BAZATA
By
©Rash Kardam
1
Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan likitoci fiskan ta sanye take da yar karamar glass wanda ya kara fito da tsananin kyan da Allah ya mata kalo daya zaka mata ka gane irin nutsuwar da take dashi, gata da kyau ga ilimi, tsayuwa nayi sosai na soma kare mata kallo, da farko zan iya ce muku farace sol, tana da manyan ido gasu farare tass! Masu fisgar hankali wato irin idon nan da ake musu lakabi da sexy eyes, tana da dan karamin baki wanda in ka gansu sai sun baka sha’awa, sa’anan tana da dogon hanci kamar pencil, Allah ya hore mata dukiyar kyau ba laifi, gata da hips dinta, san nan bata da wani kiba, ko da na kalli cikinta a dakale yake, wannan zai baka damar gane acikin wasu jerin mata take.
Sannu a hankali ta iso gun motar ta ta bude tashiga, ta juta ta kalli gefenta tace sorry Sis Feenat na dade ko amin afuwa, zakin muryanta da salon da take magana ya sani lumshe ido nan take na fara jin bacci, kunna motar tayi ta dau hanyar fita daga cikin ATBU.
Cikin nutsuwa take tukinta tayi nisa da Asibitin ABUT kena ta kaarya kwana, ta hango motar Doctor Marsal tana isowa, parking tayi a gefen hanya ta kalli feenat tace sis ina zuwa ga docter Marsal nan bari in mata magana, tafito cikin takunta mai dauke hankalin mai karatu, DR Marsal kuwa da ta hango ta itama parking tayi ta fito suka tsaya suna gaisawa, sun dauki minti biyar suna tsaye, can wata mota ciran frado mai bakin glass ta taho gadan-gadan kansu tayo, Marsal tana hango Motar tace DR Jiddah ki matsa ga dan ne man maganan nan zai fara, Dr Jiddah ta nuna kamar bata gane waye ba tace"waye dan neman magana?". Cikin dariya Dr Marsal tace " kin fini san shi wato share wa kikay"., Cikin ko in kula Dr Jidda tace "wai wa kike nufi?". Dr Marsal tace "waye in ba Doctor M Ghali ba".
"Mtss". Ta ja tsaki, aiko kafin ta rufe baki kaji tasss!…… Ya watsa mata ruwan da ya taru a gefen hanya, dake lokacin damina ne, ranta in yayi dubu to ya baci, tsayawa yayi da motarsa ya fito yana dariyan mugunta, ya soma takowa sannu a hankali ya iso inda suke, cikin tsiwa da masifa ta bude baki zata soma zazzaga masa mafifa, ya ciro kudi masu yawa, ya watsa mata tare kashe mata ido daya ya daga mata gira. ya ce"ga wannan kisai omo, ki wanke kayanki, in kuma hakan zai yi wuya to ki barsu a haka zasu dacewa da ke". Ya dan sake wani murmushin mugunta mai tattare da bayyana nasara acikintanya ce" ko da ya ke na sanki gwanar iya wanki ne ba sai kin tsaya bayar wa amiki ba". Ya sake kashe mata ido daya ya juya yana takun isa da mulki gamida kasaita ya fara tafiya yana jin wani nishadi a zuciyarsa ko ba komai yaji sanyi a ransa. Yakuma rama kadan daga cikin abubuwan da wannan Yarinyar take masa.
Idan ran Jiddah yayi dari to ya baci har wani daci-daci take ji a lebben bakinta. Bata kaiga karshen bakin ciki bata yi wani yinkuri ba tana fama da radadin abunda ya mata, yazo zai wuce da motarsa ya kara buleta da kurar motar sa, ko da ta juya aiko nan taga jama ita suke kallo, nan taji hawaye, bakin ciki yasoma zubo mata don tunda take a rayuwarta bata taba karo da cin zarafi irin wannan ba. Ko ta kan marsal bata bi ba ta nufi motarta a guje ta shiga tà saki wani kuka tare da tada motar bar gun da gudu, Marsal na mata magana ko tabi takanta.
Monday, 27 February 2017
Home »
» BAZATA PAGE 1
BAZATA PAGE 1
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
https://mynovels.com.ng/blair-waldorf-biography-net-worth-age-height-quotes/
ReplyDelete