*'YAR MAFIYA*
Sanah S Matazu.
Rash Kardam
*26*
Cikin wani surkukin daji, babu gida gaba babu gida baya Yasar ya tsinci kansa.Take garin ya juya masa, sama tai jajjur a kasa kuwa wasu irin macizaine nannade da kafaffunsa ya kasa katabus wani nannauyan naushi aka kai wa kuncinsa a sukwane ya kauce dukan yafi iska. Wata muguwar bahaguwar murya ta ziyarci dodon kunnuwansa, cikin rashin zato.
"Yasar ka fita hanyar Yasiraht, domin ita din mallakin shugabanmu ce kuma dokar kungiyarmu babu aure".
"Bazan fita ba domin Yasiraht rayuwata ce".
Ya fada da kakkausar murya mai amo, take wata irin dariya ta soma karade kunnuwansu.Cikin tashin hankali ya sa hannu ya toshe kunnuwansa, bai auneba aka soma jansa wani wawwakekken rami ya na ji yana gani ya kasa kubuta.Cikin bazata ta bayyana a wajan cikin sakan guda ta warceshi suna hadda ido ta watsa masa harara cikin fushi tace.
"Mudin kana sakaci da addu'a kana tare da gaggarin rayuwa".
Firgiggit ya tashi, zufa, zazzabi tashin hankali sukai masa rufdugu lokaci guda.Ya daga kai ya kali agogo, karfe biyun dare cike da tsoro ya dire ya dauro alwala ya soma gabatar da nafilfili.
Sai goshin asuba ya dakata ya dora da karatun alkur'ani mai girma, ana kiran asuba yai raka'atul fijir yai sallah ya dan kwanta.
Washegari ya tashi da karfin zuciya yana jin nishadi a ransa sossai, karfe takwas ya fito cikin shirin fita.A daining sukai clash da Yasiraht suna hada ido wani abu nannauya ya daki zukatansu Yasiraht ta lumshe ido batare da ta sani ba.Cikin zuciyarta tace "Allah ya yi hallita" tai saurin dauke idonta daga kansa tace"morning broth" bai tanka ba ya wuce abinsa.Tai murmushi tana jinjina yadda ya shareta.
Sanah
Rash
0 comments:
Post a Comment