*'YAR MAFIYA....*
*Rash Kardam*
*Sanah S Matazu*
*N. W. A*
Page
*22*
Kara ta saki ta zube a gun sumamiya da sauri Yasar sukayi kanta suka zuba mata ruwa ta farfad'o ajiyan zuciya ta saki, sai jin abun take kamar mafarki sai da ta mutsuke idonta taga su Yasar nan ta gaskata abun da ta tarar wani irin kuka mai ban tausayi ta saki tare da tsuma zuciya.
Bayan kwana bakwai duk Yasirah ta dawo shiru-shiru bata son yawan hayaniya mitin ma taki fita haka Samar zai zo yayi ta damunta a satin ne ta fara fita Najwa ko duk a tsorace take don tasan karonsu da Yasirah bazaiyi kyau ba. A haka jarabawansu ya fito tare da Admission d'in jami'a batare da b'ata lokaci ba aka mata komai ta fara zuwa makaranta.
'Dabi'u Yasirah sun k'ara canzawa wanda hakan ya k'ara bama S Marafa tsoro sam yanzu Yasirah bata shakkan kowa komai zatayi gabanta gad'i zata yi shi ba tare da tsoro ko shakka ba ga taurin kunne kamar k'ashi.
Kwanaki sun tafi watanni sun wuce shekaru sun shud'e game da halayan Yasirah ko ba abun da ya ragu haka gun tsafi ma tayi nisa sosai don tafi kowa a tsabibanci kuma in taso kawo mutum sai ta kawo ka wanda hakan ya kara mata matsayi a gun matsafa.
S Marafa ganin halim Yasirah ba abunda ya ragu gashi bata kula samaruka hakan yasaka ya yanke shawaran had'ata aure da Yasar d'an uwanta tunda daman sun shaku da ita sosai.
Yasar ya samu aiki cikin ikon Allah yana gudanar da komai a haka ya koma gidan mahaifinsa da zama sabida barazana da tsorata da yake yawan yi. B'angare guda aka bashi a gidan baya tare dasu don gun kam zamu iya kiransa da gida don basa had'e da Dad d'insa k'ofar su da ban nashi daban sai ya ga dama ya shiga gurinsu.
Yasar yanzu ya gama gane duk abinda Yasirah ke aikatawa amma ba halin fad'a don ko ya zo da niyayar fad'a bakinsa sai ya rik'e gashi hasali Yasar mai wasa a addu'a ne wannan yasa Yasirah ke nasara akansa.
S Marafa ne ya d'aga waya ya kira Yasar ya ce"kazo ka sameni a gida". Ba tare da b'ata lokaci ba Yasar yazo sai da ya gaida Hajiya kafin yaje gun Abbansu ya gaida shi bayan ya zauna Abba ya kira Yasirah nasiha sosai ya fara musu daga k'arshe ya ce“na yanke shawaran had'a ka aure da Yasirah 'yar uwanka kusani ba shawara nake baku ba wannan umarni nane". Yasirah ta d'ago ta fara bama Abba hak'uri tsawan da yadaka mata ne yasata yin shiru take ranta yasoma a zazzala yanayinta yasoma canzawa cikin sauri tafita daga d'akin harda gudunta ta nufi d'akinta. Ko da muka bita nan take d'akin yasoma gir-giza wani wuta ke fita daga bakinta kanta ma naci da wutan kwayar idonta shima wutar yake ci wanna abu ba k'aramin tsoro ya bamu ba na bud'e baki da niyar ihu Sanah tasa hannu ta toshe min baki na.
CI GABAN LABARI....
Rash
Sanah
0 comments:
Post a Comment