdeey da ke Kobi street._
_Kafin su isa sai da Samy ta biya da su *CINDERELLA*  ta saya musu ice cream tukun suka kamo hanya ko da ta iso k'ofar gidansu Kdeey ta faka motar da mika ma Kdeey laidar da kyar ta karb'a tazo zata bud'e k'ofar ta fita Samy ta kirata a hankali muryan kasa-kasa, Kdeey ta juyo Samy ta rik'o hannuta tare da matso da fuskanta dai-dai na Kdeey harsuna iya jin numfashin juna cikin idon Kdeey ta ke kalo tare da lumshe ido da sauri Kdeey ta kwace hannuta Samy ta rufe motar tana maida numfashi a hankali duk yanayinta ya canza gaba d'aya ta jima a gun kafin da kyar ta iya jan motarta ta nufi gida, ko da ta isa horn ta rink'ayi wa mai gadi kamar ma haukaciya cikin han zari ta bud'e gareji ta shiga ko motar bata faka da kyau ba ta ruga cikin gida da gudu tana shiga ta fara cire kayan jikinta ta d'aga waya tayi kira cikin wani irin murya ta ce" pls soby kizo gidana yanzu ina buk'atar ki". Sai da ta cire kayan jikinta kaf tana wani irin nishi tana lumshe idonta_.

                  *DEDICATED TO*
      *_KDEEY N MRS AL'AMEEN_*

_Rash Kardam💕_

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts