New Post

Friday, 7 July 2017

Yar Mafiya.. 29-31

[12:54PM, 1/13/2017] Aunty Wawu: �� *'YAR MAFIYA*��
Sanah S Matazu
Rash Kardam
*29*
Tunda aka soma shirye-shiryan kai amarya Yasiraht ta rasa nutsuwarta ga wata faduwar gaba da take mai tsananni. Da magariba aka soma yimata mitar taki shiryawa tilas ta soma niyyar shiga wanka lokacin data fito babu kowa dakinta ta lumshe ido tana tuna kalaman Yasmin.

"Aunty Yasiraht nima inaso ayi biki a gidanmu,ayi taro musha shagali".

Hawaye mai zafi ya zubo mata, tai murmushi tana furta.

"Yasmin sai na dauki fansa jininki yantacene'.

Shigowar kanwar mahaifiyarta yasa tai saurin gogge hawayan ta hau shafa mai. Kafin  mintuna goma ta shirya aka wuce sashin mahaifinta da ita.

Nasiha sossai mai ratsa jiki yai mata haka ma mahaifiyarta, daga nan aka nufi wajen mota da ita wani gunjin kuka Yasiraht take musamman dataga dagaske nisa zatai da gida. Haka aka sakata a mota zuwa gidanta dake unguwar Federal law cost.

Yan kai amarya kowa ya watse sai ita da kadai,kamar almara bangon dakinta ya soma darewa suka dunga biyo layi a shirye-a-shirye harsu ashirin da hudu cif.

Kowannansu sanye cikin jajjayan kaya da bakin dankwali, hannunsu rike da kokkouna cike da  jini suna kallonta.Najwace kan gaba tana murmushin mugunta.Samar na gefe a tsakiyarsu yaci kunu yana dubanta,ya tsuke girar sama da kasa yana muzurai ya dubeta da kakkausar murya.

"Yasiraht kin bata mana tsari kin cutar da zukatan yan kungiya, yau bandan inasonki ba sai na hallakaki amma zamu dauki fansa kan mijinki kwatankwacin kuntatta mana da kikayi"

Bat suka bacce saboda shigowar Yasar da abokansa, nan akaita barkwanci Nawas yai musu nasiha sukai salama ya tafi yi musu rakiya.

Sanah
Rash
[12:54PM, 1/13/2017] Aunty Wawu: �� *'YAR MAFIYA....*��

*Rash Kardam*
        *Sanah S Matazu*
*N. W. A*
Page
*30*

Yasar yayi rakiya ma abokansa waje nan suka yi sallama ya fawo gida cike da farin ciki yake hawar matakalan har da d'an gudunsa. Yana isa falo ya tarar ta shiga d'akinta kasancewar lokacin k'arfe goma da kusan rabi a hankali ya taka har zuwa d'akin ya saka hannu zai bud'e k'ofa  sai yaji kamar ana kwan kwasa gareji ya share zai bud'e d'aki sai yaji yanda ake buga garejin kaman za'a cire a jiyeshi a gefe.

Cikin b'acin rai da fushi ya nufi fita ya waye haka mai buga k'ofan don shi ya gama tanadin bazai fita ba ya shigo kenan ya sanya k'afarsa a step na farko  kattt! Wutan gidan gaba d'aya ya d'auke tare da wani irin k'ara mai shiga kunne a hankali uuuuuwu! Irin karannan wanda zakana jinsa cikin yana yin abun tsoro. Duhu sosai yake gani baya iya ganin hannusa bare fararen kayan da ke jikinsa duk sun zama baki.

Cikin dauriya ya sauk'a zuwa gate yana fitow haraban gidan yaji bugun k'ofan ya tsananta, sauri ya k'ara abun mamaki yana zuwa aka dai na kuma ba mai gadi a gun k'aramin k'ofar ya bud'e ya leka waje amma ba kowa a ciki da sauri ya dawo ya mayar da gate d'in ya rufe.

Har lokacin da ya dawo gun d'akin mai gadi baya nan a hankali yasoma tafiya yazo dai-dai zai shiga cikin falo sai hango wani yayi da fararen kaya yana tafiya zai nufi garden kuma wannan yana yin jikin bana mai gadi bane don yayi tsayi da yawa ga shi ko fiskansa baya gani fararen kaya sun b'oye shi.

Da sauri ya ce“Baba Mai Gadi!. Yaji bai amsa ba kuma ya ci gaba da tafiya ganin haka ya soma binsa da sauri kafin ya cimmasa har ya b'ace sai da ya duba gurin bai ga kowa ya juyo sai ya sake ganinsa ya nufi cikin gida mai fararen kayan da sauri ya sake binsa.

Har yanzu wannan k'aran yana jinsa da sauri ya fara haurawa mata kalan yana bin mai farin kayan ya hau matakala sai yaji an rike masa k'afa cikin sauri yasaka hannu agun sai jin hannu yayi amma ba alamar mutum da sauri ya feta k'afarsa sai yaji an sake sa da gudu ya haura sama ya shiga falo.

Rash
Sanah
[12:54PM, 1/13/2017] Aunty Wawu: �� *'YAR MAFIYA....*��

*Rash Kardam*
        *Sanah S Matazu*
*N. W. A*
Page
*31*
Yana zuwa hakki yasoma yi ya d'an jin gina da k'ofar gashi da duhu gun ga wayarsa ya manta a motarsa ba kuma toci bare ya haska, sai yaji ihun mai gadi da k'arfi yana kiransa yazo ya tai maka masa.

Cikin tsoro ya soma bud'e tagan don ya lek'a ya ga miye  amma yaki bud'uwa gashi ihun sai k'ara yawa yake yi, da sauri ya soma sauk'owa don ya tai maka masa bakin Yasar ya kasa furta ko da kalma d'aya na addu'a.

Yana isa bakin gate yaji ba kukan kuma ba mai gad'i a gun yana 'yan dube-dube sai yasake jin ihunsa a cikin gida da sauri ya haura saman ya zo dai-dai k'ofar shiga falonsu ya yi k'aro da wani abu kamar katako amma dogo ne da tsayi sun kuyawa yayi ya fara lalub'e cikin zuciyarshi ya ce“wannan kaman ```Makara``` ne cikin ```Makaran``` ya taba yadi yaji, da sauri ya dauki ko ya bude yadine fari kal kaman ```likkafani``` ko ince ```likkafanin``` ma.

Tsoro ne ya fara kamasa ya soma ja dabaya gani yayi ```Makaran``` yana binsa ga yadin ```likafanin``` sai k'ara haskawa yake yi a hannusa.

Cikin wata irin murya mai firgitarwa ya ji ana cewa“ ```Yasar``` kayi gan-ganci shiga hurumin da bana ka ba kasani yau kwananka ya k'are nine nan zani ```AJALINKA".``` ido ya zaro sai cikin tsoro ya ce“mai na muku da kuke bibiyata haka?". Wani irin dariyan da ya haddasa gidan gir-giza yaji ance“mu ba dogon zance muke so ba ga wannan ```Likkafanin``` na kane anan zamu kashe ka ba tare da anyi maka wankan ```gawa``` bare a maka sallah zamu gama da kai hahaha!!!".

Rash
Sanah

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts