New Post

ABUBUWA BAKWAI (7) ABIN KULA GA DAN'ADAM

1. Duniyar da za a barta, me ya kawo hadama? 2. Dukiyar da za a lissafa daya bayan daya, me ya kawo tarata? 3. Rayuwar da zata kare, ina wani farin ciki? 4. Yarintar da tsufa zai zo mzta, me ya kawo takama? 5. Ana sauraren mutuwa, ina wata walwala? 6. Jikin da zai zama gawa, me ya jawo dagawa? 7. Karshe dai makomarsa kabari, me zai sa alfahari? Wanda ya manta da wadannan a ina ya bar hankalinsa? Allah yasa mu dace, yayi mana kyakkaywan karshe. Ameen!

KADA KA RAMA CUTA GA WANDA YA CUCEKA!

Kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka, kai kayi hakuri. Zaka samu abu biyu sakamakon hakan; * Na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. * Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

KADA KA BARI ZUCIYARKA TA ZALUNCEKA!

Kada ka sale zuciyarka ta zalunceka, tabbas zaluncin zuciya ga gangar jiki yake komawa, idan akayi wasa ya zamanto ya shafi rayuwa. Assasa bak'in tunani, yawan zargi da rashin tabbas akan wani aiki, zato, shakku ko kokwanto akan wani al'amari batare da tantance gaskiyarsa ba, shine zaluncinzuciya akan dan Adam. Maza ka hana zuciyarka don akwai hadurra dubu akan hakan.

MAHAKURCI MAWADACI

Tabbas ba kowane dandanon magani ne ke da dadi ba, amma babu shakka shine abu mafi dacewa ga dukkan mara lafiya. A lokuta da dama rayuwa takan dakeka da guduma ta jefaka acikin wani mawuyacin hali, kayi ta fama amma tayi maka tutsu. Amma idan kayi hakuri sannu ahankali zata kwaranye. Hakika ba duk abinda rai yake so yakan samu ba, amma bukata bata taba sauyawa ba kuma bata taba karewa ba. Don haka ka shirya bukatunka da kyau ka bisu daya bayan daya sannu a hankali, kayi gwa- gwarmaya, sannan kayi juriya. Tabbas mafarkinka zai zama gaskiya.

KO KA SAN?

Rayuwa bakin alqalami ce tana bukatar kaifi sannan tana son tsini. Kaifin don ka yanki magauta, tsinin kuwa don ka soki makiya. Haka zalika rayuwa kamar randar ruwan sanyi ce ta kasa tana bukatar tanaji da adani, kodn wata rana ka shayar da masoyanka. Da kyau ka lura da abu biyu a rayuwa; 1. Ka lura da mai zaginka mai aibantaka wata kila wata rana zai iya zama masoyinka mai yabonka 2. Ka lura da masoyinka na kusa mai yawan ambaton alkhairinka, wata kila wata rana zai iya zama makiyinka mai zaginka.

Friday, 7 July 2017

Babbankuskure 46-55

����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

Pg-46~50.

Da sauri yayi kanta, ganin haka, tasoma ja da baya, jikinta sai bari yakeyi. Haiydar yana zuwa kutu ball yayi da boket d'in. Yana huci tamkar wani namijin zaki, yana jin yuwa yafito farauta. Indo ko ta mak'ure a jikin gini, sai b'ari take, don tunda take a rayuwanta, bata tab'a ganin fushi irin na Haiydar ba. Don in ta kali fuskansa, sai taga kamar na zakine yazo gabanta yana huci. Kanta ya nufo yana cewa"waya kawo ki gida na?.
"Meye had'in ki da wanke bedsheet d'in da na kwanta da matata.
Indo ko gani tsanani fushi ya had'u da tsoro, bata san lokacin da ta sulale, kasa sumamiya ba.
Haiydar ganin idonta sun kafe, hakan ya tabbatar masa da suma tayi, wuceta yayi ya nufi cikin gida, da fushinsa.
Falmi ko tana zaune a kan gado, takecin indimiee, wani gululun bak'in ciki ya k'ara tokaraansa, wannan wani irin iskanci ne?. A kan gado take cin abinci. "Mtsss yayi tsaki".
Cikin muryan shagwab'a tace"My Haiydar ka dawo?.
"Bayan tafiyanka yunwa ta dame ni da...
"Keee wa ya kawo min wannan bak'ar mai ido kamar na mage, gida na kuma don iskaci da rainin hankali, zanin dana kwanta da ke take wankewa.
"Mtss shikenan nikam nagama yawo, yarinyanan zata rainani.
"Ta gama sanin sirina.
"Shikenan nikam kin gama dani mtsssss.
Falmi tace"to ya kakeso nayi, ni kasan ko a gida ita, take min wanki. Hatta under wears d'ina ita take wankewa.
"Mtsss sai kiyi tayi ae.
Falo ya fito tare da bata guri, ganin zaman gun bazai masa ba, ya nufi d'akinsa cike da kunan zuciya.
Falmiko tana gama cin abinci a gun ta bar kwanon, ta sake kwanciyarta.
Indo ko ta dad'e a sume a gun, sai da ruwan da ya zuba ya iso jikinta, hakan yata daman farkawa. Hasken ranane ya haska mata ido, da sauri ta mik'e, cike da tsoro, tace"yanzu ta koma gidane ko ta shiga gidan?.
Wata zuciya tace"in kika tafi baki gama aiki ba, wani tashin hankaline. A hankali tashiga gidan d'akin da Falmi take ta nufa, poss d'inta ta d'auka, tafito falo da shirin ko ta kwana.
Haiydar ne ya fito, nan rake ta soma b'ari. Cikin fushi da muryan hargowa yace"ke mai kikeyi a cikin gidan nan da baki tafi ba?.
Kasa bashi amsa tayi masifa ya cigaba dayi, wanda hakan ya tashi Falmi ta fito. Haiydar janyo Indo yayi yace"ki fita min a gida kar na k'ara ganin k'afarki a gidan nan sai na karya ki.
Falmi tace"miye haka wacce zata min aiki zaka kora?.
"Kasan dai ni ban iya aiki ba ko?.
"Ita zata na mana girki da sairan aiki.
Haiydar ya kulu iya kuluwa, yace"kee miye aikin ki da baza kina aiki ba?.
"Ni fa ka ganni ko agida ruwan Lipton sai an dafa min.
Cike da ta kaici yace"baki isa ba to ni bana son girkin yar aiki. Ya wuceta fuuuu yayai d'akinsa qofar ya bako ya kwanta yana mai takaicin abunda ya faru, "daman haka halin Falmi yake?.
Falmi tana zuwa d'aki Mum d'inta takira, sai da ta sanar mata da komai.
Mum tace"yayi kad'an daga zuwanki zai fara fida halinsa to bai isaba wallahi.
"Yar'aiki  kuma kamar ta zauna daram, dole Indo ta dawo cikin satin da zamu shiga, tunda baki saba aiki da kanki ba.
"Ki bar min komai a hannuna dole yayi biyayya.
Falmi cike da jin dad'i ta mata sallama, ta kashe wayar.

                 DEDICATED TO
            AISHA MUHAMMAD
     (MAMAN ABDUL SHAKUR)

            ��RASH LUV✍��
[5/28/2016] Rash Karda ����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

Pg-51~55.

Indo tana fita, kuka take maras sauti, tana rokon Allah ya fitarta ya bayyana mata da danginta. Haka har ta iso gida, tana zuwa bata huta ba ta kama wasu ayyukam, da zatayi ma Hajiya, gashi sun k'aru sabida yan biki.
Falmi kuwa bata sake leko falo ba sai dare, da yunwa ya dameta, wasu matsatsun kaya tasaka. Haiydar na falo yana kalon tashar BBC WORLD ta shigo sai karairaya rakeyi, kalo d'aya ya mata ya kasa d'auke kansa, kasancewan bai da hak'uri. Take ma manta fushin da yakeyi da ita, ganin taki zuwa kusa dashi, tashi yayi a hankali yaje ya rikota, cikin rad'a yace"haba baby na fushin ne har yanzu?.
Sai da ta d'anyi farrr kafin tace"ni yunwa nakeji fa.
Hannu ta ya kamo sukaje dinning, asai yamusu take away. Nan yaringa bata a baki tana ci sai da ta k'oshi, ya sun kuceta sai d'akinsa, nan labarin ya canza.
Hajiya Fiddausi, sai datayi shige da fice, tasamo kan Haiydar, ya yarda Indo ta dawo gidan da zama tana musu aiki. Hajiya tace"ma Falmi ta bari sucika wara sai Indo tazo, a kwai abunda takeyi ne. Falmi badan taso ba ta amsa ma Mum d'inta.
Kwanaki sun tafi yau 3weeks da bikin Falmi, tasoma caza ma Haiydar kai, Haiydar duk lokacin da yazo da buk'atarsa Falmi tayi burus dashi, ko kuma in tabashi had'in kai sau d'aya, to ba zai k'ara ba. Haiydar har ya d'an rame.
Mum takira Falmi tace"to ba zama zakiyi ki zuba masa ido ba.
"Zaki fara tatsansa ne mu had'a jari.
Falmi tace"Mum to taya zan tatse sa da yawa bacin akwai komai a gida?.
"Mtss kee sai kace ba mace ba, bakisan tanda zakiyi ki samu kud'iba.
"Kina tambayansa mana.
"Ko kuma in yazo kwaciyan aure dake, kice sai yazuba kud'i ke bazaki iya ba.
Falmi tace"to Mumcyna hakan zanyi ma kawai.
Mum tace"yauwa yar albarka. (Kira gareku mata masu irin wannan galin, idan mazajenku sun zo muku da buk'ata, kuce sai sun baku kud'i, wannan BABBAN KUSKURE NE, aikata hakan haramci ne dan Allah akiyaye).
Da yamma Falmi tayi wanka tayi kyau sosai, kasancewan bata girki Haiydar ke sayo musu tayi zaman jiransa.
Haiydar ko da sallamansa ya shigo gida, tunda ya kyalo Falmi, ya had'iye wani yawu. Take yaji jikinsa ya mutu, dining ya wuce ya ajiye abinci da ya sayo musu, Falmi ko bata iya cemasa sannu da dawowa ba. Sai shine yace"ya gida fatan kin na lafiya?.
Sai da ta d'au lokaci, kafin tace"lafiya lau nake. 'Dakinsa yaje ya watsa ruwa ya saka 3quater da singlet ya fito, a dining ya ganta. Shima can yaje ya zauna, ya kaleta yace"ki d'auko plate da spoon kiyi serving d'in mu. Sai da ta ya tsina fuska taje ta d'auko ta dawo, har ta zauna yace"ruwa fa ko sai mun gama ci za'a d'auko?.
"Mtssss  ta yi tsaki ni na gaji da yawan tashi.
Sai da suka gama ci, Falmi ta zo jikinsa ta zauna, don yau tanason ta fara wankansa, tunda tagane shi mai yawan bukatane, wasani tafara masa, wanda yasaka hankalinsa tashi, gashi kwana biyu Falmi ta hanasa kanta.
Shima biye mata yayi suka dulmuya, sai da taji zai wuce ta mike zubur, cikin dashashiyar murya yace"Falmi karki ki amincewa dani.
"pls ki taimaken una cikin yanayin bukata.
Kafad'a ta ya tsina tace"ni bazan iya ba.
Cikin yanayi tausayi tafara"pls My Falmi ki taimaken dan Allah ina buk'atarki sosai.
"Duk abunda kike buk'ata zan miki matsawan zaki bani had'in kai.
Sai da tayi wani murmushin mugunta tace"kayi alkawari ina fad'i abunda nakeso zaka bani?
Da sauri ya amsa mata"da eh! Zan baki koma miy ne.
Falmi tace"kud'i nakeso masu yawa.
"Haiydar jikinsa na b'ari ya tashi ya duba Aljihun wandinsa ba wani kud'i masu yawa, sai 10k ne kawai don d'azu a gun aiki, yayi sadaka da kud'ade'en da ke jikinsa, ma masu bara, duka dubu goma ta d'ebo yace"ga abinda suka rage min nan.
Falmi tace"nawane wannan don naga da alama basa da yawa?.
Haiydar yace"10k ne kawai bana da kud'i a jikina suna banki.
"Mtss mai dubu goma zasu min,  asai baka shirya jin dad'i ba.
Haiydar kamar zaiyi kuka yace"haba Falmi ki taimaka ma halin dana ke. Zugunawa yayi akan gwiwansa, don bayason abunda zai b'ata mata rai.
"Mtsss to mai kake so na maka ne?.
Da rauri yace"ki taimaka min.
Ummmm"zan iya barinka kayi kiss a 10k amma fa da sharad'in bazaka wuce haka ba?.
"Eh na yarda in har zaki bari namiki d'an kiss d'in.
Okay!. Da sauri Haiydar ya taso yazo zai rungumeta, Falmi ta ja da baya, tana masa kalon raini wayo.
     

                 DEDICATED TO
            AISHA MUHAMMAD
    (MAMAN ABDUL  SHAKUR)

             ��RASH LUV✍��

Babban kuskure.. 31-45

����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

Pg-31~35.

Firdausi ta kirata, suka taho tare, can gefe ta zauna, sai da ta gaidasu. Alhaji Hashim yace"baiwar Allah ya sunanki?.
Matar nan tabashi amsa da"sunana Safinatu".
Alhaji Hashim yace"matana tamin bayani yanda kika fad'a mata.
" ko zan iya sanin mai ya kawoki Bauchi?.
" nan take matar ta fara kuka, tace"Ni sunana Safinatu, ni haifafiyar garin Yola ce.
"Ina gaban k'anin mahaifina, na taso cikin kulawa, har na girma, duk ran laraba, ake cin kasuwar garin mu, kuma duk ranan laraba, na ke kai tallen nono, cikin garin mu na Girei, a haka har Allah, ya had'ani da Muhammadu, shikuma yana kawo shanu, duk ran kasuwa, yana da zama'a Rugan Ribad'o. Ko da muka dai-daita kamu, nan iyayena suka mana aure. mijin dana aura ya kasance yanada garken shanu sosai, hakan yasaka wasu ke jin haushinsa. Har suna masa gorin zuwa yayi, duk da shima bafulatanine, kwanaki suka tafi, kulum garken shanunsa sai hab'aka yakeyi, hakan yasa mak'iya suka fara kawo masa hari. Tundaga likacin ya fara sanar dani, duk da banjin dad'i, ina fama da laulayin ciki. Bayan wasu watani, lokacin cikina ya fito, dadadare muna kwance, wasu yan rugan mu suka zo donsu kashe, Muhammadu su kwashi dukiyarsa, ganin hakan ya d'ebi, kud'i yaban da wasu hotuna, tare da awarwaro, yace na rike wannan. Ya kad'a shanunsa muka d'au hanya muna tafiya, su Sale suka biyo mu, sunyi artabu da Muhammadu, da kyar Allah ya basu ikon kwad'a masa sanda'a kafad'a, ganin bazai iya kare kansaba, yace"Safinatu ki gudu ki tafi garin Gombe ki nimi yan'uwana, suna Gombe. Kafin yayi wani magana sun kwad'a masa sanda take jini yasoma zuba, a gun ya fad'i ko motsi bayayi. Ganin ina kuka Sale yace"ku kamata don zata iya tona mana asiri, jin haka nasa gudu.
Haka har Allah ya taimakeni na fito bakin titi, saiga mai mota na shiga ya kaini, cikin gari nasamu motar Gombe ta tashi, sai na Bauchi, nan wasu sukace, idan ina sauri na shiga na Bauchi, haka nashiga motar Bauchi, ko da na iso yan kud'i na sun k'are, hakan yasa nayita yawon bara, gashi bansan ta inda zan fara niman dangin Muhammadu ba.
Alhaji Hashim ya nisa, Yace"naji labarinki, kuma a yanzu niman mutum batare da wani Address ba, ba k'aramin tashin hankali bane. Awarwaro ba zai zama abun shaidan da har za'a gano suba. Firdausi tace"Alhaji mai zai hana tana mana aiki sai ana biyanta, tunda Lami tayi aure wancan Satin.
Alhaji yace"haka za'ayi.
Ya kali Safinatu yace"Safinatu sunanki ko?.
Tace"masa eh! hakane.
Yaci gaba da cewa"zaki iya yin mana aikatau, ana biyanki duk wata?.
"Kuma zamu baki d'akin da zaki zauna har sai lokacin da kika buk'aci tafiya?.
Cikin girmamawa tace"eh zan iya.
Alhaji yace"Alhamdulilah! Firdausi zata gwada miki komai.
"Sanna salary ki a wata dubu shabiyar.
"Tace"nagode Allah ya ban ikon kiyaye komai.
Haka tamik'e ta koma d'akin, tundaga wannan rana tadawo itace wankin kayan Fatima da wanke-wanke, ga shara, abunci sai da Firdausi ta koya mata. Duk wani abu ita takeyi. Ana haka  har ta haihu, cikin ikon Allah a gida bataje Asibiti ba. Ranan suna yarunya taci Sunan Aisha, amma tana kiranta da Indo, haka rayuwansu ta kasance.

               DEDICATED TO
            AISHA MUHAMAD
   (MAMAN ABDUL SHAKUR)
     
             ��RAS LUV✍��
5/27/2016] Rash Kardam ����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

Pg-36~40.

Aishatu Indo ta girma sosai,, gata da wayo, Indo tana d'ibi dani amma wasu abubuwanta na haifinta ne, hatta muryanta irin nasane, kwayar idonta, yatsun k'afarta duk nasane, bak'in fata na ta d'auko. Gata da gashi kamar me, ganin Indo tayi wayo ga Fatima tana zuwa makaranta, ko d'an abu ya had'asu, karara Fatima ke mata gori, Aisha tayita kuka. Hakan yasa na duba wani private school d'in da ke nesa da gidan mu nasata, 30k ne kud'in makarantan, amma duk term zan bada 10k hakan yasa na sakata a Sky criest, kulum da sassafe zan shiryata, na d'aukota a kafad'ana da kafa zan kaita. Ina dawo gida nayi aikina da wuri inje na d'aukota. Da kud'in aikina nake biya mata, dubu shabiyar, duk wata ake bani kud'in aiki. Kuma ba abinda nake da kud'in kasancewan su suke ciyar damu. Sai in Sallah yazo nayi mana kayan Sallah.
Ahaka har Aisha tashiga Junior school, ina biyan mata, na sata a Islamiya, sam Aisha bata isa tayi k'awance da kowa ba Fatima wanda a tana Senior Secondary school, ta sata a gaba, yanzu Aisha itama tana tayani aiki, sosai mukeyi tare. Fatima tana SSS3, a Doll pine Maria, ta canza sunanta daga Fatima ta dawo Falmi, hatta Baban da Falmi yake kiranta, tana harka da kwaye wayayu, masu nutsuwan kenan Meesha da Xahra BB. Sune masu hankali. A haka ta kamala secondary school d'inta. Ko da result yafito sam baiyi kyau ba. Hakan yasa ta fara diploma, tana karanta estet management. Tana final semester, ranan ta fito a motarta, dai-dai Bauchi club, motarta ta tsaya. Ga dare ya farayi, tun daga nesa ta hango wani mota Range Rover baka, bakowa bane aciki face Aliyu Haiydar. Da kamar zai wuce ganin macece tana buk'atar taimako hakan yasa ya, ko da yazo da sallamansa ya mata, ta amsa. Yace"lafiya mai ya samu motarkin?.
"Wlh ina tafiya naji k'aranta ya canza, kafin nayi wata-wata ta tsaya. Bud'e motar yayi, yayi nasa iyawar taki tashi, hakan yasa yace"in bazaki damuba in taimaka miki.
Tace"ba matsala. Wayarsa ya kira mai masa gyara yazo ya d'au motarta, tare ma da bata address d'insa, abunda yasa bata damu ba, taga Haiydar cikin kayan Police, shiyasa tasan ba zai cutarta ba.
Motar suka shiga ya kaita har qofar gidansu, zata fita tace"nagode da taimako gashi zamu rabu bamu san juna ba.
Murmushi yay8 yace"Sunana Aliyu Khaleeb Baba, ama ana kirana da Haiydar wasu kuma sukan ce min AK Baba. Cikin yanga tace"wooow nice name!".
"Ni kuma sunana Fatima Hashim Marad'i, amma ana kirana da Falmi.
Cikin fara'a yace"suna mai dadi.
"Ku ya  Niger ne?.
Tace"masa eh zamane ya kawo mu Bauchi.
Nan sukayi exchange d'in phone number, tamasa godiya tashiga gida.
Kwanki sun tafi, yanzu Aisha tana Jss3 suna third term,  ranan jumma'a ranar da Aisha bazata manta ba a rayuwanta, shine randa ta wayi gari mahaifiyarta ta rasu, ranan tayi kuka, ta dawo bata kowa bata da gata sai Allah. Bayan kwana bakwai Hajiya Firdausi tace"yanzu sai ki maye gurbi Uwarki da aikin da kike ko kuma kisan inda dare ya miki.

                 DEDICATED TO
           AISHA MUHAMMAD
      (MAMAN ABDUL SHAKUR)

             ��RASH LUV✍��
[5/27/2016] Rash Kardam ����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

Pg-41~45.

Aisha Indo ba yanda ta iya, haka taci gaba da aiki a gidan, Hajiya da kanta ta rage mata Salary zuwa 7k, hakan yasa bazata iya d'aukan nauyin, karatunta ba ta hak'ura.
Aliyi Khaleed Baba, tun randa yaga Falmi ya rasa nutsuwarsa, kasancewan ya ganta irin matar da yakeso, gata fara sol, don shi tsarinsa bai son bak'ar mace. Masu karatu zamuso sanin,
  WAYE ALIYU KHALEED BABA(AK BABA).
Alhaji Khaleed Baba asalin d'an Bauchi ne shi, cikin k'aramar hukuman Sakuwa, dake garin Misau. Yata so cikin garun Bauchi yana aiki a kar-kashin Treasuring a yawon aikisa yaje garin Gombe suka had'u da Hajiya Khairat wanda take da zama a garin Gombe.
A haka akayi auresu da Alhaji Khaleed ya d'aukota suka dawo cikin garin Bauchi,
Suna da zama a State Low cost, bayan aurensu Allah ya azurta su da d'a Aliyu, sai da Aliyi ya girma sosai kusan shekara 12 kafin aka Haifi k'anwarsa Hasna. Wanda yanzu itace auta. Wanan kenan bari mu dawo labari.
Haiydar yakasa hak'uri takanas yazo gidan su Falmi, tun daga ranar suka sasanta kansu. Soyayya mai k'arfi tashiga tsakaninsu. Kusan kulum suna tare da juna, wata rana yazo gun Falmi tun daga nesa yaga, Aisha zata shiga gidan sam bata lura dashiba, horn ya mata sosai don tayi nisa cikin tunani. Sai da ya taka burki ya fito ya fara zazaga mata masifa. Ko da Falmi tadawo ta ga sai huci yakeyi, tace"My Haiydar mai ya faru haka?.
Nan ya fad'a mata laifin da yarinya tamasa.
"Mtsss miye na d'aga hankalunka, akan wannan yar shegen, da ba'a san ubanta ba.
"Uwarta tazo tayar mana ita.
Nan taba ma Haiydar kabarin komai harda k'arya aciki. Madadin Haiydar ya tausaya mata sai yaji haushinta.
Kwanaki sun tafi, magabatan Haiydar sun zo ansaka ranar Aure wata d'aya, sai shiri sukeyi, Falmi tasha gyara sosai, Falmi kasancewar yar casu ne, event tashirya bana wasa ba, tun daga rantalata suka fara event, har Friday idan nace zan tsaya baku labari, events d'in bikin nan da yanda komai ya kasance, charged d'in wayata zai d'auke, ban gama shiba. Ranar Friday aka d'aura aure. Duk wani abun al'ada anyishi, ranar yini da daddare abokai suka raka ango, sai da sukayi yan barkwanci, kafin suka musu sallama suka tafi. Haiydar ya rakasu ya dawo, Falmi tana ganin ya dawo, tazo cikin shagwab'a tafad'a jikinsa, azuciyar Haiydar kuwa cewa yake"wanna wata irin Amarya ce ba kunya, amma sai ya share wata zuciya tace"Son da take maka ne yasaka haka.
Falmi bata bari sukayi Sallah farinci da godiya ma Allah ba, ta fara aikin sha-shafa Haiydar tare da masa wasu salo, Haiydar kasa jurewa yayi ya d'auketa sai kan bed. Salon da ya mata, ya rikitata ranar Falmi taji jiki, kasancewa ta kawo budurcinta, Haiydar irin Mazan nane wanda zamu iya cewa shi Hariji ne, a ranan sai da ya gurjeta sau uku.
Da safe sai da yayi wanka yayi Sallah kafin, yazo ya mata wanka ya gama shiryata kena, wayarsa tayi k'ara ya d'aga, ganin daga office ne, ya kara a kunnesa tare da fad'in "Hello" daga d'aya b'an gare akace"Sir kazo Commissioner ne yazo yana son ganika yanzu, akan wani case d'in da'aka kawo.
Ba yanda ya iya dole ya fita, Falmi ko tunda taga 8:00 bai dawi ba, ga bedsheet d'in da suka kwanta ya b'aci, ko yaye wa batayi ba. Waya ta d'auko ta kira, Mum bayan sun gaisa tace"Mum ki turo min da Indo zata min aiki.
Mum tace"ke kina da glhankali kuwa?. "Kice na turo miki Indo gidanki.
Falmi tace"Mum Haiydar bayanan ankirashi a gentle a gun aiki, gashi bana iya tashi ne fa, kuma ban karya ba.
Mum tana jin haka ta gane sunyi abun garin, sai da tayi murmushi tace" gata zuwa yanzu.
Mum ta bama Indo kud'in mashine ta hau tazo. Sai da ta mata girki ta jera mata, Falmi tace"kee jeki d'akina ki yayi bed sheet d'in ki wanke. (Mata kira gareku, ku kasance masu kiyaye duk wani abun da ya shafi Sirrin Auratayyan ku, bakomai ake fad'a ba ko anuna, wanna Sirri ne tsakaninku).
Indo tunda ta gani, sai taji ba dad'i, amma ba yanda ta iya dole sai ta wanke. Ta d'ebo ruwa kenan ta fara wanki, sai ga Haiydar yashigo, tunda ya hango ta, yaji ransa ya b'aci. Ko da ya ajiye mota ya fito, dole sai yabi gefenta ya shiga gidan kasancewar qofar main falo yana rufe, yana isowa kusa da ita, karaf idonsa ya sauka kan bedsheet cikin kuna rai da zafin zuciya gami da wani kara yayi kamta da gudu.
Ni ko Rash ina ganin haka na tattaro yan komatsena, nasa ka gudu dan kar Haiydar ya had'a dani.

             DEDICATED TO
         AISHA MUHAMMAD
   ( MAMAN ABDUL SHAKUR)

              ��RASH LUV✍��

Babban kuskuren 16-30

[26/5/2016]Rash Kardam ����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

Pg-16~20.

Shewa sukayi, hiransu ta yaushe gamo sukeyi. Indo ko kitchen tashiga, ta d'aura girki, tukun tayi side d'in Falmi, sai da ta gyara ko ina, sannan ta je bedroom d'in Haiydar ta gyara, ta d'ebo kayansa da sukayi datti, ta wankesu, tana duba abinci. K'arfe uku da ta gama komai, ta jera a dining.
Falmi tace"ki kawo mana abincin mu falo".
Sai da da d'an rusuna tukun tace"to Aunty".
Taje ta zubu musu a cooler da plate takawo, Falmi cikin isa tace"kee wazai kawo miki ruwan ko ni zanje ba d'auko?.
Indo ta rusuna tace"ayi hak'uri zanje na sauke abune akan wuta.
"Mtss wuce ki d'auko kafin kiyi abunda zakiyi.
Indo ta jera musu komai agun gar zata tashi Falmi tace"ni zanyi serving d'in ko sai na fad'a miki?.
Indo ta tsuguna ta jera musu komai, tasaka ta mik'a musu, tukun ta mike ta nufi kitchen, don k'arasa sauran aikin da takeyi.
Sadeey tace"Falmi baki da k'yau, gaskiya kina juya yarinyan nan.
"Irin tsawan da kike mata ni har ta ban tausayi wallahi.
Meesha tace"niko yarinya k'yau ta min gata black beauty.
Falmi ta b'ata rai tace"mtss dad'ina da ke rashin ganewa, mai maza zasuyi da bak'ar mace.
"Bakijin yanzu cewa suke su Fara ko da mayya ce, suna sonta.
Xahrah tace"Falmi ae bazaki gane ba, sirrin k'yau yana tattare da bak'ar mace, don fara inda za'a kwashe farin ba komai zaki gani ba zai tsaban muni.
"Amma magaanan gaskiya Indo ta had'u ba k'arya.
"Sai dai rashin gyara da wayewa ne ya mata cikas.
"Ki kali tsarin jikinta mana, irin shape d'in da maza keso ne.
Take Falmi ta b'ata rai jin an kushe farare, don bak'aramin ji take da haskenta ba, gani take tafi kowace mace kyau.
A haka har suka cinye abinci su, Indo ta fito ta tattara kwanuka ta kai kitchen, tana ajiyewa ta k'oma d'aki, ko zama batayi ba taji k'aran shigowar motar Haiydar. Sai da gabanta ya fad'i, addu'a tafara yi, sabida duk lokacin da suka had'u, bata kwashewa ta dad'i.
Haiydar cikin takun isa ya shigo ckin gidan da Sallamansa, su Sadeey suka amsa, ganinsu yasa ya d'an saki fuska don yasan k'awayen Falmi ne sosai.
Gaisawa suka kafin ya wuce d'akinsa, yana shiga wani sassayan, k'amshi ya bugi hancinsa. Ajiyar zuciyzuciya ya sauke, kayansa ya cire ya nufi toilet, yayi wanka ya fito, k'ananan kaya yasaka, sabida ga bak'i, da na shan iska zai saka.
A hankali ya tako zuwa falo, Falmi tun da taga ya fito tasan in ba'a yi serving d'insa ba, zata sha surutu, cikin muryan isa ta fara kiran, Indo! Indo!
Indo dake d'aki jiki sai b'ari yake ta fito da sauri, ta rusuna a gaban Falmi.

                DEDICATED TO
                  AISHA MUH'D
    (MAMAN ABDUL SHAKUR)

             ��RASH LUV✍��
[5/26/2016] RashKardam ����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

Pg-21~25.

                    Notice
   Masu karatu, na cire Sadiya a k'awar Falmi, zan maidata k'awar Indo, sabida wani dalili, ku kasance da YAR'GIDAN JARAWA.

Falmi tace"ke kwai bakinsan aikinki bane?.
"Bakiga Haiydar ya dawo bane?.
"Kije ki zuba masa abinci.
Indo ta mik'e jikinta ba k'wari, sai bari yake, ta nufi dinning area, Haiydar ko tun da ya hango ta, yayi yar karamar tsaki, cikin zuciyarsa ko cea yake"wato falmin bata ji, nace mata bana son aikina tana saka wannan wariyan taki ji.
"Dun taga ina qaunarta da yawa bana son abunda zai bata min rai.
Indo tana zuwa dining ta fara serving d'insa, sai da ta zuba maza jelop d'in shinkafa yaji Salad, sai k'amshi yake tash, gaskiya Indo ba ya bace gurin girki, don ta taso cikin horon aiki, shiyasa bata samun matsala game da iya girki, gyaran guri. Wani lokacin in tayi decoration ta gyara ka d'auka, ba ita bace tayi, wasu daban akayi hayansu sukayi.
Sai da ta zuba masa shinkafan ta tura masa gabansa, hannuta sai rawa yakeyi, a haka ta d'auko kofin glass ta zuba masa zob'o drink da tayi, ta d'auko zata ajiyea gabansa, hannuta sai b'ari yakeyi, bisa tsautsayi ya sub'uce ya fad'i aiko sai jikin, Haiydar, take rigansa tarine.
Nan ganjin cikin Indo suka soma shooky, hawaye ta fara yi.
Haiydar cikin b'acin rai yaga yanda ta b'ata masa jiki, ransa ya b'aci ya rasa mai zai mata, mikewa yayi har yazo zai tafi, sai ya fasa, d'auko juke d'in zobon yayi, ya shek'a mata a fuska. Ae ko sai cikin idonta take tafara mutsu-mutsu, tana niman hanyan saukowa, ganin abunda ya mata bai sheshi ba, sai da ya bari tana lalub'en hanya, ya saka k'afarsa ta fad'i timm! A k'asa, aiko ba shiri ta saki k'ara shiko ya mik'e abincin da bai ciba ya kima d'akinsa.
Duk abunda ya faru a idon su Falmi, cikin jin dad'i tace"kun gani ko ita kanta yariyan tsoronsa take, bare shi uban gayya da baya son ganinta.
Xahrah tace"to ki dai bi a hankali, don in wahala yayi wahala karta gudu.
Falmi tace"ina zata je wa take dashi a Bauchi.
"Ina ga ma la Uwarta cikinta tayi tazo ta haife ta.
"Don tun zuwanta sai tana cemana ubanta Indo na raye, kulum maganan d'ayq kenan.
Meesha tace"Xahra ya kamata mu wuce fa yamma tayi.
Falmi tace"kai Messha wato ke kike zugawa ku tafi ko?.
Duka sukace yau ai mun dad'e, mu zamu wuce sai gani na biyu.
Falmi tarako su har gate kafin ta koma ciki.
Haiydar ya fito zai wuce Falmi tace"darling bazaka ci abincin bane?.
Ko kalonta baiyi ba yace"nagode fita zanyi.
Ya na fita motarsa ya shiga bai zarce ko ina ba, sai k'aton katafaren gida, na alfarma, tun daga kan gate d'in, gidan abun kalo ne, horn yayi mai gadi ya bud'e masa, ya danna hancin motarsa, cikin gidan, gurin da'aka tanada don ajiye motoci, nan ya nufa, sai da ya ajiye motar ya fito. Gidan yana da girma sosai ko da na kali harabar gidan, zagaye yake da fulawas ja da yelo, sun matuk'ar k'awata gurin, a hankali yake takawa har yashiga cikin gidan, falo ya fara tararwa, ko da na kali falon, gaskiya ya tsaru komai na ciki Silver colour ne da baki, abun gwanin burgewa.
Daga nesa na hango wata yarinya wacce bazata gaza 17yrs ba, tana danna waya, farace sol kamar Haiydar, kuma suna d'an kama amma shi yafita kyau sosai, da sallama ya k'arasa shiga ciki, Hasna ta mik'e tace" Yaya Haiydar sannu da zuwa.
Cikin fara'a ya amsa mata, zama yayi a d'aya daga cikin kujerun dasuke falon.
Yace"Hasna kawo min abinci naci".
Cikin tausaya ma Yayanta, mik'e wa tayi ta nufi kitchen, abinci ta kawo masa, sai da tayi serving d'insa, tukun koma gefe ta zauna.

                DEDICATED TO
                 AISHA MUH'D
     ( MAMAN ABDUL SHAKUR)

              ��RASH LUV✍�� [5/26/2016]RashKardam ����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

Pg-26~30.

Cikin zuciyarta ko tana tausaya ma yayanta, wanan wani irin aurene ace mutum sam bai isa da matarsa ba, ko yasata abu batayi, ga rashin kunya, ga kin jama'a, Hmm Allah ya kyauta.
Sai da ya gama cin abinci, Hasna ta kale Yayanta tace" Yaya Ya Indo?.
"Ina son yarinyan tana da hankali, ga kirki wallahi, Hajiya ma tana yawan tambayanta.
Wani harara ya sakar mata, wanda yasata jan bakinta tayi shiru, a zuciyarta ko cewa take"wai me Indo tayi ma Yaya ya tsaneta, ko sunata bai son a kira, kuma ni tafin Falminsa sau dubu wallahi.
"Mtss ina ma da itace matar yayan.
Maganan Haiydar ne ya dawo da ita daga duniyar tunani, da ta luka.
"Hasna ina Hajiya fa?
"Tana d'akinta.
Mik'ewa yayi ya haura sama.
Haiydar na fita Falmi ko kafad'a ta d'aga, alar ko in kula ta d'aki ta koma, WhatsApp ta hau taci gaba da chatting da friends d'inta.
        TUSHEN LABARI
Alhaji Hashim Marad'i, Haifafen d'an Niger ne, ya kasance mutum ne mai neman na kansa,  Allah yana bud'a masa, a haka har ya auri matansa Firdausi, bayan aurensu da kwanki ya tattara, yan dukiyarsa ya baro gari, ya dawo Bauchi da zama, shago ya bud'e, cikin ikon Allah, kasuwansa ta bun k'asa, Allah ya sanya ma dukiyar Albarka, nan da nan ya shahara ta ko ina a garin Bauchi.
Ana haka Matarsa ta samu cikin karkuso kuga kulawa da tattali, har cikinta ya kai wata tara, ana haka nakuda ya tashi, baiyi wata-wata ba sukaje Asibiti, nan aka karb'e su, sai d'akin haihuwa.
Bata dad'e sodai ba ta sankato, yarta fara sol, Nurse suka gyarata, suka dawo gida, ranan suna Yarinya taci sunan Fatima, Alhaji Hashim ya d'au son duniya ya d'aura ma fatima, baya son abunda zai tab'ata, Firdausi ma duk d'ayane, kula ta musamman suke bata, har yarinya tayi wayo ta girma sosai.
Fatima tana da shrkara biyar, tayi wayo ko ina tana zuwa har sun sata a makaranta.
Wani safiya ranar asabar, anyi ruwa sosai wata mata tana d'auke da k'aramin ciki, tazo qofar gidan Alhaji Hashim ta zauna, sai b'ari takeyi, ana haka Alhaji ya fito, ko da ya ganta, sai yaji ta bashi tausayi sosai. Mai gadi ya kira yace"kaje ka shigo da ita, gida ya koma ya samu Hajiya Firdausi, yace"ga wata mata tana buk'atar tai mako, ki bata duk abunda ya dace. Tukun ya fita.
Firdausi tasaka a ka shigo da matar sai yatdina take, ganin kayan jikinta yasa tace"ke biyo ni boys quater ta kaita, nan ta ce bara na kawo miki abinci.
Cikin gida takoma ta d'ebo abinci ta kawo mata, nan matan taci sosai, tayi godiya ma Allah. Ko da Firdausi ta dawo, tace" ina zaki kuma daga ina kike?.
"Matar tace"ni bakuwace banda kowa na fito garin Yola ne.
Firdausi tana wani isa tana yatsina tace"ok kya iya zama anan kafin mai gidan ya dawo.
Bata jira amsanta ba ta fita a d'akin, Alhaji Hashim bai dawo ba, sai yamma sai da yaci abinci, tukun yana hutawa, Firdausi tace"matar nan fa tana na.
"Oh! Na manta mai ta sanar dake gameda ita, don naga kamar ba'a cikin nutsuwarta take ba.
Firdausi ta mayar masa yanda matar ta fad'a mata.
Yace"kira min ita.

               DEDICATED TO
                AISHA MUH'D
   (MAMAN ABDUL SHAKUR)

              ��RASH LUV✍��

Babban Kuskure 1-15

����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

Bismillahi rahmanu raheem, dukkan godiya, da yabo, tsarki da mulki sun tabbata ga Ubangijin sammai da kassai. Na fara rubuta wannan littafin cikin iko Allah, ya Allah ka bani ikon isar da sak'o mai amfani aciki, san nan ka sanya, mutane zasu, nishad'an tu dashi, ta hanya mai kyau ameen.

Pg-1~5

Wani kyakyawan Matashi, mai jini ajika, sanye yake cikin, kakin sa na Police, kalan blue da bak'in wando.  Kayan sunyi matuk'ar amsan jikinsa, tamkar dashi aka tsara kayan, ko da na kali wannan guy d'in. Dogon ne fari sol, yana da faffad'an k'irji, sannan ga shi da dogon hanci tamkar pencil, yana da k'aramin baki, ga kuma wasu sexy eyes, d'insa da suka rikitani, shekarunsa bazai wuce 37 ba. A hankali yake tafiya, falo ya nufo, dai-dai nan, naji muryan mata tana kiran Indo! Indo! Indo!.
Wacce a ke kira da indo ta fito da sauri, sam bata lura da Yallab'oi ba, tana yankowa sai jin, garam sunyi karo, take jikinta ya d'au rawa ta fara dan Allah kayi... Bata k'arasa ba yasakar mata, wani lafiyayan mari a fiska. Da gudu tayi ciki don tana matuk'ar tsoron Haiydar. Shi ko gogan kar-kad'e inda ta tab'a ya fara, cikin zuciyarshi kuwa, cewa yake"mtss na tsane ki bana son ganinki, don ba yanda na iya ne.
Indo tana shiga, sai da ta share hawayenta,ta k'arasa cikin d'akin, taje ta rusuna agaban wata mata, wanda da'alama itace matar gidan, cikin sanyi muryanta mai dad'in sairaro tace"gani Hajiya".
Wacce aka kira da Hajiya sai wani yatsina take, tace"ga hulan Haiydar nan ki kaimasa, ya fita ni bazan iya tashi ba, cikin tsoro Indo ta bud'i baki tace"Aunty wal....
"Kee yi min shiru umurni na baki, tashi ki kai masa, kina yar aiki, har zanyi magana kema kiyi.
Jikin Indo ba k'wari ta k'arba ta fito falo, dai-dai koma ciki ya d'auko hulan, wani kalo ya watsa mata, take yan hanjin cikinta suka soma rawa, sam bata son had'uwar su, da Haiydar, don ya matuk'ar tsanata, sam baya son ganinta, Indo kuwa ta mak'ure ajikin garu kamar munafuka, duk tayi kalan tausayi. cikin fushi yayi kanta.

 
             DEDICATED TO
               AISHA MUH'D
    (MAMAN ABDUL SHAKUR)

          ��RASH LUV✍��
[5/26/2016]Rash Kardam ����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

Pg-6~10.

Cikin fushi Haiydar yayi kanta, hularsa ya fin cike tare da tofa mata yawu, ya wuce abunsa, cikin zuciyarsa na masa suya, "mtss ace wai matar ka ta sunna, batasan kula da hakkin miji ba.
"Bata damu da duk wani abun da nake bukata ba, wai sai yar aiki.
"Yar aikin ma wanda bata min ba, sam na tsani ganinta mtss. Yayi tsaki, dai-dai lokacin ya shiga motar sa, mai gadi da sauri ya bud'e masa yafita.
Tafe yake cikin nutsuwa har ya isa area Commander, yana shigowa aka fara sara masa, da han zari ya nufi office d'insa dake sama. Yana shiga na biyo sa, nima da sauri don na fara aikina, d'an madai-daicin office ne, d'auke yake da tebur sai kujeran zama, gefe ga k'araman fridge, da nesa na hango yar k'aramar TV bango da ke mak'ale, office d'in yayi dai-dai misali.
File d'in da ke kan tebur ya duba,  nan ya fara yan rubuce-rubuce, nan ya d'aga waya yace"hello Sargent Nasir, kazo ina nemanka a office d'ina yanzu. Wayar ya ajiye ya cigaba da rubutu, ba'a d'au lokaciba wani d'an matashi, ya turo qofar office d'in, yana shigowa ya kame kamar katako tare da buga k'afansa a kasa, hannusa ya sanya shi a gefen damansa tare da waresu. Cikin girmamawa yace" Morning sir".
Naji an kira da sir, bai s'ago kansa ba, yana rubutunsa yace" Morning how is your work?.
Sergent Nasir yace"fine too.
Haiday ya ci gaba da cewa" na duba file d'in case din mutanen nan, kun kaisu CID ne?.
"Eh Sir tun jiya ma aka kaisu.
"Ok daman abun da nake son ji kena.
"Zaka ita tafiya.
Sergent Nasir ya sake sara masa tukunan ya juya ya tafi.
Haiydar ko aikin da ke gabansa yayi, bai fito ba sai lokacin Sallah, k'arfe uku da rabi na yamma, ya kamala duk aikin da zaiyi ya fito ya shiga motarsa ya nufo gida.
Tun a hanya da yayi tunanin abunda zaije ya tarar tsaki ya farayi, duk sai yaji baya son komawa gidan.

               DEDICATED TO
                AISHA MUH'D
    (MAMAN ABDUL SHAKUR)

             ��RASH LUV✍��
[5/26/2016]Rash Kardam ����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

Pg-11~15.

Indo ko tun lokacin da Haiydar ya tofa mata miyau, da gudu tashiga d'akinta, kan gado ta fad'a tasoma rusa kuka kamar ranta zai fita, a fili take cewa"wannan wani irin rayuwa ne?.
"Mai na tsare masa ya tsaneni?.
"Ina da iyayena suna nan nasan duk rashinsu ba ran zauna cikin wanna k'uncin ba.
"Wayyo Ummi na! Allah ya jikanki, tabbas nayi rashi.
"Ina zansan inda dangina suke na nemesu, nasan su bazasu tsaneni ba. A hankali ta tashi ta d'auko wasu fotuna, da wani awarwaro masu kyau, sai d'aukar ido sukeyi, rungumesu tayi tana kuka mai tsuma zuciya, a haka har baci ya d'auketa. Kamar ama mafarki takejin ana kiran sunanta, firgigit tanfarka, aiko taji an sake kiranta, da sauri ta mike ta b'oye war-waronta da hotunanta, ta fito cikin hanzari.
Cikin isa Falmi tace"kee mai kikeyi da baki min aiki na ba?.
"Kin san Darling d'ina ya kusa dawowa.
"Ke harkina da wani saken da zakiyi bacci a gidan nan?.
"Ko kin manta matsayinki na baiwa ne?.
"Mtss na baki nan da 30 minutes ki gyara gidan nan, kuna in kin gama kije ki gyara ma only d'akinsa.
"Zakiga kayan daya ciresu ki wanke su tass, kuma karkisasu a engine kinsan bai cika son wankin....
Sallamansu Xahra da Meesha luv ne yahanata k'arasa magana.
"Oyoyo sis kune haka?.
Cikin sakin fuska sukace"eh mune da mayya.
Falmi tace"ni fushi nake daku ma rabon ku da gidan nan yau kunsan wata 2 fa.
Meesha tace"kawas tuba muke amana hak'uri.
"Sadeey tace" kyaleta kamar ita ta a zuwa mana a kai-akai.
Falmi tace"kudai ku k'araso tukun sannuku da zuwa.
Juyaa tayi ta kali Indo tace"keee mai kikeyi anan har yanzu baki mik'e kinyi aikin gaban ki ba?.
"Ko sai na b'ata miki rai ne?.
Sum-sum Indo ta wuce cikin gida.
Xahrah BB tace"Falmi wacece wannan?.
Cikin ko in kula Falmi tace"house girl d'ina ne.
Meesha tace"kee baki da hankali zaki d'auko wannan zankad'ed'iyar budurwa, wanda duk na miji mai lafiya sai ya yaba da ita.
Sadeey tace"tayani gani fa, amma kinyi gan-ganci.
Falmi tace"kai banza haka zan barta, yanda nake da kishi ae ba zan so wani ya rab'i Haiydar d'ina ba.
"Muna tare daku bari ku ga yanda zasu k'are in yadawo.
"Kuma bana barinta tayi kwaliya.
"Kai gasalima ya tsaneta tsana mai muni.
Xahrah tace"kee baki san wani lokacin tsana yana dawo soyayya ba.
Falmi tace"kee zan bar Haiydar hakane, san a haka ma baya son ganinta.

             DEDICATED TO
              AISHA MUH'D
  (MAMAN ABDUL-SHAKUR)

                ��RASH LUV✍��

Yar Mafiya.. Last page

YAR MAFIYA
Last Page.
Sanah S Matazu
Rash Kardam.
Kwanci tashi Yasiraht da Yasar zamansu masha Allah. Sossai suke kula tare da tarairayar junansu tsaye suke wajan addu'a basa wasa.Yasiraht kuwa ta lazumci nafiloli tare da azumin littinin da alhamis bata sake.

BAYAN SHEKARA GOMA.
Da gudu matashiyar yarinyar ta shigo da takardu a hannunta yar kimanin shekaru tara.

"Yee Mom and (Dad whare are you) kuna ina?"
Ta fada cinyar wata hakimar mace,mai cikar haiba da nutsuwa tana duba wani littafi mai taken Ta'alimul muta'alimi.
Ta shagwabe fuska.
"Kuna ji na kukai mun shiru?".
"Zonan Little Yasmin din Daddynta waya taba ki me kika samu kike murna".

Hajiya Yasirahr ta saki murmushi"kudai kuka sani walahi kaita batamun yarinya da salon shagwabarka".

"Daddy ka ji ta ko?".

"Ke kyaleta itama haka tayi bani labari insha cwt baby na".

"Daddy naci borading school".

Maganar tazo musu tamkar saukar aradu'cikin hargagi ta mike''ba'a gidan nan ba" jikinsa ya yi sanyi Yasiraht ta fashe da kuka''Daddy wai me yasa bata son bording sch ne kullum in nace ina so saita gwale ni?".

"Yi shiru little Yasiraht zata barki maza je ki dakinki ki huta".

Saida ya lallasheta ta yi shiru, sannan ya nufi dakin Yasiraht yana shiga ya sameta tana kuka idonta ya yi jajjir.

Kwantar da kai ya yi a kan kafadarta, ta juyo a hargitse"kana son farin cikin yarka ko? Baka tunanin kuncin da muka fada a baya ko?".

Birkito da ita yayi suka fuskanci juna"kiyarda dani Yasiraht walahi banda nufin kuntatta miki.Babu bawan da ya isa gujewa kaddararsa ita rayuwa mallakar kaddara ce kiyi mata kyakkyawan zato kowa fa da irin kaddararsa a rayuwa".

Ta yi shiru tana jinjina kalamansa, "shikenan na amince amma ta bari sai tayi jss three ta kara wayau da hankali".

"Yauwa Madam".

Sukai dariya gaba daya dai-dai lokacin ta shigo da gudunta,tana murmushi.Hannunta dauke da wani littafi mai kyau da daukar hankali idonta ya ciko da kwalla.

"Mommy a yau na karanta abinda yasa kike kina da makarantar kwana, tabbas Mommy hujojinki ababban dubawa ne kunga rayuwa keda Daddy walahi Mommy na hakura da makarantar kwana insha Allahu zanyi day gani ga ku ga  su granny nafi son kwanciyar hankalinki".

Cikin murmushi ta bude mata hannuwanta da gudu ta karaso ta fada ta maida hannu ta  rungumeta ta runtse ido hawayan farincikin ganin ta maida sunan Yasmin da kuma tuna rayuwarsu ta baya.

"Na tsani bording Yasmin SANADIN BORDING na zamo
YAR MAFIYA tai mun MUGUN DASHE acikin RAYUWATA".

Cikin kuka tace "Mom BAYAN WUYA sai dadi yau gashi da kika riki addu'a ta zamo KATANGAR KARFE a dukkan lamuranki.

NAYI ALKAWARI zan zamo farin ciki cikin rayuwarku Mom,da sanu zan muku BAZATA sai na tabbatar miki RUWA CIKIN COKALI ya isa mai hankali wanka".

Yasar yayi murmushi ya ce,"so please Madam we are free at last".
Ina labe na jawo hannun Rash muka leka bangon littafin ras! Gabanmu  yadi a rubuce radau.
*"MAFIYA A SANADIN BORDING"*

Da gudu mukai baya muna murmushi.

Masha Allah Alhamdulillahi ala kuli halin yau gashi mun kammala wnnn kirkirarre takaitacan labari mai taken YAR MAFIYA.

_KU TSUMAYE A SABON NOVEL 'DIN MU MAI TAKEN SUNA *KISHIYAR TSAKAR GIDA.*_

JINJINA GA MASU BIBBIYAR BOOK DIN YAR MAFIYA.

Aunty Zain
Jamila Kaduna
Bilkisu Muhammad Kano.
Futhatulkuairi sidi be
Mermue
Aisha Muhammad (Maman Abdul shakur)
Kausar lurv
Aisha Mazoji
Meesha lurv
Munay
Khadija Candy
Anesah
Ummieluff
Rabee'atu
Jiddah Aliyu
Queen Miemi
Ummyn Aunty Asiya Malumfashi.
Nafisan Aunty Jamcy Kt.
Zee Mmn Khady
Saeed Bebeji
Teemah Cool.
Autar Hajiya
AshNur
Maijiddah Musa
Fulany Cerdiya
Mrs Zannah
Da duk masu bibiyarsa.Sadaukarwa kacokan gareku.
Bilkisu AmmaniChuchuna.
Ayshat A Sadeeq Chuchungaye hazika mataciyyar labaranmu wato me tacewa. 

MUSHA KARATU YBK GROUP.
NAGARTA WRITER'SU
MATA MASU AJI.

Rash kardam hausa novels 1,2&3

Dandalin lubee mai tafsir

Duniyar littafin hausa
Ladies Novels World.

*TSOKACI*
Littafin yar mafiya kirkira ne dan fadakarwa kan masu sakaci da addu'a a koda yaushe bawa ya tunda tunawa addu'a KATANGA CE dake kare bawa daga dukkan fitunu da rudanin dny. A yau al ummah munyiwa addu'a rikon sakainar kashi wayoyi sunfi komai dauke mana hankali walahi muna sakaci muna cutar da kawunan mu addu a babban makami ce a garemu. ”
_Addu’a tana daga cikin qaddara, kuma sabab ce daga sabubba masu amfani, masu janyo alheri su yaye dukkan sharri. Haqiqa Allah ya yi umarni da addu’a a cinkin ayoyi masu yawa, ya ce,_
( ﻭَﻗَﺎﻝَ ﺭَﺑُّﻜُﻢُ ﺍﺩْﻋُﻮﻧِﻲ_ ﺃَﺳْﺘَﺠِﺐْ ﻟَﻜُﻢْ ﺇِﻥَّ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻳَﺴْﺘَﻜْﺒِﺮُﻭﻥَ
ﻋَﻦْ ﻋِﺒَﺎﺩَﺗِﻲ ﺳَﻴَﺪْﺧُﻠُﻮﻥَ ﺟَﻬَﻨَّﻢَ ﺩَﺍﺧِﺮِﻳﻦَ 60 ‏) ‏[ ﻏﺎﻓر
_Addu’a ta qunshi buqaturuwar bawa da tsananin matsuwarsa zuwa ga Ubangijinsa, wadannan abubuwa ne haqiqanin ma’anar ibada.Ya ku bayin Allah! Haqiqa dimbin nassoshi na hadisan Annabi S A W sun zo game da falalar addu’a.Daga cikinsu akwai abin da Abu Dawud da Tirmizi suka ruwaito daga Nu’uman bn Bashir, Allah ya qara yarda a gare su daga Annabi_

_ya ce: “Addu’a ita ce ibada.” Tirmizi ya ce: hadisi ne kyakkyawa ingantacce.Kuma an karvo daga Abu Hurairah Allah ya qara yarda a gare shi ya ce daga Annabi)._

_ya ce: “Babu wani abu da yafi girma wajen Allah kamar addu’a.” Ahmad da Tirmizi da Ibn Majah da Ibn Hibbana suka rawaito._
_An karbo daga Ubadah dan Samit (R.A) cewa, Manzo(S.A.W) ya ce, “Babu wani musulmi a ban qasa da zai roqi Allah da wata addu’a face ya ba shi ita, ko ya kade masa wani mummunan abu madadinta,matuqar ba ya roqi wani abin laifi ba ko yanke zumunci"._

_Sai wani mutum daga cikin mutanen ya ce: "Ashe za mu yawaita ke nan".Sai ya ce:“Allah Shi ne mafi yawaita wa.” Tirmizi ya rawaito kuma ya inganta shi._

_Ya ku bayi Allah! Ku sani cewa ba a roqon kowa sai Allah, ba wani mala’ika makusanci ga Allah,ko wani Annabi mursali, ko wani waliyyi nagarta cce._

_Kuma duk wanda ya kirayi wani abin halitta ba Allah ba, Annabi ne ko mala’ika, ko waliyyi, ko aljan, ko kabari, ko makamancinsa, to haqiqa ya yi shirka da Allah Ta’ala, cikin ibadarsa, shirka da za ta fitar da shi daga musulunci._

_An karbo daga Ubadah dan Samit (R.A) cewa, Manzo(S.A.W) ya ce, “Babu wani musulmi a ban qasa da zai roqi Allah da wata addu’a face ya ba shi ita, ko ya kade masa wani mummunan abu madadinta,matuqar ba ya roqi wani abin laifi ba ko yanke zumunci"._

_Sai wani mutum daga cikin mutanen ya ce: "Ashe za mu yawaita ke nan".Sai ya ce:“Allah Shi ne mafi yawaita wa.” Tirmizi ya rawaito kuma ya inganta shi._

_Ya ku bayi Allah! Ku sani cewa ba a roqon kowa sai Allah, ba wani mala’ika makusanci ga Allah,ko wani Annabi mursali, ko wani waliyyi nagarta cce._

*ALHAMDULILAH!! MASHAA ALLAH!! KUSKUREN DA MULAYI YA ALLAH KA YAFE MANA.*

MASOYA WANNAN LITTAFI DA BAMU SAMU DAMAN FADAN SUNAYENKU BA MUN GODE DA YAWA.

```KU KASANCE DA MU A LITTAFIN MU NA GABA MAI SUNA``` *KISHIN TSAKAR GIDA.*

BAN GAJI DA GODIYA BA.
Ayshat A Sadeeq Chuchungaye.
Husnah M Inuwa Ummu Samhat ubangiji ya bar zumunci mai dorewa.

*'YAR MAFIYA COMPLETE*

Ku duba����
Sanahsmatazu.mywapblog.com

MUNA MUKU FATAN ALKAIRI
RASH
SANAH KU CE.

Yar Mafiya 46-49

[12:54PM, 1/13/2017] Aunty Wawu: *'YAR MAFIYA*
Sanah S Matazu
Rash Kardam.
*46*
Gaba ɗaya kotun ta ɗauki surutu Alkali ya yi tsawa a kai shiru.Cikin girmamawa Barrister Abdul yai murmushi sannan ya soma magana.

"Ya maigirma mai shari'a ina neman wannan kotun mai adalci ta kwatanta adalcinta wajan yankewa wannan azzalumai hukunci dai-dai da abinda suka aikata".

Ya risina yai godiya,ya zauna kotun ya yi tsit sai shasshekar kukan Yasiraht mai dukkan zuciya.Alkali ya yi rubuce-ubucansa sannan ya ɗago ya soma magana.

"Abisa shaidanu da muka samu,wannan kotu ta wanke wadda ake tuhuma shi kuma Samar da Najwa kotu ta yanke musu hukuncin kisa tare da saka matakan tsaro wajan ƙtsaurara bincike kan lallubo duk wani mai hannu cikin kungiyarsu domin karɓar hukunci.Jabir ma yana cikin waɗanda zasu fuskanci hukunci".

Nan ya buga gudumarsa gaba ɗaya aka mike "kotu".

A hankali kotun ta soma watsewa mahaifinta yazo ya kamota suka fito nan fa yan jarida sukai musu rufdugu amma Yasiraht babu abinda take cewa tana hango yadda Yasar da Najwa suke kuka cike da nadama ta kauda kai tabi bayan Barrister da mahaifinta suka shiga mota har motar ta soma tafiya ta tsaya sakammakon wata tsohuwa da ta bayyana a gefansu tana murmushi Yasiraht ta ganeta sossai cikin murmushi tace.

"Abba Sarauniya ce".
Barrister saida ya tsorata tai murmushi tace"muje zan biyoku gida dan karya sihirin jikin Yasar da Yasiraht da kunje asibiti ku neni sallama".

Bata jira cewarsu ba ta wuce abinda,sunyi jigum sannan Barrister ya yi karfin halin jan motar suka wuce.Suna zuwa abin mamaki Yasar suka samu shida Mama suna kuka  babu ɓata lokaci duka wuce gida.

Hajiya banda neman afuwarta babu abinda take nan Yasar ya dinga basu labarin yadda abubuwa suka dinga tsoratashi Barrister yace.

"Gaskiya sunyi nasara a kanku sossai saboda sakacin kula da addu'a su kuma mahaifanku suna  da raunin kulawa daku.Koda kaddara zata zowa bawa to mudin yana addu'a tana zuwar  masa da sauki.

_Addu’a ta qunshi buqaturuwar bawa da tsananin matsuwarsa zuwa ga Ubangijinsa, wadannan abubuwa ne haqiqanin ma’anar ibada.Ya ku bayin Allah! Haqiqa dimbin nassoshi na hadisan Annabi S A W sun zo game da falalar addu’a.Daga cikinsu akwai abin da Abu Dawud da Tirmizi suka ruwaito daga Nu’uman bn Bashir, Allah ya qara yarda a gare su daga Annabi_ ﷺ

_ya ce: “Addu’a ita ce ibada.” Tirmizi ya ce: hadisi ne kyakkyawa ingantacce.Kuma an karvo daga Abu Hurairah Allah ya qara yarda a gare shi ya ce daga Annabi._

_ya ce: “Babu wani abu da yafi girma wajen Allah kamar addu’a.” Ahmad da Tirmizi da Ibn Majah da Ibn Hibbana suka rawaito"._
[12:54PM, 1/13/2017] Aunty Wawu: *'YAR MAFIYA*

*RASH KARDAM*
*SANAH S MATAZU*

*47*

Sarauniya Samriyana ta umurci da su Yasar suyi wanka sannan suyi alwala su zo. Ruwa ta buk'aci a kawo mata nan nan tasoma addu'o'i ta dad'e tana karanta addu'a tukum ta ajiye a gefe. Yasirah ce ta fara fitowa ta zauna a kasan kafet sai ga Yasar shima. Ruwan maganin ta mik'o ma Yasirah ta ce“kiyi bisimilla kafin ki sha  Yasar ma ta mik'a masa nasa shima ya karb'a. Yasirah tana sha ta fara wani irin juyi tana nishi ta d'au mintuna kafin ta fara aman wani abu baki da shi tare da hayaki yake fita ta hancinta ta dad'e tana aman can sai ga wani abu kamar kitse ya fito na  saraunyi ta ce“Alhamdulilah ta fitar da maitan nan Sarauniya tasaka wani kyalle ta d'auka ta jefa cikin karamin batta sannan tayi kira da wani aljani nan take ya bayyana roban ta bashi ta ce"ka kai wannan tsibirin *Zimlash* ka wurga a kogon da ke kusa da wajan". Aljani da ya bayyana a suffar mutum take ya rusuna ya karb'a ya bace bat kamar bashi.

Abba ya nisa ya ce“da farko nagode Allah sannan nagode da taimako da kika mana Sarauniya Allah ya saka da alkairi".

Sarauniya tayi murmushi ta ce"bakomai yi ma wani yi ma kai ne kuma Alherin da kamun ban manta ba kamin tai mako sai dai mukara gode ma Allah". Nan ta ce"a shiga da Yasira d'aki zatayi bacci mai nauyi in ta garka in Allah ya yarda komai ya dawo dai-dai". Sanann ta mika musu wani goran ruean addu'a ta ce"ga wannan daga ita har Yasar suna shansa ni zan tafi na barku cikin amincin Ubangiji in Allah yaso bayan kwana biyu zan kawo muku ziyara Assalamu'alaikum".

Tana gama fad'in haka bat ta bace.

Abba da Hajiya suka sauke ajiyar zuciya Yasar kuwa jin zuciyarsa yake wasai yana cikin farin ciki kamar anyi refresh d'insa yau.

Abba ne ya taso zai d'auki Yasirah.
Yasar ya mik'e da sauri duk da baya jin k'arfin jikinsa ya ce“Abba bari zan kaita". Ba musu Abba ya barsa ya dauke ta a hannusa kamar 'yar tsana ya shiga d'akinta sai da yayi bisimilla kafin ya kwantar da ita ya zauna a gefenta ya kura mata ido addu'a ya mata ya tofa mata kafin ya manna mata kiss a kumatu ya mike. Yana mai jin farin ciki a zuciyar sa kamar kar yafita a d'akin badan su Abba ai da kwanciya zaiyi kusa da matarsa ya taya ta bacci shima.

A hankali ya sauko daga gadon don karta tashi yazo bakin k'ofa ya kama kofar ya tsaya yana kallonta kafin ya fita zuwa falo.
[12:54PM, 1/13/2017] Aunty Wawu: *'YAR MAFIYA*

*RASH KARDAM*
*SANAH S MATAZU*

*49*
Yau satinsu Yasar ɗaya agidan Abba suna shan magani.

Hajiya ko kara gyara Yasira take yi kulum da abinda zata bata tasha ga mayukan gyaran jiki ta kara haske tayi fresh.

Yasar kulum sai ya haɗiye miyau don yana tsananin buk'atar Yasira.
Yau hajiya sun fitada Abba. Sai Yasirah kaɗai aka barta a gida tana kwance ɗakinta ta lumshe ido tana tunanin irin rayuwanda zasuyi da Yasar wani k'aramin rigane ajikinta sai wando duk ya ɗame mata jiki mik'ewa tayi ta nufi falo don ta ɗauko fresh milk tana taku tamkar masoyinta na k'usa da ita.

Yasar ne zaune a office ya kasa ta ɓuka komai sai tunanin Yasirah yake yi wani sassanyar ajiyar zuciya ya sauk'e ji yake yi ba zai iya hak'uri da ita ba yau.

Cikin sauri ya mik'e ya ɗauko keys ɗin motarsa ya nufi motar yana shiga ya ɗau hanyar gida.

Yasar ya iso ko ajiye motar da kyau bai yi ba ya nufi cikin gida.
Turus ya tsaya abakin k'ofa ganin irin shigan da Yasira tayi, take zuciyarsa ta soma bugawa cikin sauri ya tako yazo inda take. Rungumota yayi ta baya take ya sauk'e akiyar zuciya.
A razane Yasira ta juyo sai taga Yasar ne yana kalon fiskanta. Duk sai taji kunya ya kara rufeta hannusa yasa a gashin kanta yasoma wasa dashi.

Sum dulmiya duniyar masoya ko shigowansu Abba sam basu sani ba. Sai da ya yi gyaran murya da sauri Yasar ya saketa kunya duk ya ishesu.

Kame-kame ya fara yi. Yasirah zata gudu ɗaki Abba ya ce"dawo nan ai yanzou zaku tattara ku barmin gidana daman mun saka agyara can. Maza jeki ɗaki ko ɗauko Hijab ɗinki ku tafi.

A kunya ce ta ɗauko hijab ɗinta Hajiya nafi ta haɗa mata sauran kayanta da wasu haɗim magun-guma. Abba ya musu nasiha sosai ya sanya musu albarka ya ce"zaku iya tafiya". Hajiya ta rik'o hannuta suka raka su mota.

Suna isa taga komai tsab an gyara haka ta nufi ɗakinta.

Daddare Yasar ya shigo sanye da jallabiya nan ya umurceta da tayi alwala. Bayan ta fito daga bayi ta sanya hijab ƳYasar ya jasu sallah. Raka'a biyu sukayi bayan dun idar ya ya mata tabayoyi gameda addini Alhamdulilah ta amsa addu'a ya ringa kwararo musu na samun zuri'a ɗayyiba da zaman lafiya. Yasirah tana amsawa da amin.

Kaza gashashe ya ɗauko ya baje musu a gabansu Yasira duk kunya ya isheta. Shi ya ringa bata abaki harta k'oshi tukun yaci daganan yasoma mata hira yana ɗan wasa da ita.

Sanah tana ganin haka ta ce"Rash zo mu basu guri wannan sirrinsu ne".
"To" Na amsa mata dashi muka fara tafiya har munyi nisa sai na dawo da gudu don ban gaji da kallon wanna lobayyan ba. Dai-dai lokacin dana shigo Yasar ya ke aika ma Yasirah wasu zafafan kisses.

Sana tana juyawa taga bata ganni ba da suri ta dawo ganin na sake baki da hanci ina kallo ta finciko hannuna mukayi waje da sauri.

Washe gari da safe muna dawowa muka ga Yasar sai ƙlallaɓa Yasira yake yi ita ko sai k'ara masa shagwaɓa take yi. Bayi ya kai ta yasa ta aruwan zafi sai da ya mata wanka ya janyo mata k'ofa don tayi wankan tsarki.

Yasirah tana cikin ruwan zafi ta lumshe ido tana tuna abunda ya faru a tsakaninsu jiya,da dadsare ajiyar zuciya ta sauke afili ta ce"alhamdulilah! Allah nagode maka da ka bani ikon kare *BUDURCINA* don shine *'Yancina* duk irin gwagwarmayan rayuwan danayi ban zubar da *MARTABATA BA* da yanzu na sara wannan tarai-rayan da Yasar kake min da yanzu na dawo abar tsana a gunsa Alhamdulilahi ala kulli halin". Ta faɗi tare da sauk'e ajiyar zuciya.

Tana fitowa ta samu ya shimfiɗa mata sallaya sallah tayi. Yasar da kansa yazo yaringa bata abinci da Hajiya ta aiko misu dashi har sai da yaga tak'oshi sannan yaci.

Tun daga wannan rana suka ɗaura soyayansu mai tsafta da burgewa ga kowa. Kowannesu yana kiyaye abunda zai ɓata ma ɗan'uwasa rai.

Rash
Sanah.
[12:54PM, 1/13/2017] Aunty Wawu: *'YAR MAFIYA*

*RASH KARDAM*
*SANAH S MATAZU*

*48*
Ya fita falo ya ga su Abba da Hajiya suma basa nan ɗakinsa ya wuce sai da yayi bismilla kafin ya hau kan gado ya kwanta ido ya lumshe yana mai tunanin sahibarsa bai farka ba sai bayan sallah la'asar yana tashi bayi ya shiga yayi wanka ya ɗaura alwala.

Falo ya fito yaga ba kowa ɗakin Yasirah ya nufa yaga tana bacci gashi duk rigan da ke jikinta ya koma gefe sai santala-santalan cin yarta da ya bayyana a fili. Wani sassayan ajiyar zuciya ya sauk'e a hankali yaje kusa da ita ya gyara mata kwaciyanta tare da rufe mata jiki ya fito ya nufi masallaci.

Yana idar da sallah ya nufo gida ɗakin Yasirah ya shiga nan ya zauna abaki gado ya rik'o hannuta ya sark'e acikin nasa tare da kafe ta da ido ko kyaftawa ba yayi. Cikin zuciyarsa ya ke tunanin abin k'aunarsa ya k'ara gode ma Allah da ya tsamo Yasira daga k'ungiyar mafiya.

Abba da Hajiya suka shigo da sallama sam bai ma san sun shigo ba. Sai da Abba yayi gyaran murya tukun ya farga da su ya sauk'e ajiyar zuciya.

Abba ya ce“Yasar kai ne anan bakaje ka kwanta kai ma ka huta ba"?. Yasar ya sosa kai kunya duk ya kamasa ya sunkuyar da kai yana murmushi. Abba da Hajiya har cikin ransu sunji daɗin yanda Yasar yake nuna ma tilon 'Yarsu ɗaya kulawa. Abba ya ce"Nafisatu tashe ta tayi sallah baza'a kyaleta ba haka".

Yasar ya ce“Abba bacci fa take yi da an barta sai ta tashi".

Abba ya ce“a'a ta daɗe tana bacci fa kusan awa nawa ya kamata ta tashi tayi sallah sai taci abinci. Ina irin sakaci da addu'a ne ya janyo muku haka".
Abba ya nisa yaci gaba da cewa“kasani sallah tana kare mutun daga aikata alfasha da munanan abubuwa. Sallah ita ce aiki na farko da ranan al-qiyama za'a fara aunata a mizani, kaga ko dan me zamuyi wasa da ita dan haka a tasheta".

Hajiya ce ta tashe ta ta shiga bayi ta haɗa mata ruwan wanka. Hannuta ta kamata ta kai ta bayi ta fito Abba na k'ok'arin fita daga ɗakin Hajiya ta kalli Yasar ta ce“kaje ka ɗauko abinci kaci kaima baka ci abinci ba".

Yasar ya ce “to amma sai Yasirah ta fito sai muci tare".

Hajiya Nafi ta murmusa ta fita kawai.

Yasirah ta daɗe a bayi tana gasa jikinta sabida tsamin da ya mata. Tana fitowa taga Yasar na shimfiɗa mata Sallaya. Duk sai taji kunya ya kamata sabida ɗan k'aramin tawul ɗin da ke jikinta.

Da zata koma bayin da sauri Yasar yazo yarik'o hannuta yana mata murmushi dai-dai fiskanta ya karkato ya ce"Baby na miye na jin kunya ko kin manta yanzu kin dawo mallakina".

Kai ta k'ara sunkuyarwa hannuta ya kama ya zaunarta abakin gado ya nufi cikin drower ta ya ɗauko mata dogon riga ya mik'a mata ta ansa amma ta kasa sawa don kunyan da take ji.

Ganin bai da niyar fita ta mik'e tashiga bayi ta saka tazo ta tada k'abbara tayi sallah.

Tana idarwa ya kama hannuta dika nufi falo dining duƙa je nan ya zauna ya rink'a bata abinci a baki har ta k'oshi tukun shima ya ci.

Suna gama ci ya kamo hannuta suka dawo falo ya kunna musu tashar SUNNAH TV *MALAM TIJJANI AHAMAD GURUNTUM* ke gabatar da darasinsa mai taken suna *MAZINACIYA JAKAR GAYU* sunyi shiru duna sauraron wa'azin Abba da Hajiya suka shigo su Yasirah suka sauka k'asa suka zauna tare da yin sannu ma su Abba.

Haka rayuwan su ya siran ya kasance cikin jin daɗi Yasar kulawa na musamma ya ke bata.

Rash
Sanah

Yar Mafiya... 42-45

[12:54PM, 1/13/2017] Aunty Wawu: *'YAR MAFIYA*
Sanah S Matazu
Rash Kardam
*42*

Take tai murmushi tana dubanta amma kafun tai wani yunkurin magan Najwa ta bace bat bata tashi bayyana ba sai a gidansu ita da Yasar.

Cikin tashin hankali ta soma duba gidan, duk yayi kura alamu sun nuna ta dade a hannun Sarauniya kanta ya sara ta dafe tana tsananin takaci ji take kawai Sarauniya ba bakinsu daya da Samar ta fito kenan ta hangi shigosar yan sanda nan da nan ta bace tazama inuwa tana bin bayansu cikin hirar da suke ta fahimci bincike suke kan gawar da suka riska gabanta ya tsananta faduwa ina Yasar kodai shi aka kashe?.

Take ta bude tafin hanunta tana karanta wasu dalamusan tsafi saiga Yasar kwance a kan gadon asibiti.Hankalinta ya tashi zuciyarta tai na'am data bayyana kanta amma tambayar kanta take ta wace hanya.

Dabara ce ta fado mata ta nufi gidansu,saida ta faki idon mutane ta fadi magashiyan dama ga ciwuka  a jikinta ana nan fa aka zagayeta ana ga Yasiraht kwatsam motar mahaifinta ta nufo hanyar da hanzari ya dauketa zuwa asibiti akai emargancy da ita tana jinsu tai lakur tamkar mataciyya.

Yasar dai jiki sai godiyar Allah kasancewar asibitin suna da kwararun likitoci harya soma bude ido amma baya magana baya gane kowa kwakwalwarsa ta tabu.

Ranar da Yasiraht ta cika kwanaki uku ranar yan sanda da yan jarida suka soma yunkurin san ganawa da amaryar da aka sace a daran tarewa sai gawar maigadi da mijinta a galabaice a ka samu amma da ansoma tuntubarta saitasa kuka hakan yasa basu samu ganawa da ita ba suka hakura.

Da dare ta nemi a kaita taga Yasar,dake babu tazara tsakaninsu babu musu aka yi mata jagora suna shiga sukai sa a Yasar ya farka aikuwa yana arba da Yasirahr take kwakwalwarsa ta soma hautsunawa ya dafe kai yana kara a firgice ya furta.

"Ita ce!  Ita ce!! Ita ce!!!".
Take Samar ya bayyana ya buga masa wani katako suka kwala kara shida ita suka zube a nann...

*Shin  Yasar ya mutu ne?.*

*Ina batun Najwa da Jabir?.*

*Yaya batun Sarauniya?.*

*Shin asirin Jabir Najwa Samar da Yasiraht na tonuwa?. Wake yin nasara tsakaninsu?* .

Sanah
Rash.
[12:54PM, 1/13/2017] Aunty Wawu: *'YAR MAFIYA*
Sanah S Matazu
Rash Kardam
*43*
Nan da nan aka dauki Yasiraht akai bangaran emeegancy da ita,shi kuma Yasar likitoci suka dukufa a kansa binciken farko suka tabbatar da cewar kwakwalwarsa ce ta dawo dai dai amma wani abu ya tsoratashi ta sake samun matsala.

Yasiraht tunda ta farka take matsanancin kuka kamar zata shide Hajiya Yasiraht kuwa ko kallonta batai ba domin tayi zargin da hannunta a kwanciyar Yasar.

Tun bayan bacewar Yasiraht Sarauniya take yunkurin zuwa wajanta, amma babu hali saboda hadarurrukan da take riska a hanyarta.Kamar almara Hajiya Nafisa da Yasiraht na zaune saiga shigowar dan sanda da ankwa hannunsa rike da jaridar data tsoratasu.

Baban shafin Jaridar da aka buga a jiya mai dauke da hotan Baba Maigadi kwance cikin jini sai gefe kuma Yasar magashiyan abin mamaki Yasiraht ce a tsaye a kansu hannunta duk jini. A kasa anyi rubutu da manyan baki kamar haka.

*AMARYAR DA TA KASHE MAIGADINTA TA ILLATA MIJINTA YA RASA RUNANINSA A DARAN AURANSU SABODA WANI KUDIRI DA ITA KADAI TASAN HAKAN AN SAMU HOTUNAN DA SHAIDAR HAKAN NE A HANNUN AMINIYARTA......*

Cikin tashin hankali Hajiya Nafisat tasa kuka,suna ji suna gani aka tasa keyar Yasiraht zuwa kotu Najwa ta kyalkyale da dariya tana gefe tana kallo. Kwata kwata yanzu sun raba hanya ita da Samar da Jabir kowa farautar kowa yake yi.

Tunda aka nufi station da Najwa, mahaifinta yake shige da  fice mahaifiyarta kuwa ta rantse babu ruwanta saboda ga zahiri kowa ya gani bata da abinda yafi mika kai bori ya hau da kyar da sidin goshi ya samu barrister Kurfi ya tsaya musu a shari ar saidai zuwansa uku Yasiraht ta kasa magana sai kuka take karshema tace ya nemamata afuwar mahaifanta ita tasan kasheta za'ayi hankalin mahaifonta yai tsananin tashi duk ya rame addu a ce kawai rake rike da shi ga jikin Yasar rai a hannun Allah.

Ranar Littinin itace aka tsayar ranar shiga kotu, kotun makil take da jama'a babu masaka tsinke nan aka taso keyar Yasiraht tana zubda hawaye nan lauyan gwamnati ya tashi ya gabatar da kansa.

"Sunana Barrister Husssin Abubakar Muhammad, wanda aka fi sani da Brr. HAM ni nake wakiltar gwamnati".

Cikin shigar kamala ya fito yana murmushi, ya shafi kasumarsa zuwa gashin bakinsa.Rash ta taboni "Sanahty wannan gayan fa?" na doke hannunta na sha kunu. "Madam muyi abinda yake gabanmu cikin hanzari ta saisaita kanta nai mata gwalo nace"namiki miji kwalellanki mijin Jiddona ne.Hankalinmu ya koma kansa.

"Sunana Barrister Abdurraham Sulaiman Kurfi, ni ne lauyan dake kare wadda ake kara".

Cikin takunsa mai gamsarwa ya koma ya zauna, nan Brr Ham ya fito yana cin magani.

"Malama Yasiraht ko zan iya sanin dalilin daya sa kika kashe maigadinki da mijinki a daran auranki?".

"Objection ya mai shari a Brr yana neman yiwa wanda ake kara tambaya,mai cike da tozartawa".

"Korafi bai karbu ba".

A sanyaye ya zauna, Brr, Ham yai murmushin mugunta yana duban Yasiraht.

Tana dago kai suka hada ido da Najwa ta nai mata murmushin mugunta a zuciyarta tace "kinyi nasara" a fili ta ce.

"Bani da amsar da zan baka saidai in ce nina kashe shi nima ku kashe ni.. ..".

Kuka yaci karfinta ta kifa kai rana shassheka,mahaifinta ya dinga share kwallar tausayi kamar zaije ya janyota.

Dai dai lokacin Samar na can yana yunkurin zuwa hallatar kotun Jabir ya daureshi tamau habu halin fitowa a tsuburin mula'ali.

Da sauri Barritar Abdul ya mike yace, " ina neman wannan kotu ta daga karar nan har sai an binciki kwakwalwar wadda ake tuhuma"

MUJE ZUWA
[12:54PM, 1/13/2017] Aunty Wawu: *'YAR MAFIYA*
Sanah S Matazu
Rash Kardam
*44*
Haka kotun ta tashi babu wata gamsashiyar amsa, a ranar aka wuce da ita firsin dan jiran hukunci.

Jikin Yasar ya soma sauki an yi sa'ar yi masa aiki kwakwalwarsa ta dawo dai-dai tunda ya farka yaki magana da kowa cikinsu sai bi da ido yanajin yadda suke hira suna aibata Yasirsht mahaifintane kadai baya jin bakinsa.

Sarauniya ta cigaba da bibiyar lamarin Samar da Najwa cikin ikon Allah duk ta karya tsafin da suke takama dashi ta kamasu ta daure.Samar bai mata wuyar kamu ba saboda yana daure a tsuburin muli'ali.

Duk yunkurin Brr nasan ganawa da Yasiraht taki bashi fuska, hasalima in yazo bata sauraransa.Yasiraht ta kade ta rame, tayi baki sossai burinta kawai a yanke mata hukunci ta mutu ta huta.

KOTU ZAMA NA BIYU...........

Kamar yadda aka saba kowane Brr ya mike ya gabatar da sunansa sanan Brr Ham ya soma gabatar da binciken likitoci.

"Ya mai girma mai shari a,binciken likitoci ya tabbatar da cewar Yasiraht lafiyayya ce bata da matsala kota ciwon kai bale tabin hankali.Wannan ya bada tabbacin kisan da tai da nakasa mai gidanta da gangan ta aikata hakan.Ina rokon wannan kotu mai adalci ta gaggauta hukunta wannan azzalumar dan fitarwa da iyalan marigayi hakkinsu".

Cikin girmammawa ya ajiye sakammakon likitocin ya risina yai godiya ya zauna.

"Lauyan wanda ake kara ko kana da magana?".

"Eh ya maigirma mai shari a".

Kamar an keho su suka shigo kotun hakan yasa Brr dakatawa gaba daya kallo ya koma sama.

Samar ne da Najwa cikin galabaitacan yanayi,bayansu Jabir ne yana huci.

"Afuwan ya mai girima mai shari a mun katse muku hanzari amma hakan yana da muhimmanci saboda wadaanan Azzaluman sune silar komai".

Nan take kotun ta hautsine kowa da abinda yake fada, Alkali ya buga abin dakatawa kowa yai shiru.Sannan ya bawa Brr damar magana da Jabir cikin nutsuwa ya dubeshi".

"Malam munasan sanin sunanka da dalilinka da kawo wadsnan bayin Allah kan cewa sune tushan wannan matsala".

Murmushi Jabir ya yi yana dubansa.

"Cikakken sunana Jabir Adama Saulawa,ni haifafan garin Katsina ne sana ata shi ne kasuwanci bani da iyali.Kamar yadda kasani na gaya muku cewa wadanan mutane su ne tushan wannan fitina eh hakane amma zanfi so kuji daga bakinsu".

Barrister ya juya kan Najwa yana dubanta.

"Mallama ya sunanki?".

"Sunana Najwa".
"Shin menene alakarki da wannan shari'a?".

Kai ta sunkuyar kasa tana share hawaye a hankali ta bude baki ta soma bayani.
"Tabbas nayi nadamar cutar da Najwa... ....." tiryan-tiryan ta dinga bayanin tun daga alakarta da Samar da yadda suka ja Yasiraht har zuwa yau.Kotun tayi tsit sai shashekar kukansu da take tashi,kowa na Allah wadai da Najwa da Samar masu tsinuwa nayi masu kuka nayi.

Bsrrister ya dubi"Samar zancan da Najwa ta fada gaskiya ne?".

"Gaskiya ne Barrister".
"Samar mecece hujjarka ta cutar da karamar yarinya kamar Yasiraht?".Yai shiru na tsayin lokaci sannan ya  soma magana.
[12:54PM, 1/13/2017] Aunty Wawu: *'YAR MAFIYA*
Sanah S Matazu
Rash Kardam
*45*

"Gaskiyar magana tun ranar da naga Yasiraht na tuna da burina da nake son cikawa wato zama babban matsafi wanda zai dinga jagorantar Matasan jahar da nake ciki.Sai dai an bani tabbacin bazan samu ba saina kawo matashiyar budurwa mai kimanin shekaru ashirin da daya wadda ranar data cika shekarun za ayi aikin.Tunda aka lissafun yanayin budurwar nake fafutukar nema kwatsam nai gamo da Yasiraht saidai kash shekarunta basu kai ba hakan yasa nasamu nasarar dasawa Najwa son ta jawo mana ita tare da yimata alkawarin hawa kujerar Sarauta.Lokacin da Najwa ta kawo Yasiraht sai nabata sarauta dan san karfafa kusancina da ita hakan ya tunzurata ta soma nunawa Yasirahr tsana da hantara tun bata fahimta ba harta fahimta suka soma takun saka sai dai bata nasara kanta nasararta daya kashe Yasmine da tayi.Sai kuma wannan sharin da taiwa Yasiraht.

A duniya babu abinda na tsana irin ganin Yasiraht da wani namiji hakan yasa na dasa mata tsanar kowa saboda an bani tabbacin mudin nai sakaci ta soma soyayya to aikina zai wargaje Marwan shine saurayin dana fara kashewa sannan na dasa mata bakin jinin dana saurayin da yake kulata.

Daganan ya dora bayanin kaf abinda ya faru bayan shigowarta kungiya har zuwa kashe me gadi da kwanciyar Yasar asibiti.

Ya cigaba...Najwa ita ta hada tsafin da ta hada hotan Yasiraht da gawar maigadi ta taka takaiwa jamian tsaro ba tare da sun gane ita bace tai bada kama ta basu report na komai sai dai sun tsareta a cell dansan tsananta bincike amma da suka dawo babu ita hakan yasa sukaita nemanta amma ko me kamarta basu samu ba tilas suka tattara hotuna da rahotanni zuwa ga yan jarida nan da nan aka shiga yadidi da hotuna har aka kama Yasiraht.Kama Yasiraht ya fusata Sarauniya sossai".

"Wace ce hakan Malam Samar? ".

Lokacin da mukai nasarar shigar da Yasiraht cikinmu bisa sakaci da take da yin addu'a sai Sarainiya ta dinga bibbiyar rayuwarta.Sarauniya wata jinsi ce cikin jinsin aljanu amma musulmace ita take taimawa Yasiraht wasu lokutan tana bibbiyar Yasiraht ne saboda taimakon da mahaifinta ya yi mata a wasu shekaru........ nan ya bada labarin alakar mahaifin Yasiraht da Sarauniya har zuwa dauketa da tayi da godowar da tayi  sanan ya cigaba.

"Wannan ya fusata ta ta dinga bibiyar lamuranmu, fahimtar hakan yasa muka dinga wasa da hankalinta nida Najwa wajan tare mata hanya harta samu kaucewa da taimakon Jabir ta kamamu ta karya duk wani shiri namu harta samu nasarar kawo mu wannan waje".

Yar Mafiya 39-41

�� *'YAR MAFIYA*��

Sanah S Matazu
Rash Kardam
*39 to 41*

Kwanci tashi tsayin watanni ana neman Yasiraht amma babu ita labarinta.Jikin Yasar dai gashi nan yau fari gobe tsuma.
A haka aka samu numfashinsa ya dawo, saidai liitoci sun bada tabbaci zai iya rasa tunaninsa gaba daya.

Yasiraht na cigaba da samun kulawa wajan Sarauniya sossai, saidai  bata da karfin da zatai tafiya saboda jigatuwar da jikinta ya yi lokacin da Najwa taso hallakata.A hankalin ta soma takawa tana fita baki dajin tana kallon namun daji tare da taya Sarauniya farautar namun daji zuwa cikin dajin.

Kamar koda yaushe yauma tafe suke suna hira Yasiraht ta dubeta.
"Sarauniyya naji sauki ina son in koma gida saboda sanin halin da Yasar yake amma bakimun bayani wace ke ba".

"Cikin murmushi tace zakisan wacece ni bada jimawa ba,amma menene alakarki da wanda suke bibbiyar rayuwarki?".

Yasiraht ta sunkuyar da kai idonta ya ciko da hawaye tasa hannu ta share ta cigaba.

"Kawai tasowa nayi na tsinci kaina a cikin wannan harka amma kafin mutuwar Emeka ta bani labari cewa:

Asalin kungiyarmu ta mahaifin Samar ce,haifaffan garin Kano ne mahaifinsa Malam Sammani da me dakinsa Saudatu. Mahaifinsa mutum ne mai kwadayi da san tara dukiya tun yana saurayi harya girma iyayansa talakawa ne sossai suna zaune unguwar Yalwa a cikin Kano.Fahimtar hakan yasa suke yi masa nasiha sossai, amma baya ji idan yaga masu kudi baya tunanin tayaya suka samu dukiyar kawai burinsa Allah ya bani itaku ko kuma ya dinga biy-biyarsu yana su bashi aikin yi shima yayi kudin hakan yana batawa mahaifansa rai sossai.Lokacin da yai auran fari kwatsam yana matakin karatu s college kasancewar duk da rashin mahaifinsa ya tsaya masa matuka kan karatu suna level one ya soma samun matsala a jarrabawarsa hakan yasa ya shiga damuwa sabida ya dogara da karatunsa sossai  kwatsam ya samu kansa an masa tallar kungiyar kan cewar in dai ya shiga bashi ba faduwa a jarrabawa ga kuma kudi da zai dinga samu mudin zai bi dokoki bai jimaba ya amshi batun hannu biy-biyu lokacin bai yi auran fari ba sai da ya shiga aka soma jero masa dokokin kungiya babu fita in an shiga kuma duk wanda ya tona musu asiri kashe shi zasui.

Hajara itace diyar kanin mahaifinsa da ya mutu ya bashi a gidansu ta tashi itace yake matukar so, farkon shigarsa aka bashi kudi naira dubu dari biyar ganin kudin ya daga hankalinsa bai taba kama irinsu ba nan ya boye dubu dari uku ya nufi gida da dubu dari biyu nan ya zauna ya shiryawa mahaifansa karya kan cewar mahaifin abokinsane ya bashi aiki kafin ya gama makaranta suna yi masa aikin company wannan kudi an basu ne  dan farkon daukane duk wata za a dinga basu dubu hamsin mahaifansa sunji dadi sossai har gida suka taka gidan daya daga manyan kungiyarsu a zuwan mahaifin abokinsa ne tafi-tafi watanni naja ya soma shirin auran Hajara watansu biyar da aure ta samu juna biyu nan dodon tsafi ya nemi jininta shi kuma yace atabau bazai bayar ba nan suka nemi jinin mahaifansa mahaifinrsa ya fara badawa kawai sai wayar gari akai aka ganshi a mace.Bayan wata uku da mutuwarsa Hajara ta haifi kyakkyawan yaronta namiji yaci sunan kakansa ake kiransa Samar.

Kwanci tashi Samar na girma kyakkyawa dashi, sun shaku da mahaifiyarsa da kakarsa mahaifin Samar kullum cikin bibiyar shuganinsa yake harya gama sanin makamar aiki kaf kwatsam aka nemi jinin mahaifiyar Samar a lokacin yai musu tawaye da hadin bakin wasu cikin manyan abokansa kaf suka kakkashe manyan ya maye kujerar shugabanci wanda saida ya bada jinin mahaifiyarsa sannan ya hau a cewarsu dalilin da yasa suke bukatar jinin mahaifa saboda mutum bashi da wanda yafisu mudin  ya bada su to zai iya bayar da kowa tun Samar na shekara goma mahaifinsa yake koya masa zafi ya kware sossai sannan ya sashi makaranta ta hanyarsa suke samun shan jinin yara kanana tare da kswosu cikin kungiya. Samar na aji shida na firamari suka hadu da Najwa lokacin tana aji hudu shakuwarsu ta samo asaline daliin lesson na maths da yake musu  tsakanin gidajansu gida kusan goma ne ya rabasu. Shakuwarsu tayi tsanani sossai a haka ya gama primary ya faɗa secondary ita ƙkuma tana aji biyar yana jss two akai masa jumping ya tafi aji biyar yazana jarrabawa ya shiga aji shida lokacin ta tafi form one yana aji shida ta shiga form two tana aji uku ya gama secondary mahaifinsa ya nema masa gurbin karatu a Cairo.

Lokacin da zai tafi tasha kuka sossai.Asalin mahaifan Najwa haifafun garin Jos platue ne Hajiya Moma da Najwa ke kira da Moma itace ta haifi mahaifinta tare da mijinta wanda ya jima da rssuwa.Alhaji Shazali shida yayansa Shamsudeen Shamsu deen ya rasu ya bar Shazali hakan yasa Moma ta dauki so ta dorawa Shazali lokacin da ya kammala karatunsa yai aure ya auri abokiyar karatunsa Maryam mace mai nutsuwa da hankali shekararsu daya da aure aiki ya dawo dashi Kano yaso tahowa da Moma taki amincewa haka suka rabu suna kewar juna.

Zamansu a Kano zamane me daɗi da kwanciyar hankali shekararsu ɗaya suka haifi yara biyu kyawawa Najwa da yayanta Nura wanda suke kira Nur sun taso cikin so da kulawar iyaye uwa uba Kakarsu duk hutu wajanta suke yi cike da so da kulawa bayan Najwa da Nur akwai Fadil da Fadila daga su iyayansu basu sake haihuwa ba.

Lokacin da Samar yazo hutun farko sai mamaki ya ƙkamashi ganin yadda Najwa ta koma katuwa da ita yana ziyartar gidansu akai akai kowa ya sanshi wani zuwa da Samar ya yi gidansu Najwa suna hira take bashi labarin tana son bording schl ba ƙkaramin daɗi ya jiba amma bai nuna mata a ransa yana ayyana wannan lokacine ya dace ya jawo Najwa kungiya yadda zasu ji ɗaɗin samun mata matasa cikin tafiyar.Samar babu abinda ƴya fasa na zafi daya je karatu saima gaba saboda ya  damu waɗanda suka fishi gogewa kan harkar.Washegari ya zowa Najwa da tsafataciyar alawarsa ya bada babu jinkiri ta shanye a barta tun daga lokacin ta soma bibbiyar Samar sau da kafa kuma komai ya bukata babu jimawa take masa a haka yasa ta bashi jinin Fadil da Fadila kawai sai tsintar gawar yaran a kai a ruwan wankan su na boys quaters mutuwarsu ta girgiza kowa sossai bayan rasuwarsu aka kai Najwa makaranta nan ta soma jawowa kungiya member hakan yasa matsayinta ya girmama a cikinsu suna jss three ta bada jinin mahaifanta biyu saboda san samun kujerar Sarauta ta tsafi karshe ta faɗi bata cimma nasara ba.

Hakan ya yi matuka bata mata rai ta hakura Samar ya haye karagarta kwatsam Samar ya kawowa Najwa ziyara makaranta anan ya gani tun daga lokacin ya ke nunawa Najwa ta jawoni cikin kungiyarsu hakan zaisa ta zamo Sarauniya idon Najwa ya rufe kwata kwata mulki take so da wannan damar Samar yasata kawoni cikinsu ta hanyar yaudarata ta bani alawa kwatsam na riski kaina a cikinsu.Bangare daya kuma Samar soyayyata ce tai kaka gida a cikin zuciyarsa zuwana cikinsu yafi komai kwantar masa da hankali sai lokacin Najwa ta fuskanta zuciyarta tai zafi saboda tana burin ace itace matarsa kodan ta hau kujerar mulkinsa wnnan yasa ta soma bin wasu matsafa a boye harta kai ga bada jini Nur ya zamo bata da kowa sai Moma hakan yasa ko hutu akai to Jos take tafiya tarkacan tsafinta kuwa na gidansu na Kano fahimtar tsangwamar da Najwa take mun yasa Emeka ta soma taimakamun ta hanyar wani boka dake. garinsu a Ebira cikin dare take tashina mu tafi farkon shigata kungiya naso fita amma suka bani tabbacin mudun na fita zasu kashe mahaifana nikuma du duniya nafisan mahaifana fiye da kowa tsoron hakan yasa naki fita daga cikinsu abinda ya batamun rai na fitinin kowa cikinsu kuwa mutuwar Yasmen hakan yasa na soma yi musu barna nasoma daukar fansa akan Najwa wanda hakan ya haifar mana da gaggarumar gaba uwa uwa tsananin kishin juna. Gagarumar gaba ta cigaba da gudana tsakaninmu sai dai basa nasara a kaina saboda taimakon da Emeke kemun har sukai nasarar kawar da ita bayan ta mallakamun zoban kakanta ta sihiri ni kuma na hallaka Shanny daga nan muketa cudawa har zuwa lokacin aurena".

Murmushi Sarauniyya ta yi tace "kema ba sonki yake ba bibiyarki yake dan cikar burinsa kuma yana daf da cika Allah ya kawo Emeka kika fitinesu kuma ba wata bace Emeka nice Emeka nake bada kama ina bibboyarki duk wani wajan tsafi da kike ganin muna zuwa kawai rufa ido nake miki sabida banaso kisan kudirina a kanki cikin razana Yasiraht ta soma ja da baya tana nunata da yatsa.... wace ce ke?

ku biyomu

Yar Mafiya 36-38

[12:54PM, 1/13/2017] Aunty Wawu: �� *'YAR MAFIYA....*��

*Rash Kardam*
        *Sanah S Matazu*
*N. W. A*
Page
*36*
Jabir da Najwa sai keta tsaunuka sukeyi sai da suka isa wani kogon dutsi suka tsaya yada-zango don su huta a gun. Najwa da ta gama galabaita ga tabo a jikinta cikin murya gajiya da wahala ta ce“Jabir nagode da ceto na da kayi nasu damar da zan k'arasa d'aukar fansa na".

Murmushi Jabir yayi ya ce“karki damu na tai maka miki ne don nima ina da wani kuduri akan Samar ina so mu had'a hannu da k'arfe muga bayansa kamar yanda yasaka muka kawo iyayen mu da masoyan mu".

Najwa tayi murmushi ta ce“ni kuma ina matuk'ar k'aunan samar bazan iya cutar da shi ba sai dai fansa na akan Yasirah ne ita zanga bayanta".

Jabir ya numfasa yana nazarin kalaman Najwa amma sam bai ji zai fasa abunda yayi niya ba.

A can dajin *KARAMGATURA* cikin gidan Sarauniyan Aljanu *Samriyana* tana ta kula da Yasirah wanda tsafin yasoma tasiri a jikinta. Duk jinyan da take mata a banza ne wana hakan yasa tafara tunani taya zata tai maki wannan yarinya don bazata tab'a mantawa da alherin da mahaifin Yasirah ya mata ba shiyasa a ko da yaushe ta ke bibiyarsa tana tunanin ta inda da zata rama wannan alherin don *Alkairi danko ne*  baya tab'a fad'uwa kasa banza haka.

Ajiyar zuciya ta sauke ta lumshe idonta tare da gyara dogon gashin da ya sauka  har kusa da gwiwar k'afanta tana kara nazarin rayuwanta.

*WACECE WANNAN SARAUNIYA SAMRIYANA?.....*

*MAI NENE ALAK'ARTA DA BABAN YASIRAH WATO S MARAFA?....*

```Don jin wa'yan nan amsoshi ku kasance da.```

Rash
Sanah ku ce.
[12:54PM, 1/13/2017] Aunty Wawu: �� *'YAR MAFIYA....*��

*Rash Kardam*
        *Sanah S Matazu*
*N. W. A*
Page
*37*
Sarauniya Samriyana ta kasance 'Ya d'aya tilo ga Sarki Sarguna sarkin aljanu na k'arni goma da ya wuce, ya kasance Sarki ne mai kwatanta adalci a tsakanin mutanen garinsa *KARAMGATURA.* Suna jin dad'i mulkinsa kuma suna masa biyayya da kyautata masa a matsayinsa na shugaba. 'Yar sa d'aya tilo ita ce *Samriyana* yarinyn da ta gado halin mahaifinta ga son tai makon jama'a.

*Samriyana* ta kasance mai son zaga duniya taga mai ke gudana wata rana ta fito ita kad'ai ba tare da hadimanta ba ta iso k'asar Nigeria sai da ta zagata har ta iso garin Bauchi, tayi kwanaki a garin tana zagawa sabida yanayin garin ya burgeta hakan yasa tayi kwanaki a cikinta tana yawo.

Wata rana cikin irin yawon da takeyi a garin Bauchi ta bullo ta wani unguwa, da alaman unguwan na masu hali ne gashi ta galabaita da yawa don yunwa ta keji ga kishin ruwa.

Taje gida yafi nawa  a rin yanayin da tarikid'a takoma kamar mai bara sai su wulakanta ta su kure ta a haka har tazo bakin titi ta zauna ta zuba tagumi sai hamma take yi. Sani Marafa ne ya fito daga makaranta tun kafin yayi aure yana matashi lokacin ma a makarantar gaba da primary yake. Ya hangi wata mata cikin yanayin tausayaa da har zai wuce sai yaga tana hawaye tana magana a hankali bai jin mai take fad'a, cikin tausayawa ya matso kus da ita ya ce“bai war Allah lafiya kike zaune anan?". cikin yanayin wahala ta ce“ka tai maka min da ruwa yunwa nake ji". Cikin hanzari ya juya yaga gurin da suke da gidansu akwai tazara gashi bai da kud'i sai naira d'ari. Hakan yasa ya ce“bai Allah kiyi hakuri naira d'arine ya rage a jikina amma barin sayo miki ruwa da bredi kinji".

Da sauri ya nufi wani shagon da ke nesa da gun ya sayo mata bredi da ruwa ya kawo mata ya bata hakuri.

Sanah
Rash
[12:54PM, 1/13/2017] Aunty Wawu: �� *'YAR MAFIYA....*��

*Rash Kardam*
        *Sanah S Matazu*
*N. W. A*
Page
*38*
Da sauri ta karba tana ci kamar mahaukaciya duk sai ta bashi tausayi sai da ta gama ci ya mata sallama ya ce“ni zan tafi gida gashi bani da wani abu da zan tai maka miki amma kiyi hakuri". Ya mike ya fara tafiya.

*Samriyana* sai da taga yagi nisa ta mike ta bace ta na binsa ba tare da ya sani ba.

S Marafa yana isa gida ya gai da Mamansa aka kawo masa abinci sai da yayi wanka ya sanya kaya ya d'auko kularsa zai ci abinci sai ya bud'e yaga girkin Mashaa Allah yayi sai kamshi ke tashi, yazo zai saka hannu sai ya tuna da matar d'azu a fili ya ce“ni yanzu gani zanci abinci mai kyau yayi da wasu ke nima kuma ina ci zan ban saura don haka barin raba biyu inci rabi in kai wa matar nan rabi Allah zai ban ladan tai mako". Murfin kulan ya jawo ya raba ya diba nasa yasa a murfi ya ci tukun ya mike ya nufi cikin gida.

*Samriyana* da ta biyosa duk abunda yake fad'a taji ta gani hakan yasa ta bace ta koma inda ya barta tana mamakin asai yanzu ana samun masu tausayi irin Sani.

Sani yana shiga gida friza ya bud'e ya dauko juice gora daya da goran ruwa ya fito ya d'auki kulan ya nufi inda ya bar matan.

Yana zuwa ya sameta a inda ya barta nan ya mika mata kulan sai da tayi godiya ta karba taci nan ya mata sallama ya koma gida.

Yana tafiya ta bace ta dau hanyan garinsu tana mai farin ciki ko da ta koma sai da ta sanar da mahaifinta abunda ya faru ya ji dadi ya ce“ina so daga yau kina bibiyansa da hadimanki duk wani abun tai mako in ya taso masa kina masa in har baifi karfinki ba.

Sani Marafa washe gari da ya dawo bai sake ganin matan ba tun yana bibiyan gun har ya hakura haka kurum ya tsinci kansa da son tai maka mata don yana mata kalon ta haifeshi ko tayi jika da shi.

To kunji wannan shine dalilin da yasa Samriyana ta tai maki Yasirah wanda da badun Allah ya kawota a wannan lokacin ba da an shude tarihin Yasirah.

Rash
Sanah

Popular Posts

 
]]>All content on thisblog are copyright protected and cannot be reproduced on other websites without permission.