New Post

Friday, 24 February 2017

MOTAR KWADAYI PAGE 1

MOTAR KWAYI
BY

Rash Kardam

Bismillahi rahmanu rahim.

Dukkan yabo, godia da tsarki, Mulki, sun tabbata ga ubangijin Al'arshi maigirma.

1

Sauri2take tafiya, duk da saurin da takeyi, hakan ba zai hana ka gane, cikin nutsuwa ta ke tafiyar ba, sanye take da hijab dinta har kasa, kalo daya zaka mata ka gane yarinyar yar mutumci ne, kuma tana da hankali.

Kalo na kai duba zuwa ga fuskan ta ba laifi, tana da dogon hanci, gata da yalwan gashin gira, wanda ko da batai ja gira ba, hakan ba zai boye kyan da Allah ya mata ba, tana da yar kamar baki, sai manyan idonta masu fisgan mutum, tana da haske dai2 gwargwado, ko dana kara kalonta, tana da dan zayi san'nan ba za'a kirata da guntuwa ba, ba kuma za'ace mata doguwa can ba, tana da jikin ta dan dai2, abun sai wanda ya gani.

A hankali ta rinka tafiya, har ta iso gurin masu sai da icce, sallama ta musu, tace baba mai ice aban dami daya, nan ta mika masa naira hamsin, ta zabi mai kyau, wanda tasan zai yi ci, daukowa tayi, ta nufo gida, sauri takeyi don yau basu daura girki da wuri ba, kasan cewan yau Umman ta ke da girki, sauri take har ta iso dan ma dai2cin kofar gidansu, sam bata lura da addah Safiya tana zuwa ba, sai ji tayi sun karo da mutum, ga iccen ya bugeta soaai wani uwar ashar ta narko, Ayshat tuni ta san kame agurin, cikinta ya soma dura ruwa, don ta san yau ta jaza musu kwandon bala'i, bakin ta na bari, tafara Adda dan Allah kiyi hakuri bada sani...... Ai bata karasa ba ta ji saukar dun'du, a bayarta, Inna safiya ce, tace wato bakin halin ki da na uwarki da kika gado, ya sauko kan tilon yata, yar gwal ko don kunga ku bakin jini ya muku yawa, kin rasa mai tayawa shiyasa za'a sauke akan diyata, to ahirr... Bazaku iya ba, tayi muku nisa, nan takama hannun safiya suka nufi cikin gd, safiya sai wani karai raya takeyi, ita ala dole mai kyau, kallo na tsaya kare mata, ba laifi tana da kyau dai2 gwargwado kuma farace ainun amma ta hada da man bleaching, san nan ga duk wanda yasan kyau, Aisha tafi Safiya kyau ita dai safiya farinta yayi yawa, gashi ta hada da man bleaching.

Aisha ta dau iccenta, jiki ba kwari ta nufi cikin gd, da sallamarta, tashiga dakunsu, nan ta tarar da ummanta, ta zabga uban ta gumi da sauri tayi gunta idonta fal da hawaye, tace ummah banson kina wan'nan yawan tunanin zai iya jawo miki matsala, wataran sai lbr, kuma duk abunda yayi farko zaiyi karshe, sai da ta tabbatar hankalin umma ya kwanta, ta nufi kitchen don ta musu aikinsu, Aysha kenan yarinya mai hankali da nutsuwa.

............. Na.....
Rash Kardam

1 comment:

Popular Posts