New Post

Friday, 7 July 2017

Yar Mafiya... 23

�� *'YAR MAFIYA....*��

*Rash Kardam*
        *Sanah S Matazu*
*N. W. A*
Page
*23*
Yasar an sallame shi a Asibiti tare da garg'ad'in ya kiyaye shan magani da kuma abunda zai janyo makansa mumunan buguwa don zai shafi kwanyansa. Ko da suka dawo gida Ammar shi ya ci gaba da kula dashi har ya warke sosai.

Samar ne ya shigo da motar sa haraban gidan su Yasirah mai gadi ya gai dashi Samar ya amsa cikin sakin fuska mai gadi ya ce“barin kira maka Hajiyar". Mai gadi ya shiga gida ya tarar da Yasira tana shirin fitowa haraban gidan daman ta san da zuwan Samar, mai gadi shi ya sanar mata da sak'on Samar ta ce" gata nan zuwa k'irjinta sai bugawa yake yi don ta san Samar ba zaiyi sassauci akan maganan ba.

Tunda ta fito Samar ya kafeta da ido sai jin zuciyarsa na harba masa da sauri-da-sauri kasa d'auke idonsa yayi daga gareta, tana isowa ta ce"King barka da yamma". Cikin sanyin jiki ya amsa“lafiya ya kk?". Yasirah ta rausaya ta ce“lafiyalau". Shiru gurin yayi sai Samar da yayi dauriya da d'ago ya kalleta cikin so da k'auana. Yasirah ta ce“Samar nayi duk yanda zanyi Abba yaki afasa aure ya ce aure dole ba fashi".

"Yasirah gaskiya da sakel"cewar Samar dake zaune kan mota fuskarsa babu alamun walwala. Tayi ajiyar zuciya tana dubansa ranta duk a cakud'e hawaye tag ya ciko idonta tasa hannu ta share. "Samar bansan ya zamu yi ba, Abba ya dage kan lamarin sossai.Gashi shugaba kullum cikin gargad'ina take bisa kaucewa dokar k'ungiya".Ta k'arasa maganar cikin raunin murya.

Cikin kaushin murya yace"zanyi hukunci"cikin sauri ta tari hanzarinsa "nasan hukincinka bahagone Samar karkayi pls na rokeka."Bai jira cewarta ba ya kwashi mota da tsananin gudu yabar harabar gidan. Durkushewa tayi  take yanayin halitarta ya soma sauyawa daga yadda take zuwa wata suffar da gudu ta tashi ta shiga cikin gida d'akinta tashiga tasaka ma makulli ta kulle kanta..........

Yasar jiki ya warke kwance ya ke yana tunanin irin had'in da Abba ke shirin yi masa da wannan azzaluman don shi ba wai sonta bane ba yayi a'a sai abunda take aikatawa gashi yakasa sanar da kowa ko yayi yun k'urin hakan bakinsa nauyi keyi ya kasa fad'a. Da wanna tunani aka kira sallah ya fita ya tafi masallaci bai dawo ba sai da yayi sallah isha'i yana zuwa ya samu an kawo masa abinci dining ya je ya zauna ya bud'e kular sai ya manta bai d'auko ruwa ba mik'ewa ya sake yi ya je friza ya d'auko hollandia mai sanyi yazo dining.

Ido ya zaro alamar tsoro don wasu manyan tsutsotsi ya gani suna yawo a rabin abinci da baya yasoma ja sai ganin koyayen d'akin sun d'auke hoton Yasirah dake mak'ale a d'akin ya haska ya tsatstsage wani irin mumunan fuska ya gani a cikin hoton sai ji yayi ana kiran sunansa Ya....sa...r! Ya.....sa...r!! Ya....sa...r!!! Cikin wata irin murya mai ban tsoro ga haske da ke haskashi wal-wal sai ya d'auke gurin yayi duhu tsoro ne ya soma kama shi

Rash
Sanah

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts