*'YAR MAFIYA....*
*Rash Kardam*
*Sanah S Matazu*
*N. W. A*
Page
*25*
Bata tanka ba ta wuce ta rufemasa office din, ya cigaba da jujjuya maganarta a ransa.Shigowar Nawas ya katsemasa tunani, yace "Ango! Ango!! Ango!!! Dariya kawai yai suka soma hira.
Sun jima suna hira yai masa sallama ya wuce, haka Yasar ya yini sukuku da shi.
Ana tashi daga aiki ya d'au jakarsa da wayoyinsa ya fita motarsa ya bud'e ya shiga ya tayar ya d'au hanyar gida zuciyarsa cike da tunani kala-kala yana cikin tuk'i sai yaga wata ya rinya cikin fararen kaya ta baza gashinta ba'a ko ganin fuskanta ga ganin haka ya yi shirin taka burki cikin sauri ta juyo garesa tare da ihu ga hak'oranta sun fito, bai san lokacin da ya saki ihu ba ya sake sitiyarin motar ya rutse ido don ya sadak'ar mutuwa zai yi.
Cikin sauri Yasirah ta bayyana gaban motar ta rik'e sitiyarin cikin salon tsafi ta mayar dashi gefen hanya duk abunda yake faruwa idonsa na rufe jin motar ya tsaya ya bud'e idons a hankali dai-dai lokacin Yasirah ta juyo garesa karaf fiskansu ya had'u dana juna hancinsu har na gogan na juna take numfashinsu yasoma fita da sauri-da-sauri kasa d'auke idonsu suka yi daga kallon juna kalon ido-cikin-ido.
Yasirah cikin zuciyarta cewa take“tabbas Yasar ya had'u irin had'uwar da kowacce mace ke fatan malakan miji kamar sa, had'uwa bana wasa ba ni sai yau naga yafi min ko yaushe kyau da kwarjini gashi wasu na farauta rayuwanka d'an uwana kai nake so ada gashi yanzu ina jin abubuwa game da kai da dama alokacin da wasu ke neman yi mana sha maki da juna".
Yasar shima a gunsa abun haka yake baran shida tun haihuwar Yasira ya ke tsananin sonta matsalar d'aya ce abunda ta aikatawa". Bai san lokacin da ya saki ajiyar zuciya ba kafin ya sake duba Yasirah ta b'ace ba labarinta shi yanzu abun ma tsoro ya fara bashi sai da ya 'yan waige-waige bai ga kowa ba da gudu ya tayar da mota ya bar gun ko da ya isa gida yamma tayi sosai abincin ma kasa ci yayi tunanine kala-kala a zuciyarshi sai da aka kira sallah ya fita sai bayan isha'i ya nufo gida zuciyarsa cike da tsoro da ikon yau yashigo lafiya ba abunda ya gani har kusan tara na dare hakan yasa yayi shirin kwanciya ya kwanta.
Rash
Sanah
0 comments:
Post a Comment