New Post

Monday, 20 February 2017

RUWAN CIKIN COKALI PAGE 1

°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•°
    _(Ya ishi mai hankali wanka)_
*{BASED ON TRUE LIFE STORY}*
                 *(JULY 2016)*

                          *NA*

*®Rashida .A. Kardam*
      

*_لبسم الله الر حمن الر حيم_*

*YA ZAMA DOLE IN YABA MUKU*
  
         Ya zama dole na yaba muku tare da jin-jina muku ga k'ungiyar mu mai d'umbin Albarka had'in kai tare da k'ok'ari gami da hazaka *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* ALLAH ya kara kare mana k'ungiayr mu ya d'aukakata tare k'ara mana fasa mai albarka da tunani mai kyau acikin rubutum mu da al'amuran yau da kulum Ameen.

  
                *TSOKACI*

   *_Wanan labarin yana d'auke da labarin daya faru na gaskiya(True life story) kashi biyu tare da k'ari aciki don yak'awata labarin, in har yazo d'aya da labarin  ka/ki to ina shawarta ki/ka kuyi k'ok'arin gyara halinku Allah ya shirye mu baki d'aya, sannan na zauna nayi tunani mai tarin yawa gami da bincike akan abunda yake addabar 'Yan mata da Samarin zamani yanda munanan ayyuka da alfasha da fasadi wanda Allah ya hana sukuma sun mayarshi abin ado da burgewa a tsakaninsu Matasa da 'Yan mata yanzu Ya Allah ka tsaremu da aikata haramci Ya Allah ka kare mana Imanin mu Ya Allah ka sanya zuciyar mu ta karkata ga addinin ka Ya Allah ka tsare mu da yin alfasha da munanan ayyuka ameen._*     

       *GODIYA TA MUSAMAN*

Maryam Alkali(Mamu
Sanah S Matazu
Kausar Lurv
Benazir Umar
Munay
Lubee Mai Tafsir
Khadija Candy
Aseeya B Aleeyu
Miss Hafsy
Autar Hajiya
Aisha S Mazoji

             *MACE MAI KAMALA*
                   *DA TUNANI*

*MRS AL'AMEEN DOLE NA JIN-JINA MIKI DON KECE GINSHIKIN YIN WANNAN RUBUTUN ALLAH YA BARMU TARE*

*N.W.A*
Page
*1*

_Cikin hanzari ta d'auki jakarta na hannu tare da sanya hijab d'inta ruwan bula mai shek'i sosai wanda ya matuk'ar yi mata kyau, cikin nutsuwa ta fito ta nufi d'akin Umminta da sallama ta shiga Ummi da ke ninke kaya ta d'ago kalo d'aya zakayi wa matar ka ga kamalarta, fiska a sake ta ce"a'a d'iyar alkairi har kin fito ne?". Cikin murmushi jin dad'i wacce aka kira da d'iyar albarka ta amsa da"eh Ummi yau ma na makara gashi Aunty sami tana ta kirana yanzu haka". Ummi ta ce"ayya to ki hanzarta tafiya Allah ya kare min ke sannan ki kula banda k'awayen banza ki kula da mutuncinki Allah ya miki albarka adawo lafiya". Cikin jin dad'in kalaman Umminta ta amsa da"Ameen Ummi na na tafi", cikin sauri ta fito ta tsari mai Napep ta ce"ATAP(ABUBAKAR TATARI ALI POLYTECHNIC) zaka kai ni can Wintin dada". Mai Napep ya ce ki bada d'ari biyar cikin hanzari ta zaro ido ta ce"haba Malam kamar baka san yanayin gariba ni students (d'aliba) zan baka d'ari da hamsin". Mai Napep(National porverty N Eradication Program)ya ce"to ki kawo d'ari biyu kawai", ta amsa da "Allah ya kaimu lafiya". Tashiga Napep(National Poverty N Eradication Program) d'in suka d'au hanyan ATAP(ABUBAKAR TATARI ALI POLYTECHNIC) sun d'anyi tafiya mai nisa har ya iso k'ofar makarantar sai da ya kai ta har k'ofar hall d'in da suke lectures(d'akin taro na darasi), cikin sauri ta bashi kud'insa tare da shiga da sauri d'akin taron da sauri._
_Cikin sa'a Malamin  dake gabatar da darasin bai koreta ba ta nimi guri ta zauna Samy cikin sauri ta kamo hannunta tana mata wani shu'umin kalo tare da fara murza hannuta wanda kulum haka take mata Samy ta ce"Dear mai yasa kike son yin latti kinga har anjima da fara darasi". A hankali ta zare hannuta cikin taushin murya ta ce"yau aiki ne ban fara da wuru ba". Tun daga kan haka bata k'ara ce wa komai ba ta mayar da hankalita ga karatun da ake musu._

                *DEDICATED TO*
     *_KDEEY N MRS AL'AMEEN_*

_Rash Kardam💕_

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts