BABBAN KUSKEREN
DANA TAFKA
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Bismillahi rahmanu raheem, dukkan godiya, da yabo, tsarki da mulki sun tabbata ga Ubangijin sammai da kassai. Na fara rubuta wannan littafin cikin iko Allah, ya Allah ka bani ikon isar da sak'o mai amfani aciki, san nan ka sanya, mutane zasu, nishad'an tu dashi, ta hanya mai kyau ameen.
Pg-1~5
Wani kyakyawan Matashi, mai jini ajika, sanye yake cikin, kakin sa na Police, kalan blue da bak'in wando. Kayan sunyi matuk'ar amsan jikinsa, tamkar dashi aka tsara kayan, ko da na kali wannan guy d'in. Dogon ne fari sol, yana da faffad'an k'irji, sannan ga shi da dogon hanci tamkar pencil, yana da k'aramin baki, ga kuma wasu sexy eyes, d'insa da suka rikitani, shekarunsa bazai wuce 37 ba. A hankali yake tafiya, falo ya nufo, dai-dai nan, naji muryan mata tana kiran Indo! Indo! Indo!.
Wacce a ke kira da indo ta fito da sauri, sam bata lura da Yallab'oi ba, tana yankowa sai jin, garam sunyi karo, take jikinta ya d'au rawa ta fara dan Allah kayi... Bata k'arasa ba yasakar mata, wani lafiyayan mari a fiska. Da gudu tayi ciki don tana matuk'ar tsoron Haiydar. Shi ko gogan kar-kad'e inda ta tab'a ya fara, cikin zuciyarshi kuwa, cewa yake"mtss na tsane ki bana son ganinki, don ba yanda na iya ne.
Indo tana shiga, sai da ta share hawayenta,ta k'arasa cikin d'akin, taje ta rusuna agaban wata mata, wanda da'alama itace matar gidan, cikin sanyi muryanta mai dad'in sairaro tace"gani Hajiya".
Wacce aka kira da Hajiya sai wani yatsina take, tace"ga hulan Haiydar nan ki kaimasa, ya fita ni bazan iya tashi ba, cikin tsoro Indo ta bud'i baki tace"Aunty wal....
"Kee yi min shiru umurni na baki, tashi ki kai masa, kina yar aiki, har zanyi magana kema kiyi.
Jikin Indo ba k'wari ta k'arba ta fito falo, dai-dai koma ciki ya d'auko hulan, wani kalo ya watsa mata, take yan hanjin cikinta suka soma rawa, sam bata son had'uwar su, da Haiydar, don ya matuk'ar tsanata, sam baya son ganinta, Indo kuwa ta mak'ure ajikin garu kamar munafuka, duk tayi kalan tausayi. cikin fushi yayi kanta.
DEDICATED TO
AISHA MUH'D
(MAMAN ABDUL SHAKUR)
RASH LUV✍
[5/26/2016]Rash Kardam
BABBAN KUSKEREN
DANA TAFKA
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-6~10.
Cikin fushi Haiydar yayi kanta, hularsa ya fin cike tare da tofa mata yawu, ya wuce abunsa, cikin zuciyarsa na masa suya, "mtss ace wai matar ka ta sunna, batasan kula da hakkin miji ba.
"Bata damu da duk wani abun da nake bukata ba, wai sai yar aiki.
"Yar aikin ma wanda bata min ba, sam na tsani ganinta mtss. Yayi tsaki, dai-dai lokacin ya shiga motar sa, mai gadi da sauri ya bud'e masa yafita.
Tafe yake cikin nutsuwa har ya isa area Commander, yana shigowa aka fara sara masa, da han zari ya nufi office d'insa dake sama. Yana shiga na biyo sa, nima da sauri don na fara aikina, d'an madai-daicin office ne, d'auke yake da tebur sai kujeran zama, gefe ga k'araman fridge, da nesa na hango yar k'aramar TV bango da ke mak'ale, office d'in yayi dai-dai misali.
File d'in da ke kan tebur ya duba, nan ya fara yan rubuce-rubuce, nan ya d'aga waya yace"hello Sargent Nasir, kazo ina nemanka a office d'ina yanzu. Wayar ya ajiye ya cigaba da rubutu, ba'a d'au lokaciba wani d'an matashi, ya turo qofar office d'in, yana shigowa ya kame kamar katako tare da buga k'afansa a kasa, hannusa ya sanya shi a gefen damansa tare da waresu. Cikin girmamawa yace" Morning sir".
Naji an kira da sir, bai s'ago kansa ba, yana rubutunsa yace" Morning how is your work?.
Sergent Nasir yace"fine too.
Haiday ya ci gaba da cewa" na duba file d'in case din mutanen nan, kun kaisu CID ne?.
"Eh Sir tun jiya ma aka kaisu.
"Ok daman abun da nake son ji kena.
"Zaka ita tafiya.
Sergent Nasir ya sake sara masa tukunan ya juya ya tafi.
Haiydar ko aikin da ke gabansa yayi, bai fito ba sai lokacin Sallah, k'arfe uku da rabi na yamma, ya kamala duk aikin da zaiyi ya fito ya shiga motarsa ya nufo gida.
Tun a hanya da yayi tunanin abunda zaije ya tarar tsaki ya farayi, duk sai yaji baya son komawa gidan.
DEDICATED TO
AISHA MUH'D
(MAMAN ABDUL SHAKUR)
RASH LUV✍
[5/26/2016]Rash Kardam
BABBAN KUSKEREN
DANA TAFKA
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-11~15.
Indo ko tun lokacin da Haiydar ya tofa mata miyau, da gudu tashiga d'akinta, kan gado ta fad'a tasoma rusa kuka kamar ranta zai fita, a fili take cewa"wannan wani irin rayuwa ne?.
"Mai na tsare masa ya tsaneni?.
"Ina da iyayena suna nan nasan duk rashinsu ba ran zauna cikin wanna k'uncin ba.
"Wayyo Ummi na! Allah ya jikanki, tabbas nayi rashi.
"Ina zansan inda dangina suke na nemesu, nasan su bazasu tsaneni ba. A hankali ta tashi ta d'auko wasu fotuna, da wani awarwaro masu kyau, sai d'aukar ido sukeyi, rungumesu tayi tana kuka mai tsuma zuciya, a haka har baci ya d'auketa. Kamar ama mafarki takejin ana kiran sunanta, firgigit tanfarka, aiko taji an sake kiranta, da sauri ta mike ta b'oye war-waronta da hotunanta, ta fito cikin hanzari.
Cikin isa Falmi tace"kee mai kikeyi da baki min aiki na ba?.
"Kin san Darling d'ina ya kusa dawowa.
"Ke harkina da wani saken da zakiyi bacci a gidan nan?.
"Ko kin manta matsayinki na baiwa ne?.
"Mtss na baki nan da 30 minutes ki gyara gidan nan, kuna in kin gama kije ki gyara ma only d'akinsa.
"Zakiga kayan daya ciresu ki wanke su tass, kuma karkisasu a engine kinsan bai cika son wankin....
Sallamansu Xahra da Meesha luv ne yahanata k'arasa magana.
"Oyoyo sis kune haka?.
Cikin sakin fuska sukace"eh mune da mayya.
Falmi tace"ni fushi nake daku ma rabon ku da gidan nan yau kunsan wata 2 fa.
Meesha tace"kawas tuba muke amana hak'uri.
"Sadeey tace" kyaleta kamar ita ta a zuwa mana a kai-akai.
Falmi tace"kudai ku k'araso tukun sannuku da zuwa.
Juyaa tayi ta kali Indo tace"keee mai kikeyi anan har yanzu baki mik'e kinyi aikin gaban ki ba?.
"Ko sai na b'ata miki rai ne?.
Sum-sum Indo ta wuce cikin gida.
Xahrah BB tace"Falmi wacece wannan?.
Cikin ko in kula Falmi tace"house girl d'ina ne.
Meesha tace"kee baki da hankali zaki d'auko wannan zankad'ed'iyar budurwa, wanda duk na miji mai lafiya sai ya yaba da ita.
Sadeey tace"tayani gani fa, amma kinyi gan-ganci.
Falmi tace"kai banza haka zan barta, yanda nake da kishi ae ba zan so wani ya rab'i Haiydar d'ina ba.
"Muna tare daku bari ku ga yanda zasu k'are in yadawo.
"Kuma bana barinta tayi kwaliya.
"Kai gasalima ya tsaneta tsana mai muni.
Xahrah tace"kee baki san wani lokacin tsana yana dawo soyayya ba.
Falmi tace"kee zan bar Haiydar hakane, san a haka ma baya son ganinta.
DEDICATED TO
AISHA MUH'D
(MAMAN ABDUL-SHAKUR)
RASH LUV✍
0 comments:
Post a Comment