New Post

Tuesday, 18 April 2017

'YA'YA DA DUKIYA... 21-25

YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-21~25.
Malam suna hira da Khadi Gwaggo ta
fito wani sak’on kalon da Gwaggo ta
aika ma Khadi, yasa ta mike ba sh’iri ta
nufi kitchen ta d’aura girkin dare, sai da
ta magama aiki Gwaggo tazo ta d’auke
tukunyan d’akinta ta sh’iga dash’i duk
abun da suke Malam na kalon su bai ce
mata komai ba. A zuciyansa ya na mai
jin-jina bak’in hali irin na Gwaggo,
Malam ya mike ya fita waje zuwa gurin
da suke d’aukan karatu.
Rabi ce ta sh’igo tayi d’akinsu ta
nufa ta dau naira goman Gwaggo tasa a
wando ta fita waje, alawa ta siya sai da
ta shanye kafin ta dawo gida.
Gwaggo tazo d’aukan raina gomanta don
a siyo mata sikari ta saka a surki, taga
babu kud’i cike da masifa tazo ta danki
Khadi tace”ke barauniya bani kud’i na
da kika d’aukar min wato satan ma
gadonsa kikayi a gun uwar ki.
Khadi tace”Gwaggo ko d’akin ma
ban sh’iga ba ina zaune a nan gurin fa.
Gwaggo tace”oh! Sharri zan miki ko?. Ni
a ya’ya na babu b’arawo ba mu gaji sata
ba sai dai ko gun uwarki ne zuri’an
barayi. Nan take Khadi ta soma hawaye
jin takaicin yanda ake kiran iyayenta da
suke kasa.
Eyeh lalle kin samu gu dan ban
dakaki ba shine kike kuka ko?. Gwaggo
ta d’auko dorina tazane Khadi sai da taji
hannu ta ya gaji tace”naira goman da
kika d’auka a madadin abinciki na yau
da kuma karin safiya. Gwaggo ta juya
zata tafi sai ta dawo ta rike kunne Khadi
tace”saura in Malam ya baki abunci ki
karb’a ki gani ni dake yau a gidan nan.
Ina son ana kiran Sallah ki sh’iga d’aki
ban yarda ki leko waje ba, ina ga
munanan kafarki a guri kin san sauran
ta nufi d’aki.
Taku a kullum mai k’aunar ku
ﺭﺷﻴﺪ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts