[12:54PM, 1/13/2017] Aunty Wawu: *'YAR MAFIYA....*
*Rash Kardam*
*Sanah S Matazu*
*N. W. A*
Page
*36*
Jabir da Najwa sai keta tsaunuka sukeyi sai da suka isa wani kogon dutsi suka tsaya yada-zango don su huta a gun. Najwa da ta gama galabaita ga tabo a jikinta cikin murya gajiya da wahala ta ce“Jabir nagode da ceto na da kayi nasu damar da zan k'arasa d'aukar fansa na".
Murmushi Jabir yayi ya ce“karki damu na tai maka miki ne don nima ina da wani kuduri akan Samar ina so mu had'a hannu da k'arfe muga bayansa kamar yanda yasaka muka kawo iyayen mu da masoyan mu".
Najwa tayi murmushi ta ce“ni kuma ina matuk'ar k'aunan samar bazan iya cutar da shi ba sai dai fansa na akan Yasirah ne ita zanga bayanta".
Jabir ya numfasa yana nazarin kalaman Najwa amma sam bai ji zai fasa abunda yayi niya ba.
A can dajin *KARAMGATURA* cikin gidan Sarauniyan Aljanu *Samriyana* tana ta kula da Yasirah wanda tsafin yasoma tasiri a jikinta. Duk jinyan da take mata a banza ne wana hakan yasa tafara tunani taya zata tai maki wannan yarinya don bazata tab'a mantawa da alherin da mahaifin Yasirah ya mata ba shiyasa a ko da yaushe ta ke bibiyarsa tana tunanin ta inda da zata rama wannan alherin don *Alkairi danko ne* baya tab'a fad'uwa kasa banza haka.
Ajiyar zuciya ta sauke ta lumshe idonta tare da gyara dogon gashin da ya sauka har kusa da gwiwar k'afanta tana kara nazarin rayuwanta.
*WACECE WANNAN SARAUNIYA SAMRIYANA?.....*
*MAI NENE ALAK'ARTA DA BABAN YASIRAH WATO S MARAFA?....*
```Don jin wa'yan nan amsoshi ku kasance da.```
Rash
Sanah ku ce.
[12:54PM, 1/13/2017] Aunty Wawu: *'YAR MAFIYA....*
*Rash Kardam*
*Sanah S Matazu*
*N. W. A*
Page
*37*
Sarauniya Samriyana ta kasance 'Ya d'aya tilo ga Sarki Sarguna sarkin aljanu na k'arni goma da ya wuce, ya kasance Sarki ne mai kwatanta adalci a tsakanin mutanen garinsa *KARAMGATURA.* Suna jin dad'i mulkinsa kuma suna masa biyayya da kyautata masa a matsayinsa na shugaba. 'Yar sa d'aya tilo ita ce *Samriyana* yarinyn da ta gado halin mahaifinta ga son tai makon jama'a.
*Samriyana* ta kasance mai son zaga duniya taga mai ke gudana wata rana ta fito ita kad'ai ba tare da hadimanta ba ta iso k'asar Nigeria sai da ta zagata har ta iso garin Bauchi, tayi kwanaki a garin tana zagawa sabida yanayin garin ya burgeta hakan yasa tayi kwanaki a cikinta tana yawo.
Wata rana cikin irin yawon da takeyi a garin Bauchi ta bullo ta wani unguwa, da alaman unguwan na masu hali ne gashi ta galabaita da yawa don yunwa ta keji ga kishin ruwa.
Taje gida yafi nawa a rin yanayin da tarikid'a takoma kamar mai bara sai su wulakanta ta su kure ta a haka har tazo bakin titi ta zauna ta zuba tagumi sai hamma take yi. Sani Marafa ne ya fito daga makaranta tun kafin yayi aure yana matashi lokacin ma a makarantar gaba da primary yake. Ya hangi wata mata cikin yanayin tausayaa da har zai wuce sai yaga tana hawaye tana magana a hankali bai jin mai take fad'a, cikin tausayawa ya matso kus da ita ya ce“bai war Allah lafiya kike zaune anan?". cikin yanayin wahala ta ce“ka tai maka min da ruwa yunwa nake ji". Cikin hanzari ya juya yaga gurin da suke da gidansu akwai tazara gashi bai da kud'i sai naira d'ari. Hakan yasa ya ce“bai Allah kiyi hakuri naira d'arine ya rage a jikina amma barin sayo miki ruwa da bredi kinji".
Da sauri ya nufi wani shagon da ke nesa da gun ya sayo mata bredi da ruwa ya kawo mata ya bata hakuri.
Sanah
Rash
[12:54PM, 1/13/2017] Aunty Wawu: *'YAR MAFIYA....*
*Rash Kardam*
*Sanah S Matazu*
*N. W. A*
Page
*38*
Da sauri ta karba tana ci kamar mahaukaciya duk sai ta bashi tausayi sai da ta gama ci ya mata sallama ya ce“ni zan tafi gida gashi bani da wani abu da zan tai maka miki amma kiyi hakuri". Ya mike ya fara tafiya.
*Samriyana* sai da taga yagi nisa ta mike ta bace ta na binsa ba tare da ya sani ba.
S Marafa yana isa gida ya gai da Mamansa aka kawo masa abinci sai da yayi wanka ya sanya kaya ya d'auko kularsa zai ci abinci sai ya bud'e yaga girkin Mashaa Allah yayi sai kamshi ke tashi, yazo zai saka hannu sai ya tuna da matar d'azu a fili ya ce“ni yanzu gani zanci abinci mai kyau yayi da wasu ke nima kuma ina ci zan ban saura don haka barin raba biyu inci rabi in kai wa matar nan rabi Allah zai ban ladan tai mako". Murfin kulan ya jawo ya raba ya diba nasa yasa a murfi ya ci tukun ya mike ya nufi cikin gida.
*Samriyana* da ta biyosa duk abunda yake fad'a taji ta gani hakan yasa ta bace ta koma inda ya barta tana mamakin asai yanzu ana samun masu tausayi irin Sani.
Sani yana shiga gida friza ya bud'e ya dauko juice gora daya da goran ruwa ya fito ya d'auki kulan ya nufi inda ya bar matan.
Yana zuwa ya sameta a inda ya barta nan ya mika mata kulan sai da tayi godiya ta karba taci nan ya mata sallama ya koma gida.
Yana tafiya ta bace ta dau hanyan garinsu tana mai farin ciki ko da ta koma sai da ta sanar da mahaifinta abunda ya faru ya ji dadi ya ce“ina so daga yau kina bibiyansa da hadimanki duk wani abun tai mako in ya taso masa kina masa in har baifi karfinki ba.
Sani Marafa washe gari da ya dawo bai sake ganin matan ba tun yana bibiyan gun har ya hakura haka kurum ya tsinci kansa da son tai maka mata don yana mata kalon ta haifeshi ko tayi jika da shi.
To kunji wannan shine dalilin da yasa Samriyana ta tai maki Yasirah wanda da badun Allah ya kawota a wannan lokacin ba da an shude tarihin Yasirah.
Rash
Sanah
0 comments:
Post a Comment