New Post

Wednesday, 16 August 2017

BABBAN KUSKURE... 106-115

����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

Pg-106~110.

Cikin k'araji ko salati babu ta farka, daga mumunan mafarkin datayi cikin baccinta, duk sassan jikinta rawa yakeyi, kasa hak'ura tayi, tana ga kamar abun da ta gani a mafarki, shi zasu aikata a zahiri. Da sauri ta duro daga kan gado tayi hanyar qofar falo, tsit kakeji ba kowa sai k'aran fanka. Wani ajiyan zuciya ta saki, tare da zuwa window d'akin Indo ta leka, Indo na kwance tana baccinta hankali kwance. 'Dakinta ta koma ta kwanta itama.
Haiydar ko da ya rungume rigan can kuma yayi tsaki"mtsss wai me hakan ke nufi?.
"Ni bana son raini kar yarinyan nan tazo ta rainani.
"Amma fa gaskiya yau tayimin kyau.
"Kamar ba itaba wallahi.
"Mtss to ina ruwana ma da kyanta?. A haka yayi wanka ya kwanta bacci.
Hajiya Fiddausi taje gun boka, a duban da yamata, ha hango zallan koyayar da Haiydar ke ma Indo, don haka yace mata karta damu, su hak'ura ayi auren, don in basu bari anyi da Indo ba, to fa ba makawa sai yayi aure.
Hajiya tana dawowa ta sanar da Falmi duk abunda ake ciki, amma tace"karta ragarmata, ta yanka mata kazan wahalan da bazata iya figewa ba.
Indo ko wasan b'uya suka shiga yi da mutanen gidan, dan tabbasa tasan abunda ya faru, Falmi bazata kyaleta ba.
A gidan Hajiya kuwa Abba ya dawo ta sanar masa da komai.
Yace"zaiyi bincike akan yarinyan, bayan kwana biyu da yayi bincike, duk wani labari ya samu gameda zaman gidan su Falmi, ta hankalin Aisha ila dai rashin mahaifinta da basu saniba. Hakan bai damesa ba yana dawowa gida ya mayar ma Hajiya, yace"inaga bikin nan da wata guda kawai, inyaso komai da uba ke ma yarsa, ni na d'au nauyi zanmata. Hajiya cike da murna ta masa godiya, Haiyadar suka kira sukace"yazo yasamu Abban sa, zasuyi magana da shi.
Haiydar da yazo Abba yace"mun tsayar da biki nan da wata d'aya dan haka kaje ka fara shiri.
"Sannan zansa a gyara maka gidana da ke bayan Airport nan zaku zauna tunda part biyu ne a gidan, kuma tsarin gidan yayi kyau.
Haiydar godiya yayi ya tashi ya fita. Hajiya ta mik'e tabi bayansa, a falo ta samesa, ta zauna ya kara gaidata ta amsa, tace"kaji yanda al'amarin ya kasance ko?.
"Dan Allah inaso ka d'au komai da sanyi wataran zakayi alfahari da auren nan.
"Sannan ina son ka kawo kud'i zamuje mu had'a kayan lefe dana fad'an kishiya.
Haiydar cikin girmamawa yace"to zan ciro kud'i zan kawo muku.
Hajiya ta sanya masa albarka ya mata sallama.ya tafi.
Bayan kwana biyu, Hajiya ta aika Hasna ta je ta d'auko Indo, da duk abunda take da buk'ata, don in ta bar gidan Falmi, ta tafi kenan sai in sun had'u a gidansu.
Hasna jiki na b'ari tayi wanka ta d'au hanya,  tafiya mai d'an nisa tayi kafin ta isa gidan, horn tayi mai gadi ya bud'e mata, tashiga da murnanta tayi sallama. Turus ta tsaya sakamakon ganin Falmi da tab'arya a hannuta, tana tsaye a qofar d'akin Indo tana son ta shiga ta kwad'a mata. Hasna tace"Aunty Falmi lafiya kuwa?.
Cikin fushi ta huyo tace"to bak'ar munafuka algun-guma.
"Har wani tambayan lafiya kikeyi?
"Bacin duk wani muna furcin da ake had'awa dake ne, da tdohuwar uwar ta....
Bata k'arasa ba taji saukan, lafiyayyen mari a fuskanta. Cikin zafin rai ta d'ago da niyar kwad'a ma Hasna tab'arya don a zatanta Hasna ce ta mareta, amma me cikin mamaki take kalon wanda......

                 DEDICATED TO
            AISHA MUHAMMAD
      (MAMAN ABDUL SHAKUR)

            RASH KARDAM��
[5/31/2016] Rash Kardam ����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

Pg-111~115.

Cikin mamaki take kalon Haiydar yau ita zai mara a gaban Hasna ga Indo, shikenan ai raini kam yagama jan mata yau, cikin muryan kuka tace"Haiydar ni ka mara?.
"Kamaren?
"Lallae yau zakasan ka maren?.
Haiydar yace"na lura bakida kunya wato?.
"Duk iskancinki ya tashi a kaina harda uwata ko?.
"Don akan auren da ba so nake ba?.
"Mtss ki sani ni uwata ta isa dani dole ta ban umarni nabi.
"Kuma duk randa kika k'ara zaginta sai kinga abunda zan miki wallahi.
Kalon Hasna yayi yace"kekuma mai kika zo yi ne?.
Hasna tace"Hajiyace tace nazo in tafi da Indo.
Kafin Haiydar yayi magana Falmi tace"ai daman na fad'a bakinku d'aya gashi nan.
"Yauko ba wanda ya isa ya fita da Indo a gidan nan.
"Tunda ni na kawota a k'ark'ashina take.
"Kuma dalilina kuka santa, dan haka ba wanda ya isa ya fita da ita.
Haiydar yace"kinyi k'arya mahaifiya ta ke son ganinta dole taje ta.
"Don na san darajanta.
"Hasna zo ki mata magana ku fita ina nan gurin.
Falmi ta gyara d'amaran skit d'inta, tace"inga mai fitan da ita yau?.
"Shege ka fasa, yau ko ni ko Indo.
"Wai dad'in abun ma shegiyace, a titi akayi cikinta yar kwararao ne.
Ran Haiydar sai tafasa yakeyi, don yatsani kalman cikin shrge ko yar shege.
Hasna tasaka Indo ta b'ud'e qofar d'akin, sai kuka takeyi sosai. Hasna tace"Aunty ki tattara duk wani abunda kike buk'ata, don in kin tafi bazaki dawoba. Indo bata iya tanka mata ba sai kukan da takeyi, Hasna ce ta taimaka mata suka had'a kayanta, a yar madai-daiciyar  trolley d'inta suka jawo zuwa falo.
Indo ko sai kuka takeyi, kalo d'aya Haiydar ya mata yaji ta bashi tausayi, yaune rana ta farko da Haiydar ya fara tausaya mata, Falmi tana ganin sun fito tayi kansu, cikin zafin nama Haiydar ya samata k'afa ta fad'i, kanta yayi ya mata kyakyawan runguma, yanda bazata iya kwaceba. Hasna su ganin haka suka fita.
Haiydar sunsha rigima da Falmi sosai, don daga k'arshe kuleta yayi a d'aki ya fita abunsa.
Hajiya kaya na dai-dai misali suka had'ama Indo na lefe, a kwati hud'u da kit, sai kuma Falmi sun mata biyu da kit itama.
Hajiya damtse ta zage gurin gyara Indo, Haiydar ko abun duniya ya ishesa, don sam bai son wannan aure. Shiyasa ma ko ya fad'a ma wani yayi shiru, Hajiya ko ganin haka tasaka a ka kira mata abokinsa, Sadiq ta sanar masa, tace"ya kuma shirya duk wani abumda ake buk'ata, zata bada kud'in.
Yau ya kai kayan fad'an kishiya suka nufi gidan Falmi, da Sallamansu suka shiga.
Hajiya Firdausi da ke kitsa ma Falmi makirci, ta amsa musu, cike da mamaki suke kalonsu, Aunty Rahma ce tace"daman kayan fad'an kishiya muka kawo muku.
Falmi ta zabura ta mike tace"kayan fad'an me?.
Aunty Rahma tace"kayan fadar kishiya ko bakiji bane?.
Hajiya ta mik'e tace"ke kale mu daga sama har k'asa waye matsiyaci.
"Mai zamuyi da wannan d'an tsiyakon kayanku?.
Falmi ta mik'e tare da d'eban kayan ta fara watsa ma su Aunty Rahma.

Masu karatu kumin afuwa na rashin jina yau, ina busy ne amma in Allah ya yarda, zan tak'aita labarin nan mugama kafin azumi. Sabida wasu na min message, da qorafin a gama kafin azumi, zanyi iya yina inga na k'arasa,  In Allah ya so hakan.
Khaleesat Haiydar Novel facebook, ina mik'a godiyata mai tarin yawa, comments d'inku, shi yake k'ara bani k'arfin gwiwa.
Whatsapp members kuma ban manta kuba nagode dayawa, Allah ya bar zumunci Ameen.

                DEDICATED TO
           AISHA MUHAMMAD
     (MAMAN ABDUL SHAKUR)

          RASH KARDAM��

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts