New Post

Friday, 7 July 2017

Yar Mafiya..27-28

[12:54PM, 1/13/2017] Aunty Wawu: �� *'YAR MAFIYA....*��

*Rash Kardam*
        *Sanah S Matazu*
*N. W. A*
Page
*27*
Yana fita yaje ya gai da su Abba nan Abba yake tambayansa “ya shirye-shiryen biki?". Cike da jin kunya Yasar ya amsa da “Alhamdulilah! Abba mu kai". Abba ya ce“madallah! Allah yayi albarka a kara kula katashi ka tafi aiki kar ka makara". Cikin ladabi ya mik'e ya fita motarsa ya shiga ya nufi office cike da jin ni shad'i.

aiki yayi sosai sai da lokacin sallah yayi ya fita yaje masallaci bayan ya idar da sallah ya nufi office kenan suka had'u da Nawas cikin zolaya Nawas ya ce“Ango! Ango!! Kai tun ba'ayi bikin bama naga kasha mai sai wani shek'i kake yi dan Allah miye sirri?". Cikin sigar zolaya da raha yayi maganan.

Yasar ya ce“ sirrin da ka gani Amarya na kusa dani ya bazanyi mai k'o ba". Shima cikin sigar wasa ya mayar masa da amsa.

Nawas ya ce“maganar gaskiya ya kamata mu tsaya mu tsara biki yau saura sati uku biki amma banga kana wani shiri ba?".

Yasar ya ce“shiri ai nakune kune manyan abokai nawa akai min ne kawai".

Nawas ya ce“ai baka isa ba dole mumaka 'yan jike-jike sabida ka dawo tuzuru kaga kar kaje ka....“.

Yasar ya ce“kai ka sani ni lafiyata lau aha zam-zam nake".

Haka suka yita raha daga k'arshe Yasar ya ce“ka bar magan bikin nan inaga sai a weekend sai mu tsara komai in Allah ya kai mu".

Nauwas ya ce“ba matsala Angon Yasirah kuma 'Ya'yan Abba". Da haka kowa ya nufi office d'insa basu fita ba sai yamma da'aka tashi daga aiki kowa ya nufi gida.

Yasar ya na zuwa gidan Abba ya wuce don haka kurum yaji yana son ganin Amaryansan yana zuwa ya ajiye mota ya shiga gida da salalmansa ba kowa a falo hakan yasa ya wuce d'akinta.

K'ofan ya tura ya ganta tana bacci sai murmushi take yi a hankali ya tako har zuwa bakin gadon ya zauna a d'an k'aramin kujeran da ke bakin gadon kalon ta yakeyi cikin so da k'auna bai san lokacin da bakinsa ya fara furta “Yasirah ina tsananin k'aunarki gan-gan jikina mallakin kine a duk lokacin dana kalli kyakyawan fuskanki nakan tsinci kaina cikin nishad'i wansa bazai misaltu ba".

A hankali ya sauk'e numfashi tare da lumshe idonsa ya bud'e ya cigaba da cewa“ban san mai yasa baki sona ba kuma kika fad'a wani irin hali wanda nagasa a hak'uri akanki ina matuk'ar kaunanki Yasirah". Hannuta ya kama ya mata kiss ya fita abunsa.

Rash
Sanah
[12:54PM, 1/13/2017] Aunty Wawu: �� *'YAR MAFIYA*��
Sanah S Matazu
Rash Kardam
  *28*

Kwanci tashi babu wuya wajan ubangiji biki ya rage saura sati daya,duk kauce kaucan Yasiraht sai da ta tsaya ta saurari Yasar suka shirya lamarin bikin.Duk ta rame ta fita hayyacinta, ga yawan barazanar Samar da kungiya da take samu.Ga rama Najwa ta lafaffa mata ganin zata auri wani ta barmata Samar.Sai dai a wani fannin tana taya Samar kishi domin samun shiga wajansa, tare suke yakin.Rana bata karya sai dai uwar diya taji kunya, cikin hukuncin ubangiji aka soma shirye-shiryan biki gadan-gadan babu kama hannun yaro.

Ranar Alhamis sukai kamu, a babban dakin taro na Hajiya Rash dake Bauchi .An shirya wajan ya kawatu sossai, yara matasa aka samu sukai shigar yoruba kowace tasha murjani ta tamke kugu tamkar ahlin emeka su goma shabiyu ne suka saka amarya a tsakiya suna tafe suna watsa mata wani hadin turare mai hade da furani sunai mata kirari.Har zuwa tsakiyar dakin taron wanda ya kawatu da shimfidu kilisai da tum-tum tamkar diyar sarauta.Yasiraht sanye take cikin wani rantsatsan swice kalar blue light, an mata head pink kafarta flate shoe shima pink sai mayafi da aka lulluba mata kalar azurfa mai ratsin golden.Fuskarta ta kawatu matuka,sai sheki take tana zama ta dago kai dam! Gabanta ya fadi saboda hango Najwa da Samar cikin tawagar biki tai saurin dauke kanta tana mamaki.Batai auneba yara matasa kimanin mutum sha biyu suma suka sako Ango gaba, tamkar yadda akai mata. Dukkansu suma suna sanye da kayan yoruba da izga da murjani nan fa waje ya dauki tafi ni kaina sun burgemu har Rash ta dubeni tace.

"Cwt Sanah nima haka zan yi da bikina amma shigar Larabawa".

Na saki murmushi nace "ni kau shigar Fulfulde ko Kanuri zan yi".

Mukasa dariya muka maida hankali kansu, a hankali Malama Husnah Muhammad Inuwa ta bud'e taro da addu'a ta soma lacture kan biyayyar aure.
_"Bisimillahir-rahmanir rahim yake kawata yata yayyata kakkata, da duk wata mace dake wannan waje. Inaso ki bude kunnuwanki ki ssurarreni,shin kina cikin sahun mata nagari?  Idan ma bakya ciki saurarreni domin zama abar alfaharin mijinki in kuma kina ciki kikara kaimi. WACECE MACE TAGARI?.Mace tagari itace takan yi kokaarin tazamar wa mijinta aljannarsa ce, batason taga gazawarta a idanunsa,don haka takan yi farin ciki idan taga murmushinsa takan damu matuka in taga fushinsa koda badaita yake ba.Bata jinkiri a wajen abinci, kuma ta iya dafawa batare da almubazzaranci ba, itace amintacciyar abokin shawararsa, mai iya rike masa sirri, bata yarda wani yasani ko waye kuwa, sannan ga taimako._

_Mace a kullum mai sanyaya raice ba mai jiran a sanyaya mata ba, farin cikin maigidanta shi ne nata, komai yabata takan gode, ga fadin yi haquri kamar nunfashinta.Tana fama da baqin ciki amma tayi dariya,tanajin zafin abin da mijin yayi mata amma tayi tunanin yadda zata faranta masa rai._
_Aure sunna ce da Annabawan Allah duk sukayi,ya kamata mugaya matansu suka zauna dasu ???Bai dace ba kowane mutum ya riqa jin matsolinki da mijinki, sai in abin yafi qarfinki.Mace tagari mijinta shine komai, koda bai iya soyayya ba.Bata zama a gabansa ko gefensa saida yardarsa,takan cika da ladabi aduk inda yake, takan nuna masa qauna sosai ta gaskiya ce ko qirqira ce kawai.Idan zai fita qafarsa qafarta, idan taji ya shigo ta tarbo shi cikin fara'a da annushuwa, nan da nan tafesa turare ta shafawa lallenta mai yafito sosai ta danyi kwaskwarima, ta canja murya tareda yawan murmushi da fari.Idan zai fita addu'a, in yadawo godiya da murna dafarin ciki._

_Asma'u bnt Kharijatul Furaziy take cewa 'yarta ranar budar kanta cewa:ke cewa 'yarta ranar budar kanta cewa:"Yanzu fa kinfita daga sheqar da aka kyankkyashe zuwa shimfidar da baki santa ba, da abokin tare da baki san shiba, ki zamar masa qasa sai ya zamar miki sama, kizamar masa shimfida zai zama miki turaku, ki zamar masa baiwa, zai zama miki bawa, kar ki nace wajen neman abubuwa domin karya gujeki, kar kiyi nisa dashi domin karya manta dake, idan ya matso, ki kusance shi, idan yaja jiki, kema ki dan ja da baya, amma ki kiyaye hancinsa da kunnensa da idonsa, karya shinshini komai a wurinki sai qamshi, kar yaji komai sai kyakkyawan abu, kar yaga komai sai wanda zai burge shi.Girki, mahalin kwanciyya girmama danginsa mahaifiyarsa haka abokansa.Tattalin kayansa tare da kilace masa su, kula da damuwarsa insha Allahu zai yi farin ciki dake".Dan uwana maigidanta shawara zan baka, ga amana zamu baka a cikin hannunka.Ci da shanta da tufafi suna hannunku,kyautattamata ka rike amana insha Allah ka zamo mai kauna zatai zaman lafiya_

Bayan an gama aka soma rabon abubuwan kayatarwa, lalle turare littafan addu'o.Mazan suka watse aka soma rawar gada.Yasiraht ta saki ajiyar zuciya ganin an kare lafiya su Najwa basu tada rigimar komai ba.

Washegari aka daura aure da safe da yamma akai dinner zuwa dare aka soma haramar sadata da dakinta.

Sanah
Rash.

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts