[7/10/2016]Rash Kardam
BABBAN KUSKEREN
DANA TAFKA
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
*®NWA.*
Pg-190~193.
Cikin tsiwa Aishat ta ce"Allah ya sauwake, wace zata had'a jiki da kai?. Wai ko ka manta Aishat 'Yar aiki ne? Kuma ba'kar mace, wanda bata waye ba, marar ilimi. Mai zakayi da ni Indo?". Cikin zafin nama Haiydar ya riko hab'arta, ya ce"mai ki ka ce?". Aishat ko alamar tsoro babu a tare da ita, ta sake mai-maita abunda ta fad'a. Haiydar ya sassauta murya ya ce"Aishat always be the first to forgive the other person". Wani mugun kalo ta masa ta ce"oh! Yanzu ne kasan da haka? Ko ka manta irin tsa..... Bai bari ta k'arasa ba, ya toshe mata baki da hannusa. Aishat hannu tasa tare da zage iya k'arfinta ta turesa, sai da Haiydar ya d'anyi tangal-tangal kamar zai fad'i. Aishat tana kaiwa bakin k'ofar office d'in, ta juyo tare da rike k'ugu, ta ce"Haiydar ni Aishat ba tsaranka ba ce, a yanzu ne na dawo mutum? Kasani kwarya ta bi kwarya, kuma *DAI-DAI RUWA DAI-DAI GARI*. Ni Aishat Yar shege ce kuma bakace ni, sai kuma nayi sa'a baka son ba'kar mace, to mai za kayi dani?. Haiydar duk ya rasa inda zai sa kansa, hannusa ya had'a biyu alamar hakuri. Aishat ta aika masa da harara ta ce" Aliyu kake da suna ko? To ka sani wutsiyar rakumi tai nesa da kasa, da ga yau sai yau, karka kara shiga sabgata, kayi hanyarka nayi tawa mtsss". Ta saki tsaki ta fita abunta ko ta wai-wayesa. Haiydar dafe k'irjinsa yayi, don zuciyarsa wani irin zogi take masa, kujera ya nima ya zauna, ya lumshe ido, a haka Abokinsa yazo ya samesa, fuska yayi ya b'oye damuwarsa, sallama yayi ma Abokinsa tare da masa godiya ya fito ya bar makarantan. Aishat ta na shiga class da Sadeey suka fara karo, Sadeey ta ce"ya dai lafiya? Mai ya sameki?". Aishat batace komai ba, Sanah ce ta shigo class d'in, da sauri ta k'araso gurinsu ta ce"Aishat lafiya kuwa yanzu naga Haiydar zai shiga motarsa a school d'in nan? Ko dai shi ya aika a kiraki?". Aishat taso ta b'oye musu amma jin Sanah taga Haiydar, kawai ta sanar musu komai. Sanah ta ce"Aishat ba wai ina had'a ki da mijinki ba, gaskiya karki kuskura ki basa fuska, yanda ya wulakanta ki, ya kamata ki rama kema, ki basa wahala har sai ya gane kurensa, don baiyi nadama ba tukun da sauransa". Sadeey ta ce"gaskiya kam". Haka sukayita hira har lokacin tashi yayi suka fito. Haiydar ko da kyar ya iya jan motar ya koma gida, don ko ya koma office ba zai iya aikata komai ba. 'Daki yaje ya kwanta tunani yake kala-kala, cikin zuciyarsa ko cewa ya ke"ya zanyi da k'aunar Aishat da ke baraza ga rayuwa ta? Duk wanda yayi yunkurin rabani da Aishat, to tabbas na san baya k'aunata, barema in Allah ya yarda ba abunda zai sa na saketa, ko da zatayi ta gallaza min a haka". Aishat ko tana tashi daga makaranta gidan Hajiya ta wuce, a gun ta yini, sai yamma ta koma gidanta, ta na zuwa d'akinta ta shiga, wanka tayi kafin ta fito, kitchen tashiga ta girka kuskus da miyan stew, falo ta fito ta zauna tana cin abinci, Haiydar ya d'an kwaso yun warsa ya ga Aishat tana cin abinci, cike da isa ya ce"ke tashi ki zubo min nawa". Banza tayi dashi kamar bata jishi ba, ganin bata da niyar tashi, ya ce"in fa bazaki zubo min ba, to zan kwace naki". Nan ma bata ce masa ba, ganin haka yayi kanta zai kwace abinci da gudu ta mike ya bi bayanta. Dai-dai lokacin Falmi ta sanyo k'afarta cikin falon, dai-dai lokacin kuma Aishat ta iso gabanta, turus suka tsaya dukkansu a gabanta cike da tsoro a fuskansu, jakan da ke hannuta ne ya fad'i a kasa, ba k'arami gir-giza tayi da ganin su haka ba.
*®NWA*
*DEDICATED TO*
*AISHAT MUHAMMAD*
*(MAMAN ABDUL SHAKUR)*
*RASH LUV*
0 comments:
Post a Comment