*YAR MAFIYA.....*
*Rash Kardam*
*Sanah S Matazu*
*6*
Tun daga wannan lokacin aka shiga tsorata Yasirsht, tana gayawa Yasar musamman in yazo mata visiting amma data ayyana hakan sai wani gaggarumin tsoro ya dumfari zuciyarta. Lamarin daya haifar da tarin k'alubale cikin lamuranta na yau da kullum ta soma bak'i da rama ga yawan kad'aici da san kusantar wajan da babu hayanniya musamman dajin cikin makaranta, Lokuta da dama can take tafiya, tai ta shawagi tana yawace-yawacenta.
Abin ya soma ta'azara a gareta, musamman in zata ci abinci ko ruwa sai taga sun sauya launi zuwa jini. Gashi met d'inta sun fara damunta idonta yana tsoratasu saboda rikid'ar da yake yi. Ana haka kwatsam wata rana Yasar ya kawo mata ziyarar bazata shi da Yasmin tayi murna sossai. Suna tsaye suna hira,Yasiraht ta hango abinda yasa ta dinga jan baya..........
Wani k'adangare ta hango suffarsa irin ta mutane ya mik'e yana tafiya zuwa wajan da suke. Dariya yake mata sossai ya bud'e hannayansa yana fad'ar"maraba da mataimakiyar shugaba ki zo garemu zamui miki kyakkyawan masauki".Wasu hallitu masu kawuna suka bayyana gefansa, suna masu biyo bayansa bakunansu biy-biyune wata giggitaciyar k'ara ta saki tai baya. Yasar yai saurin kai mata cafka, lau ta fad'o jikinsa babu numfashi babu alamunsa.
Hankalinsa ya tashi sossai, da sauri ya bude motarsa yana neman ruwan da zai yayyafa mata da kyar ya dai-daita nutsuwarsa ya samo yana zuba mata ta saki ajiyar zuciya ta dawo hayyacinta.Zuba mata ido ya yi yana nazarinta.
"Lafiya Yasiraht? "
"Babu komai".
Ta bashi amsa tana inda-indar rashin gaskiya kai ya jinjina kawai suka cigaba da hira jikinsa a sanyayye.
Sun dad'e suna hira kafin ya bata sayyya sa suka mata da 'yan kud'ad'e suka mata sallama cike da kewar juna suka tafi, ita kuma ta dawo hostel tana kewan gida kayanta ta jera a locker tana gamawa ta kwanta a kan gado tare da lumshe ido tana tunanin gida don yanzu duk makaranta ya isheta baran ma da Shukura ta bar makarantar sai da lokacin sallah magriba yayi sannan ta tashi tayi alwala ta nufi masallacin makaranta.
Ku biyo mu
Rash
Sanah
0 comments:
Post a Comment