New Post

Sunday, 12 March 2017

AMANA TA CE 1

AMANA TA CE
By
©Rash Kardam
  1
                   
Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassan ne ya fito daga dakinsa cikin manyan kaya, yayi shiga ta alfarma, dining yaje ya zauna hajiya fatima ne zaune tana jiran mai gidanta, bayan ya zauna ta masa sannu, ya amsa cikin sakin fuska ya kalleta yace Fatima ina Auta take, tace tana sana’arta har yanzu inaga bata farka ba, cikin kulawa ya kalli fatima yace hajiya ina fada miki kulum ki ringa kula min da Auta, cikin daure fuska tace Alhaji kulum haka kacewa yarinya duk ta san garce sakalci ya mata yawa ta girma aman kamar wata jaririya, Alhaji ya nisa yace hmm fatima akwai maganar dana ke so muyi da Auta da Ammar, ana cikin haka sai ga Ammar ya shigo cikin ladabi ya gaidasu, suka amsa da sakin fiska, ya kalli Hajiya yace Mum ina Auta tace tana daki tana sana’ar ta na baccin sage barinje na tasota, Ammar ya mike da nufin komawa falon Abba yace aaa Ammar bama haka ai kaima dana ne don ina jinka ajikina kazauna mu karya tare, ana haka sai ga Mum tafito Auta na biye da ita, yau anyi sa’ah harta yiwanka da wuri bata tsaya baccin gadonta ba, cikin zazza kar muryanta ta gaida Dad dinta da Mum san nan Ammar cikin kulawa ya amsa, kusa da Dad ta zauna suka karya bayan sun gama suka koma falo, dad ya zauna mum na gefensa Ammar na kasa tana zaune, Autar Hajiya na kusa da ita, Abba ya dago cikin muryansa mai sa sanyin jiki kalo daya zaka masa ka gane yana cikin taradadadi, Zainab ya ambata, Autar Hajiya sai da taji sunan har cikin ranta tasan dad baya kiran sunan ta haka kurum sai da dalili, ta amsa da na’am dad, Dad ya kalle ta yace Zainab ina son insanar dake wani abu, sanana inaso ko bayan raina Auta kikasance mai hakuri da biyya ga wanda zakiyi tarayya dasu san nan ki rike mutuncinki, karki sake kiyi watsi da tarbiyan da muka miki, nasan ki amma ina son ki kara rike mutun ciki, ki rike Adu’ah a duk inda kike, Zainab idonta duk ya ciko da kwala don tun da take da dad bai taba mata zance makamancun haka ba,maganar dad ne ya katse mata tunani, Ammar ya kira ya amsa, dad yaci gaba dacewa Ammar kai kadai na yarda da kai acikin wayanda mukayi tarayya, kaine ka rike min “AMANA” ta don mutane yanzu ba yarda, san nan ko bayan raina banyarda ka bar Zainab ba ga “AMANARTA” na baka kai kadai nasan zaka kula min da ita, cikin sanyi jiki Ammar yace dad mai yasa kake irin wan nan maganan Dad yayi murmushin manya yace Ammar da Zainab atare, yace kukadai zan sanar da maganan nan kusani akwai wayanda suke min barazanan kashe ni da iyali na akan dukiyata, da nanema da gumi na, nikuma naki amsamusu sabida mutuwa da rayuwa tana hannun Allah, ba wanda ya isa ya kashe wani face da izinin Allah. Cikin damuwa Auta da Ammar sukacewa suwaye dad murmushi yayi yace ka kyalesu kawai zan sanar muku amma bayanzu ba, hajiya ma tayi musu nasiha sosai, dad ya mike ya fita hajiya tayi daki Auta kuka takeyi Ammar ne ya rarrasheta sai da tayi shiru kafin ya fito harabar gidan nan sale suka fara masa kallon bansa da kuma zaka sani yau, musa kam dariya yayi sosai kafin yace mun kusa ganin karshen wan nan rigima taka da kafafa kamar gidan ubanka, an samu gidin zama sai nuna isa kamar dan gd ko ta kansu bai bi ba ya wuce dakinsa shidai yana fatan Allah ya tsaresa da sharrin masu sharri.
Dad bai dawo ba sai kusan 10 lokacolin Auta tayi bacci hira sukayi sosai da Hajiya kafin yace bari ya watsa ruwa bayan yayi wanka hajiya fatima tafito cikin kayan baccinta mai daukar hankali ta nufi dakin Alhaji sun yi hira sosai kafin suka kwanta, Misalin karfe 2 gari yayi shiru sai sai hadirin daya hadu gari yayi baki2 nan take ruwa ya tsinke sosai kamar da bakin kwarya, kowani mutum na gidansa yana bacci, wata bakar jeep ce mai bakar glas na ga tanufo gaye din gidan Alhaji Al-hassan sai da suka fito duka kwan kwasa wa mai gadi ya bude musu suka shiga, duk da ruwan da akeyi bai dame
dame musuba kalo daya zaka musu kasan ba alkairi bane, atare dasu, sun rufe fidkokinsu da marks bakinsu da kwayan ido   su da kofar hancinsu  ke waje, magana sukayi tsakaninsu wanda sukazo a jeep  dasu sale da musa, da alaman dai sun san da zuwansu, bayan sun gama ne, suka nufi cikin gida ko da suka shiga dakin Alhaji suka nufa suka samesi da hajiya suna tare,
Ammar ko yatashi tun karfe daya yasoma sallah nafilan da yasabayi duk dare bayan ya idar duk da ruwanda da akeyi yaji alamar shigowan mota da sauri ya leka nan yaga wasu da bakaken kaya sun rufe face dinsu duk abunda sukayi na kallonsu nan yaga sun ciro bin diga, yana kalon sun shiga ya bude kofar dakinsa cikin sanda ya kwanta a kasa yadoma tafiya da ciki kamar yanda soja suleyi a fagen yaki cikin fulawas ya soma bi ko da yaje ta kofar baya ya shiga yayi sa’ar kofar abude take nan ya tura a hankali, daman duk wanda yashigo ta baya dakin Auta zai fara samu don haka ya tura kofar a hankali.
yaganta tana bacci, a hankali ya soma tashita, cikin ikon Allah ta mike ba gyan gyadi, ihu zata sa ya toshe bakinta yace Auta kina jina wasu mutane sun zo gidan nan da   kuma da alamar wayanda dad yafa da.suna son kashesa ne, nan cikinta ya fara rawa idonta  ya ciko da kwalla, yace dau hijab diki mu leka muga don musan abinyi, kasa dauka tayi shi ya daukar mata ko ta kalmi bata tsaya dauka ba suka nufo falo a han kali suka leka, nan suka ga abunda ya razana su dad ne aka samasa bindiga  da Hajiya  suna kara lekawa nan suka ga fuskan Baba Sani da yayansa iyaka, alokacin suka dana kuna mar bingigan  tass kake ji karan harbin bindiga, nan take auta tasaki kara atake suka juyo gurin da sukaji kara suna fadin suwaye suka nufo gunsu.
Yan uwa amin afuwa za ku ga ban2 dana farkon dana soma sakewa, yanzu na dawo da lbr daga tsakiya ne amin afuwa  inaga hakan watakil zaifi.
Shin su Autar Hajiya da Ammar suna kubuta daga sharrin mutanen nan? bacin gashi gate din gdn a kulle.
Suwaye wayan nan mitanen?
Mai nene alakarsu da Dad?
Waye Ammar?
Don son jin amsarnan kubiyo Yar Gidan Kardamawa .
Taku akulum mai kaunarku  

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts