[4:42PM, 7/22/2016] Rash Kardam:
BABBAN KUSKEREN
DANA TAFKA
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
*®NWA.*
*Pg-235~236.*
4yrs latter
Wani kyakyawan Yaro na hango rik'e da teddy a hannusa yana gudu yana dariya ko dana kalli wanda yake bi wani kyakyawa ne fari sol tamkar shi yayi kansa ko dana kalleshi da kyau sai naga kaman Haiydar wata kyakkyawar mace ce ta fito ta ce"Abban Abdul in kun fara wasa kai ma sai kadawo kamar wani k'aramin yaro ya tsaya jin maganar ta Abdul~shakur ne yazo ya kama Abban sa ya dariya ya ce"na kama na kama". Haiydar yayi dariya ya d'agashi ya cilla shi sama duka suna dariya, Assalamu'alaikum jin sallama duka suka juya sai da suka kalli mai sallaman sosai suka gane Falmi ce da sauri tazo ta durk'usa tana basu hak'uri Haiydar ya kau da fuska ya tashi zai tafi Aisha ce tazo ta rungume Falmi ta ce"Aunty na ni bakimin komai ba na yafe miki Aunty na", Falmi ta share hawaye ta ce"nagode ina rokinki dan Allah ki rok'ar min Haiydar da ya mayarni d'akina wallahi nayi nadama". Ta karashe maganan tana kuka Aisha ta rungume ta tace"Aunty kar ki damu Haiydar zai mai daki kuma Haiydar na sonki kawai zugan kawaye ne daman". Falmi tayi godiya ta tafi, Aisha da daddare tasamu Haiydar da maganan dawo da Falmi ya nuna bazai dawo da ita ba, ganin tayi yaki hakan yasa tayi fushi ta juya masa baya kusan kwanan su uku basa magana kafin Haiydar yaga bazai iya jure rashinta ba da kansa yazo ya bata hak'uri ta ce"in ka ga na hak'ura ka mayar da Aunty na". Haiydar da kyar ya yarda sai da suka sanar da su Hajiya tayi murna don ita ma Falmi har gida taje ta bata hakuri.
Aisha ita da Hasna sukayi ta jagale Haiydar shi ya basu kud'i suka had'a kayan akwati aka biya sadaki ranar jumma'a aka d'aura aure, dadadare amarya ta tare a gidan ta Haiydar bayan ya shigo sai da ya tarasu ya musu nasiha tare da kashedi banda fad'a bare hayaniya suka amsa, Aisha ita taje ta taya Haiydar shiryawa ta basa jallabiya mai kyau sabo ta fesheshi da turare ta kama Hannusa kafin ta rakosa Har d'akin Falmi bayan sun shiga da sallama Aisha tana ta addu'a a zuciyar ta don wani irin kishi takeji amma tana ta addu'a ta kori shaid'an cikin sanyi murya ta ce"Aunty ga Ango ki na kawo miki ina muku fatan alkairi sai da safe". Tana fita da gudu tayi d'aki tanahawaye niko Rash na ce"hmm kishi kumallon mata", Falmi ita ta matso kusa dashi ta fara shafa sa daga haka na fito, washe gari Aisha ta shirya musu karin kumalo mai lafiya.
Bayan kwana biyu zaman lafiya a gidan Haiydar ba'a magana dukkansu suna girmama junasu, yau k'awar Falmi ne Gwantsi ta kawo mata ziyara ganin irin zaman da sukeyi nan ta fara hure mata kunne tun kafin tayi nisa Falmi ta ce"kee tsaya da fa da yanzu ba d'aya band in ada kin zugani na d'auka yanzu na nutsu nasan mai nakeyi, dakam nasan *NA TAFKA BABBAN KUSKURE* amma yanzu ina cikin hankali na kinaso in fito muna yawon kan titi tare tare".
*®NWA*
*DEDICATED TO*
*AISHA MUHAMMAD*
*(MAMAN ABDUL SHAKUR)*
*RASH KARDAM*
0 comments:
Post a Comment