New Post

Saturday, 1 April 2017

AMANA TA CE 39

AMANA TA CE 
                        By
©Rasheedah .A. Kardam

  39                          
Wani daga cikinsu ya ce tsaya, baiyi musu ba ya tsaya, daya daga cikinsu yace haka zamu kyaleshi baiji a jikinsa ba,ammar adu’ah ya ke tayi na neman tsari, gani basa kusa da shi kuma yana yin kwana zai shiga gidan da suka kama, fakar idonsu yayi yasa gudu don ya sadakar ko ya tsira ko su mishi illa, iya karfinsa yake gudu yazo dai2 shiga gidan kafin ya bude kofar gdn, wani daga cikin yan saran ya kai masa sara cikin ikon Allah bai same sa sosai ba, ya shiga gidan sakata.
Auta jin haya niya ta fito ita da matar gd sun tsaya cirko2, nan matan gd take bata lbr yan sara garin nan take auta ido ya ciko da kwala, yayanta ta tuna ko a wani hali yake oho nan ta fara masa adu’a kariya daga uban giji, suna tsaye agun sukaji an rufo kofa matar rayi daki da gudu sabida tsoro, auta kam ko motsi kasawa tayi da sauri tayi zaure tsaban dakiyar zuciya tana haska wa taga ammar da sauri tazo ta rike hannusa tana hawaye shiko ido ya runtse sabida safin ciwo sai mai da numfashi yake yi kama hannunsa da auta tayi yasa ya bude idonsa, han’nu da ba ciwo yasa yana goge mata hawaye suka nufi daki, dan kwalinta ta yanka biyu ta daure masa han’nu tana masa san’nu ya amsa.
3yrs leter
Garin kaduna wata kyakyawan yarinya na hango cikin farin ciki ta nufi gidan inspector Abubakar ko dana kare mata kalo naga futha ce ta kara girma sosai tadawo cikakiyar mace abun sai mai karatu ya ganta, cikin murna iyayenta suka tareta bayan yar kwarya-kwaryan malimar da aka shirya mata, sadiya ma ta hallara inda yanzu tagama karatunta ta dawo cikakiyar yar’jarida walima ya gudana cikin kayatarwa.
     Baku tambayeni ya labarin pinky yar’rawan kai, hmm ku biyo ni kuji.duniya ta juya don yanzu pinky ko yar motar da take ja babu don yanzu dukiyar baba isiya ta kare ba abunda ya rage masa yanzu sai diabetes da tasa sa agaba har an yanke kafa daya gasa rai kwa-kwai mutuwa kwa-kwai, don shi tun daga duniya yafa ganin nasa saka makon bai ko ina ba matansa sun gujesa don tanzu ba abun duniya.
       Baba sani kuwa ba laifi komai yana tafiya yanda ya kamata don har ya manta da wasu yan’uwansa da kuma yar’auta rayuwansa ya ke ci son ransa.
       Garin bauchi kuwa ammar da auta ci gaba ya samu cikin she kara biyu Allah ya buda wa ammar ya albarkaci dukiyarsa da ya nema da guminsa yanzu shaguna 2 garesa na atamfa da shadda less masu kyau sai na takalma da jakukuna, wani abun dadi sunan auta yasake mayarwa, haka rayuwansu ya kasance cikin jin dadi da farinciki, watara na ammar suna zaune da auta take cemai tana son suje kaduna ko da ba dade wa zasuyi ba, ina son inga futha da sadiya don nasan bayan tafiyata suna cikin damuwa ina son inga wasu yan’uwa, ammar yace ina sane da haka don ba yanzu nake son zuwa ba akwai lokaci in muna raye don na dau wa kaina alkawarin matsawan ina raye sai na dau fansa masu Dad da mum kuma sai an yanke masu baba sani hukunci dai2 da laifinsu, auta har cikin zuciyarta taji dadi ta kuma kara masa fatan na sara.
        5 weeks leter
Ammar ne a shago yana ta fama da jama’a cikinsa ya fara murda masa tun na daurewa abun har yasoma da munsa kafin kace me ammar ya fadi akasa cikin firgici yaron shaginsa ya dauwaya yana son ya kira auwal abokinsa ya kira auta cikin rudewa yake mata bayani akan zasu kaishi asibiti, sai da tayi magana ya ga ba auwal ya kira ba, da sauri ya kira na auwal akwai yace gani a kofar Central market din yanzu zan shigo da gudu yazo suka daukesa sai “NI’IMA CLINIC” auta cikin rudewa ta kira wayansa nan auwal ya daga tana kuka tace kuna wani asibiti ne yace suna ni’ima tace to gata zuwa, duk da bawani yawo take a gari ba mai napep tatsara ya kaita tana zuwa ta samu auwal sai safa da marwa yake a kofar emergency, nan yasoma lallabinta don kuka take sosai, ana cikin haka nurses tafito ta tafito ta ba ma auwal ta kardan magani yace bari yaje ya sayo.
Dr tace tafito auta na ganinta ta nufeta tana hawaye Dr ya jikinsa, ta ce da sauki, ke ce matarsa, auta kamar ta ce aa ta dauka ba wani abu bane kawai sai tace eh nice ok!! Ki biyo ni office to tace Dr tayi gaba tana binta a baya sai da sukaje wani office ta nuna mata kujera ta zauna, sai da Dr ta cire glass din idonta, tace ya sunan ki madam tace Zainab, Dr tace zainab daga ganin ki kamar wayyayiya amma kina abu kamar baki san komai ba, ae yanzu kai ya waye, duk auta na cikin duhu sai da Dr tace mai yasa baki ba wa mijinki hakkinsa kinsan laifin ki kuwa Allah na fushi dake haka mala’iku suna tsine miki, ga shi kinsa mijinki cikin wani hali yanzu in ya fara bin matan banza fa hakki na kanki, don a yanzu haka sperm ya masa yawa don in bai samu ya biya bukatarsa ba zai iya shiga ko wani irin hali, auta sai da taji gananta ya fadi, dake Dr macece nasiha ta mata sosai, tukun tace ta je ta duba mijinta, sai a lokacin suka ga sun dade sosai kusan 1hrs tana mata nasiha kwatance dakin da aka kaisa tamata, auta jiki ba kwari ta fito ta nufi dakin.
         Ammar ko bayan da aka masa allura ciwon cikin bai dade ba ya lafa, auwal a gefensa kusan 40 minutes yayi ya farka dake jinisa da karfi ko alluran bacci aka masa bai cika dadewa ba, nan auwal ya fara masa nasiha akan tunda auta yakeso ya fito ya fada mata ko yanimi wata ya aura, sai da yagama maganarsa kafin ammar ya fara magana da ni bana son takura ma zainab don banga alamar tana sona ba, abunda ya hanani sanar mata kenan kawai shakuwar da mukayi ne, ni kuma banjin zan zauna da wata mace kamar bazan iya mata adalci ba, zuciyata zainab take so, sai hawaye ya fara zuba masa amma zan bama zuciyata hakuri matsawan zainab taki amincewa na auri wata ko don gudun fadawa halaka.
Auta da ta dade da isowa tana shirin shiga taji anakiran sunanta, nan taji duk abunda suke fada kuka takeyi tana fadi bazan iya ba Ammar .
 
Hmmm karkuso ku gani alokaci idi na zaro don tsananin mamakin auta duk halaci da ammar ya miki cab… Ko dai mai take nufi zamuji nan gaba.
Taku a kulum mai kaunar ku 
  
Rash Kardam 

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts