*'YAR MAFIYA*
*24*
Cikin tsananin tashin hankali yai baya, kansa ya soma juyawa wani abu ya daki kirjinsa.Ya zube kan gado Allah ya bashi sa'a ya soma jan addu'o'i duk wada tazo bakinsa.
Take dakin ya daina girgiza, komai ya koma mazauninsa har abincin tamkar komai bai faruba.Ya yi jim yana tunanin lamarin ture abincin yai ya mike ya dauki mukulin motarsa kai tsaye ya wuce wajan park ya dauki motarsa kirar corrola.Gidansu Nawas abokinsa ya nufa sai dai bisa akasi baya nan haka ya dawo gida jiki a sanyayye.
Kwanci tashi maganar biki kara kusantowa take, babu wani jituwa tsakaninsu sai kallon banza da bakakken maganganu in kuwa suka hadu a gaban iyayyansu nunawa suke tamkar babu komai tsakaninsu a haka aketa cudawa.
Yasiraht da Samar hankalinsu yayi mummunan tashi, musamman yadda duk yadda Samar da Najwa sukai kokarin runkarar mahaifan Yasiraht basa nasara saboda karfin addu'a.Har lamarin ya soma taba tsafinsu wanda yake kawo musu koma baya,hankulansu yai matukar tashi sossai.
Yasar ne zaune a office haka kawai yaga office din na girgiza, take kasa ta dare wasu irin hallitu masu kahunhuna suka bayyana suna kawo masa cafka.Ya rintse ido yana ta'awizi wani mashi kakkaifa ya ratso tsakani ya nufoshi gadan-gadan.Take ya runtse yana jiran me aukuwa ta auku jin shiru na lokaci yasa ya bude ido abin mamaki mashin ya gani tsaye dai-dai kirjinsa yana daga ido yaga Yasiraht ce tsaye tana masifa ta tsayar da mashin da karfin tsafinta. Ta ware ta fin hannuta wani haske da abu kamar walkiya suka tsaya a tsakanin hannayenta abun kalan ruwan gaye-gaye da fari-fari abun gwanin tsoro sai ya saje da kalan kayan jikinta ruwan ganye.
"Shima kasheshi zaki yi Najwa?"
"Tabbas Yasiraht walahi sai na illata rayuwarki,ninai sanadin zuwanki kungiya yau gashi kin fini komai".
"Kinyi kuskure Najwa na shirya ja dakowa cikinku, ciki hada daukar rayukan masu neman bibbiyar lamurana".
Take suka soma gumurzun tashin hankali, wanda hakan yaja farfashewar wasu cikin kayan.Can Najwa ta saki kara sakammakon nasarar sokarta da tai da mashin hannunta a gefan kafad'a b'acewa tai tana kuka.
Yasar ya saki ajiyar zuciya, Yasiraht ta gyara office din tas ta dago tana dubansa tai masa murmushi tace.
"Kana musulmi kana sakaci da addu'a ko Yah Yasar?".
Bata tanka ba ta wuce ta rufemasa office din, ya cigaba da jujjuya maganarta a ransa.Shigowar Nawas ya katsemasa tunani, yace "Ango! Ango!! Ango!!! Dariya kawai yai suka soma hira.
Sun jima suna hira yai masa sallama ya wuce, haka Yasar ya yini sukuku dashi.
Rash
Sanah
0 comments:
Post a Comment