New Post

Saturday, 11 February 2017

RUWA CIKIN COKALI... PAGE 18

°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•°
    _(Ya ishi mai hankali wanka)_
*{BASED ON TRUE LIFE STORY}*
                *(AUGUST 2016)*

                          *NA*

*®Rashida .A. Kardam*
       
*N. W. A*
Page
*18*

_Umma duk lokacin da Kdeey ta dawo daga makaranta sai ta bincika jakarta bata sani ba taga ko wani abu ya canza a mu'amalanta na yau-da-kullum wani sa'in akwatin kayan Kdeey Umma ita ke gyara mata shi da kanta********._
_6 years latter_
_Kdeey na hango ta dawo daga unguwa kasancewan ta gama jarabawa na makarantar gaba da primary tazo zata shiga d'aki Umma ta ce “zo nan Khadijatu" Kdeey tazo ta rusuna Umma ta ce“d'an ban aron wayanki na yi kira nawa ba kati ne aciki". Ba musu Kdeey ta mik'a mata Umma ta karb'a har Kdeey ta shiga d'aki Umma ta ce"miye number security wayanki?". Kdeey ta fito ta ce“sunanki zaki saka". Umma tana danna sunanta ya bud'u sai da ta bincike wayar taga ba komai aciki tukun ta mayar ma Kdeey._
_Jarabawan su Kdeey ya fito ta samu sakamako mai kyau cikin ikon Allah ga Admission d'inta na N C E ya fito sun bata course d'in ENGLISH P.E.S(English primary education studies) nan ta fara zuwa makaranta tana d'aukan darasi kwanaki sun tafi ana haka wata Samy ta lik'e ma Kdeey tun bata kulata har ta fara kulata._
_Duk wani alheri tana yi ma Kdeey tun bata kulawa har tazo ta fara kulata har gida Samy zata zo ta gaida Umma cikin shiga ta mutunci da kamala._

*_WACECE SAMY_*

_Samy asalin iyayenta 'yan garin bauchi ne suna da kud'i bana wasa ba ta taso cikin gata da sakalci gata da kawaye iri-da-kala, ta kanje ta karbi kud'i agun iyayenta tayi facaka dashi. Samy ta kasance irin yarannan ne wayayyu tun tana k'arama ta san hawa 2go da sauransu duk wani hayoyin da zai sadata da abubuwan batsa ta sani hakan yasa ta kasance mai tsananin sha'awa ga yawan kalon fina-finan batsa tana budurwa hakan yasa ta kasa hakuri ta d'auko k'araman k'anwata suna kwana tare haka zata rungumeta tana shafarta da duk wata hanyan da tasan zai gamsar da ita. In zata fita a gida sai ta sanya hijab da nikaf ta fita alhalin layyanta na ciki ba kyau. A makaranta suka had'a group suna kallon fina-finan lesbian (mad'igo) wanda hakan yasaka suka ware gidan wata k'awarsu mai suna Suby zasuna had'uwa a gidansu suna biyan buk'atar kansu kasancewa gidan su Suby iyayenta basa zama gari Babanta baya aiki a gari Mamanta tana business tana fita waje sarin kaya. Da haka su Samy suka kware a gun mad'igo(lesbian) Samy suka had'a group harda maza suna lalaewarsu, kasancewan Samy tana da kyau Mazan group d'in suna kawo mata buk'atarsu amma sam rak'i kulasu har wasu kawayenta na jin haushinta suna mata kallon bata waye ba ta ce“ba wai maza ne bana so ba a'a ina sonsu sosai sai dai bana son na zubar da budurcina a waje har sai na kai ma mijina darajata._

                *DEDICATED TO*
     *_KDEEY ‘N' MRS AL'AMEEN_*

_Rash Kardam💕_

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts