New Post

Wednesday, 16 August 2017

BABBAN KUSKURE... 71-80

����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

Pg-71~75.

Indo bata dawo ba sai daf magriba tashigo, da sallamata, Hasna dake falo tana kalo tace"oyoyo Aunty Indo sanu da dawowa, tun d'azu nake jiranki.
Cikin sassayan murmushi Indo tace"sannu Hasna ya kk?. Yasu Hajiya?.
Hasna tace"lafiya lau".
Indo tace"kin dad'e da zuwa ne Hasna.
Hasna tace"eh! Hajiyar ma tazo, bata dad'e da tafiya ba.
"Tace muje tare dake yanzu nan.
Indo ta zaro ido tace"lafiya dai ko Hasna?.
Hasna tayi murmushi tace"lafiya lau mudaije zakiji.
Indo tace"bara na fad'a ma Aunty aika.
Hasna tace"kyaleta ki zo muje kinga Hajiya ke kiranki.
Indo tarasa mai zatace ma Hasna, can tace"karfa ta zage ko ta maren ina tsoro.
Hasna tace"Itama tasan da Hajiya tana kiranki itama.
"Karki damu yanzu zo mu tafi.
Ba musu Indi ta bita suka fito, motan Hasna suka shiga ta su zuwa State Low cost. Cikin nutsuwa suke tafiyar har suka iso katon katafaren gidansu, horn tayi mai gadi ya bud'e mata, ta danna hancin motarta cikin gidan.
Gurin ajiye motoci taje ta ajiye motar suka fito tare, sannu a hankali sushiga cikin gidan, Indo tun zuwarsu taji gabanta na fad'uwa, addu'a tasomayi. Da sallama suka shiga falon ba kowa, Hasna ta nuna mata kujera tace"zauna Aunty na" Hasna taje fridge ta d'auko mata lemu da cup ta kawo mata, saida ta siyaya sannan tace"Aunty na barinje na kira Hajiyan.
Indo murmushi tayi wanda ya k'ara fitar mata da kyauta.
Hasna ta hausa sama zuwa d'akin Hajiya, ta tura da sallama tashiga.
Hajiya tace"Hasna kun zo tare da ita ne?.
"Eh! Hajiya gata a falo tana zaune.
"To kije gunta ina zuwa yanzu.
Hassana ta sauk'o a hankali zuwa falo, kalo ta kunna musu, sai ta mik'e ta koma d'akinta ta d'ebo ma Indo, hotunansu na school ta kawo mata.
Kusa da ita ta zauna Indo ta fara ganin photo, Hasna  tana fad'a mata sunan kwayenta.
Tun Indo na d'ari-d'ari, har ta saki jiki da Hasna, suka fara hira sosai, a tsakaninsu nan Indo kece ma Hasna itama tayi karatu, amma a Jss3 ta tsaya bata ci gababa. Hasna tace"maiya hana ki ci gana Aunty n?.
Nan take idon Indo yaciko da kwalla, ta fara sharewa tace"Mamana ke biyan min kud'in makaranta, ta rasu kuma ba mai d'aukan nauyina.
"Hakan yasa na hak'ura da karatu. "Amma ina son nayi karatu wallahi.
Hasna tace"Allah sarki Allah ya jikanta da rahma.
Indo ta amsa da amin.

              DEDICATED TO
         AISHA MUHAMMAD
    (MAMAN ABDUL SHAKUR)

                ��RASH LUV✍��
[5/28/2016] Rash Kardam ����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

Pg-76~80.

Hasna hira sosai sukeyi da Indo, abun gwanin burgewa in ka gansu ka d'auka sun dad'e da sabawa da juna.
Haiydar da kyar yashifa d'aki wani irin jiri yakeji, cikin zuciyanshi ko cewa yake" amma Fatima ta cuceni gaskiya.
"Mai ta kawo bakinta na cewa na Auri Indo.
"Ina zan kai b'akar mace?.
"Sam ni tsarina bana son b'aka.
"Kuma a b'akar ma yar aiki, wanda bata wayeba.
"Mtssss halama ko secondary school batayi ba?.
"Gashi hajiya fiskanta ba alamar wasa aciki.
"Dole nasan matakin da zan d'auka.
"Don Indo da k'afarta zataje tace ma Hajiya bata son auren. Wani lallausan murmushi ya saki.
Falmi ko tana shiga d'aki ta kira wayar Mum d'inta yakinshiga, ganin wannan kukan bazai fiddata ba, tafito d'akin Haiydar ta nufa tana kuka wi-wi da hawaye.
Qofar ta tura tashiga tana zuwa ta fad'a jikin Haiydar, kuka mai tsuma zuciya ta saki.
Haiydar jin Falmi ajikinsa duk ya rikece, bare yana hannu, take yasa hannusa ya fara share mata hawaye.
A hankali yace"Falmi duk ke kika jawo mana.
Cikin muryan kukan tace"pls kaje kace ma Hajiya ta hak'ura ni bada nufin ayi auren na fad'a ba.
Na fad'a ne irin nagana rainamata, ko kamarta gwara kanemo a waje.
Ajiyar zuciya ya sauke yace"karki damu zanbi duk hanyan da ya dace.
Haiydar ya lalub'o bakin Falmi ya had'a danasa, a hankali yake mata masu salo mai rikitarwa, duk wani gab'ar cikinta yana bi yana aika musu da sak'o mai sanyi.
Cikin nuysuwa ya soma cire mata kayan jikinta Falmi ta rike hannusa, cikin da shashiyar murya yace"kinga irin abun ko mai yasa kike hanani kanki.
"Why! Why! Why! Falmi".
Ganin da gaske wai ita fushi take hakan yasa shikuma bazai iya hak'ura ba, ta k'arfi yasoma cire mata kaya.
Hajiyansu Haiydar wanka zata shiga, cikim gaggawa ta yi wanka tasaka kayanta, da fara'a ta soma sauk'owa k'asa, tana mai farinciki yau zata yi surka ta gari mai nutsuwa.
Don yanda takeyi Husna na yabonta, gakan yasa da Falmi tayi gatse, itakuma ta mayar da gaske, don rasan watarana Falmi zatayi danasani.
A hankali take tafiya ta kusa sauk'owa daga step, ta soma jin muryan da ko a mafarki bazata manta shi ba.
Ko a wani yanayi take bazata manta da muryanan ba.
Duk da shekara ishirin da d'oriya.
Cikin hanzari tasoma sauk'owa step d'in don gani take, tankar mai muryan zai gudu.
Nima Rash ganin haka yasa nace barana biyo Hajiya.

To madu karatu wani murya ne Hajiya ta tsinkayo a falo?.

Shin Hajiya tana gane mai muryan nan kuwa?.

Donjin wannan amsar ku biyo YAR KARDAMAWA.

               DEDICATED TO
         AISHA MUHAMMAD
   (MAMAN ABDUL SHAKUR)

              ��RASH LUV✍��

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts