New Post

Tuesday, 9 May 2017

'YAR MAFIYA... 8

�� *'YAR MAFIYA.....*��
*Rash Kardam*
     *Sanah S Matazu*

*N.W.A*
     *8*
Wata giggitaciyar k'ara ta saki tana ja baya, a hankali haske ya gauraye komai ya dawo mata dai-dai. A rikice Yasar ya juyo hakan ya haifar da sub'ucewar sitiyarin hannunsa motar ta kaucewa titi ta nufi daji. Wata k'atuwar bishiya ta daka cikin ikon Allah gaban motar ne ya lotsa, da sauri ya fito ya bud'e sashin da take ciki. Sai sauke ajiyar zuciya take, hannunta ya kama jinsa ya yi yayi sanyi k'alau das! Gabansa ya fad'i sakammakon ganin yadda idanunta ya sauya cikin rikicewar murya yace.
"Yasiraht lafiyarki kuwa? ".
Ya fad'a da tsorataciyar murya,

Muryar tace ta sauya tare da bud'ewa, "me ka gani ne?" take ya soma ja da baya a tsorace binsa take launinta ya cigaba da sauyawa wasu hak'ora suka bayyana zak'wazak'wa jini na zuba daga idanunta k'ara ya saki ya yi cikin daji da matsanancin gudu take dajin ya kaure da wata hatsabibbiyar dariya ta cigaba da kuwa da karad'e kunnuwansa. Gaba daya ya rikice can tunanin adu'a ya ziyarci zuciyarsa, take ya soma karanta ayatulkirsiyyu.Wata hajijjiya aka yi dashi ya bugu da bishiya take kansa ya fashe ya fadi babu numfashi.

Shud'ewar rabin awa ya farfado ji yayi kansa ya yi nauyi, ya bude ido a hankali shasshek'ar kukanta ta karade kunnuwansa ya shafa goshinsa babu ciwo sai dai jikinsa ya tsamamma sossai. Ga mamakinsa sai ya riski kansa a bigiran da suka bar motarsu lamarin ya girmi kansa an janyo motar zuwa kusa da hanya. Ya bud'e baki zai yi magana,suna hada idanu wani matsanancin tsoro ya ziyarce shi ji ya yi yaka katabus.
"Tashi mu tafi gida".
Ta fada babu walwala,tayi gaba bin bayanta ya yi tamkar rak'umi suna isa tace "shiga muje".Jiki a sanyaye ya shiga yana tada motar ta tashi suka dauki hanya. Kansa ya yi zafi da yawa, a haka suka karasa gida babu um babu um um.

Ganin yanayin su ya tashi hankalin iyayansu, cikin damuwa suke tambayarsu abinda ya faru haka kawai Yasar ya samu kansa cikin kasa magana Yasiraht ce tayi bayanin cewar hatsari suka yi mamaki ya kashe Yasar amma ya kasa magana saboda fitinan nan kallon da take jefa masa a sace wanda yake hautsina kwanyarsa. Sun jajjanta musu sossai kai tsaye Yasar ya nufi sashinsa bakinsa a nauyayye zuciyarsa cinkushe babu damar magantuwa. Yasiraht taja hannun Yasmin suka nufi sashinta, take akasa masu aiki suka fita da motar bayan an fitar da kayan Yasiraht.

Yasar yana shiga sashinsa ya zube a kan gado, mamakin Yasiraht yake sossai, ji yayi inama ya fad'a abinda ya faru amma daya yi yunkurin hakan sai yaji bakinsa yayi nauyi. Kansa ya sara yana tsananin ciwo.

Rash
Sanah

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts