*YAR MAFIYA*
Sanah S Mstazu
Rash Kardam
*15*
Cikin fushi yake nunata da yatsa, "wato Najwa bakya jin magana ko? Ina kaucewa sab'amiki kina k'ok'arin k'untatamin to walahi zanyi maganinki".Wata giggitaciyar dariya ta saki, tana hucci mai zafi ta dubeshi.
"Samar ni zaka wulakanta saboda ina bibbiyarka?Walahi kabani mamaki k'warai da gaske, zan nuna maka sharin mace sai kayi nadamar cin amanata".....bata k'arasa ba ya nunata da hannu tuni wani sirririn haske kore ya fito ta tsintsiyar hannunsa ya daki fuskarta take ta saki wata giggitaciyar k'ara data kid'ima dajin.Namun dajin suka dinga gudu suna neman mafaka,yaraf ta zube k'asa babu numfashi.'Daukar Yasiraht ta yi suka bar wajan.
Cikin tsananin gudu suka dinga keta dazzuzuka, a hankali ya sauketa cikin labry d'in ya kama yatsanta yasa mata wani zobe.Zoban yana da tsananin haske in ka kalleshi, jikinsa tambarin kan skelaton ne a jiki daga tsakiya an masa ado da gwal yanata k'yali b'at ya b'ace.A hankali idonta ya soma washewa ta saki ajiyar zuciya kanta yai nauyi sossai a jigace ta nufi hostel saboda gajiya.Turus ta tsaya lokacin data fito, sakammakon ganin d'alibai dandazo guda sun zagaye Najwa cikin galabaitaccen yanayi.
A sanyayye ta karasa wajan tana tambayar abinda ya faru, wata muguwar shak'a Shany ta kawomata wani shock da hannunta ya yi yasa ta sakin Yasiraht bata shirya ba tai baya tana muzurai.Ita dai Yasiraht rakata ta yi da idanu zuciyarta k'war cike mamakin ganin Najwa a wannan yanayi.Take abinda ya faru ya dawo mata, kanta ya sara ras! Ta dafe ta wuce area d'insu jikinta na rawa.Emeka dake gefe ta kwashe da dariya, cikin gurbataciyyar hausarta tace "yaro bai san wuta ba".
Wani rikitaccen kallo Shany ta aika mata, a daddafe ta wuce hostel tana zuwa ta zube kan gadonta tana numfarfashi.Ta dafe kanta da yake juya mata sossai, a haka ta yini kwance.Najwa sai da tai kwana biyar kwance sannan ta dawo hayyacinta.
Tun daga lokacin wata gaba ta k'ulu tsakanin Najwa da Yasiraht, kwata-kwata basa ga miciji idan hanya ta had'asu sun dinga hararre-hararre kenan.Abinda yake tada hankalin Najwa yadda duk yadda taso cutar da Yasiraht sai zoban hannunta ya zamo shamaki wajan afkuwar hakan, haka take hakura kiri-kiri kwatsam aka nemesu taron gaggawa a k'ungiya.
Harabar wajan cike take da manyan motoci ababban kalo, abin sai wanda ya gani an kawata fillin ra jajjayan furani da bak'ak'k'e komai na wajan ja da bak'i ne har kayan jikinsu.A hankali aka soma darewa ana bashi waje yana rik'e da hannunta har suka samu waje suka zauna.Nan aka saki kida sossai taro ya soma gudana, an gama gabatarwa an ci an sha Najwa da Shany na gefe suna kus-kus.Can Samar ya mike ya gabatar da jawabin godiya ga mahallata taron,ya juya yana murmushi ya kali Yasiraht hannunsa ya mika sama yana karanta wasu dalamusan tsafi take wasu kwarre guda biyu suka bayyana kan hannunsa.
Cikin kasaita ya tsareta da ido"karbi kisha" jikinta ko ina rawa yake take ta kafa kai ta hausha wajan ya rude da shewa"kinzama sarauniya! Kinzama sarauniya!! Kin zama sarauniya!!! ".Wata giggitaciyar kara Najwa ta saki tai kanta da wata takobi mai tsananin haske, take Samar ya dakawa Yasiraht tsawa itama tai kanta tana shafa zobanta takobi ta bayyana irin ta Najwa nan da nan wajan ya hautsine sai karar k'arafa kake ji na tashi can Yasiraht tai nasarar yankar Najwa a gefan wuya take ta kwala kara tai lau zata fado kasa. Caraf Samar ya rikota Yasiraht ta diro kan kafafunta tana murmushi ganin Najwa a hannun Samar yasa ta jefa masa wani shu umin kallo ta danna zobanta b'at ta b'ace....
KUBIYO MU.
0 comments:
Post a Comment