[12:54PM, 1/13/2017] Aunty Wawu: *'YAR MAFIYA....*
*Rash Kardam*
*Sanah S Matazu*
*N. W. A*
Page
*32*
Cikin rawan murya Yasar ya ce“ waye kai dan Allah?". Sai da akayi wani dariya mai amo sanan ya ce“nine nan ```ALJALINKA! AJALAINKA!! ALAJALINKA NE!!.``` hahaha!!!!". A ka ci gaba da dariya Yasar na ganin haka bai san lokacin da yayi wani tsalle ya tsallake makaran ya nufi cikin falo da gudu.
'Dakin da ke farkon shiga falon ya shiga yana shiga sai yaga an kawo wuta nan yaga abu a lulub'e da farin kyalle wanda zamu iya kiranshi ```likkafani``` an rufe abu dashi ga jini ya b'ata shi da sauri cikin tsoro ya je ya bud'e wa zai gani Baba mai gadi ne wance matatce a cikin jini da baya yasoma ja jikin tsoro dun ya gama razana.
Samar ya kalli Najwa ya ce“ki je gun Yasirah kiyi ta janta ban yarda ki cutar da ita ba kin san ina matuk'ar sonta ni zanje na gama da Yasar". Yana gama fad'in haka ya b'ace bat kamar ba shi a gun.
Samar ne ya bayyana a gaban Yasar yana dariya ya ce“kad'an da ga aiki na". Ya nuna kansa da d'an yatsa ya ce“kai ma yanzu zamu gama da kai".
Yasar ya soma bashi a hak'uri batare da b'ata lokaci ba Samar ya ce“da ka bar b'ata bakinka ko ka manta irin jan kunne da muka yi ta maka da tsoratarwa kala-kalq amma ka share don haka yau ba sassauci.
Wani sanda ya soma nuna Yasar dashi take wata irin iska mai k'arfj tayi sama dashi tasoma jujuya shi a saman d'akin tana buga kanshi da bango take jini ya fara zubowa tamkar an kunna famfo.
Rash
Sanah
[12:54PM, 1/13/2017] Aunty Wawu: *'YAR MAFIYA....*
*Rash Kardam*
*Sanah S Matazu*
*N. W. A*
Page
*33*
Samar na b'acewa Najwa ta kece da dariyan mugunta ta ce“daman wannan ranan nake jira tazo ranan d'aukar fansa ta d'aure fiska ta ce“ni Najwa ```Bana yafiya bana manta ranan d'aukar fansa".``` tabbas Samar kayi gan-ganci barina da Yasira a ranan ta yau". Tana gama fad'in haka ta b'ace bata bayyana ko ina ba sai d'akin Yasirah.
Amarya Yasirah ganin ango ya fita rakiya nan ta soma rage kayan kyale-kyalen dake jikinta zoben gwal ta cire sannan tashiga bayi ta watsa ruwa tana fitowa ta shafa mai tasaka kayan bacci riga da wando masu d'an kauri bayida shara-shara sosai sabida yanayin huturu da ake ciki.
Najwa ne ta bayyana gaban Yasira nan ta kalleta ta ce“kee Yasirah ina mai farin cikin sanar da ke ranan dana ke jira tazo ki sani ina tare da Mijinki Yasar Yanzu haka kuma yana gab da mutuwa". Tana fad'in haka ta b'ace.
Yasirah na jin haka itama tayi siddabaru ta b'ace nan ta hango Najwa ta nufi wani daji cikin hanzari ta bita da kyar ta isota tana zuwa taga bata gun sai can ta hango wani k'aton maciji yana kawo mata hari nan ta gane Najwa ne itama ta rikid'a ta dawo wani k'aton kububuwan maciji nan suka fara fafatawa cikin salon tsafi dankwarewa. Sun d'au kusan awa d'aya da kyar Najwa tayi nasaran cire wannan babban Zoben sihirin da ke hannu Yasirah wanda dashi ne yake sarrafa mayan siddabaru da tsafin da takeyi.
Najwa tana saka zoben a hannuta ta kece da dariya ta ce“tababs yau buri na ya cika yau zan b'atar dake a doron k'asa sannan kuma Yasar yana gun Samar ya gama dashi". Nan ta bayyana mata hotonsu Yasirah na ganin haka ta saki k'ara ranta ya b'aci gashi ba halin yin wani yink'uri.
Najwa ta nuna Yasirah da wannan zobe tasoma wasu surkulle. Kuma in har wannan surkulen ya kama Yasirah to narkewa zatayi ta k'one q gun ta zama tarihi.
Shin masu karatu
Samar yana nasaran kashe Yasar kuwa?.
Shin Najwa na cimma burinta akan Yasirah kuwa?.
Don jin wannan amsoshin sai ku biyo mu.
Rash
Sanah
[12:54PM, 1/13/2017] Aunty Wawu: *'YAR MAFIYA*
Sanah S Matazu
Rash Kardam
*34*
Take Najwa ta soma wani irin surkule tana karanta wasu dalamusan tsafi batai aune ba ta nemi Yasiraht ta rasa. Nan ta soma yunkurin nemanta amma babu alamunta hankalinta yai mugun tashi ta bace saboda yadda tsafin ya soma cin jikinta.
Yasirah na hango a hannu wata Tsohuwa mai shiga ta kamala ko da na kalli k'afar matan kwafato ne irin na doki gashin kanta fari k'al kamar auduga. Cikin ke keb'antacan daji mai cike da ni'ima, take tafiya da Yasirah a kafad'arta sai da tayi tafiya mai nisa naga ta tsaya a wani gili wanda namun daji irin su Kura, Damisa, Zaki, B'auna su suke mata gadin gidanta. Katangan gida na alfarma da gani kasan ginin aljanu ne saboda bene ne hawa uku komai akwai a ciki. Tsohuwan ne ta kai Yasirah wani d'aki ta kwantar da ita gashi ko motsi bata yi da alamar kamar ba numfashi a tare da ita.
Washegari da safe aka aiko a kawo musu abinci, dan 'yar aika tana shigowa ta haura sama shuru taji kamar alaman bakowa haka kurum taji gabanta na fad'uwa, da sallamanta nan tayi karo da Yasar kwance cikin jini ko motsi ba yayi.
Cikin tashin hankali ta fita da gudu ta sanar ma driver tare suka shigo ganin halin da Yasar ke ciki ya d'aga waya ya kira Abba ya sanar masa cikin tashin hankali ba tare da b'ata lokaci ba sula iso. Aka dauki Yasar zuwa asubiti, babuma lokacin tambayar ya hakan ta faru.Dr yai ta fada sabida yaga yamusu matsalarsa, to harzuwa wayewar gari baima farfadoba hankalin Hajiya Nafisa ya tashi sossai duk tayi zuru-zuru.Sai lokacin suka soma bincikar ina Yasiraht asibitin suka baro Yasar kwance suka nufi gidan.
Samar ne ya bayyana gaban Najwa yana huci bai saurareta ba ya sureta. Bai dire ko'inaba sai cikin wasu mugayan tsaunuka, take yai nuni da hannunsa wani dutse ya fashe wasu sarkoki suka bayyana ya daureta a jiki tamau tamkar daurin goro.Yai nuni kujera ta bayyana ya hau kai ya dora daya kan daya yana murmushin mugunta.
"Baki da mutunci Najwa, zanyi maganinki".
"Kayi kuskuren bani amanar Yasiraht walahi saina illatata".
Bai tanka ba ya wuce, ya bari ana azabtar da ita. Kwanan Yasar hud'u a gadon asibiti bai san inda kansa yake ba kuma kwanansa hudu bai farfadoba hankalin kowa ya tashi musamman da likitoci suka bada tabbacin in ya kai kwana biyar komai zai iya faruwa..
Sanahku
Rash taku
[12:54PM, 1/13/2017] Aunty Wawu: *'YAR MAFIYA*
*35*
Sanah S Matazu.
Rash Kardam.
Sai can dare Hajiya ta soma tambayar ina Yasiraht lamarin daya haifar da kace nace ita ta zauna mahaifinta ya nufi gidan.Tunda suka shiga shi da Nawas gabansu ke faduwa harzuwa cikin falon nan suka tsaya turus sakammakon ganin gawar Baba maigadi cikin kaduwa sukai kansa harya soma bugawa da sauri Nawas ya kai hannu zai buda Daddy ya rike shi karka taba kira police.Kafin mintuna uku yaiwa abokinsu waya nan da nan aka shigo tare da magunguna akai amfani dasu aka dauke gawar harta soma bugawa.Nan suka hau neman Yasiraht babu ita babu dalilinta sai kayanta wanda aka kawota dasu jiki a sanyaye suka fito daganan aka nufi policestation akai refort babu amarya babu dalilinta.
Hankula ya tashi sossai neman Yasiraht ake amma amsar d'ayace ba'a ganta ba lamarin daya dugunzuma hankalin danginta sossai ga Yasar rai a hannun Allah kwata-kwata bai san wanda yake kansa ba.Tsayin kwana biyar ana nemanta, nan iyayanta suka fida tsamanin ko an sace ta ne nan da nan suka buga bayanai a jaridu da mujalu tare da makudan kudi kyauta ga wanda ya samota.
Najwa ta shiga matsanancin tashin hankali, daboda tunda Samar ya daureta ya tafi bai waiwaye ta ba hakan yai matukar tada mata hankali duk wani yunkurinta na tsinka sarkokin tsafin da suka daureta abun yaci cura duk ta rame ta kwantsame ta fita hayyacinta yunwa da kishirwa sun soma galabaitar da ita kwatsam Jabir daya daga cikin yan kungiyarsu wanda ya kasance daga Samar sai shi ya bayyana ya kwance ta suka bar wajan.
Rash
Sanah
0 comments:
Post a Comment