New Post

Wednesday, 16 August 2017

BABBAN KUSKURE.... 156-163

����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

Pg-156~160.

Ba yan gama wanan shagalin, Falmi ita da tawaganta suka koma gidanta. Yayin da Hajiyansu Haiydar ta kira Amarya d'akinta, ta bata wani abu a cofi tasha. Hajiya tace"ki k'wanta ki huta sosai. Sai da a kayi sallan magriba Hajiya tasa ta gaba taci abinci mai yawa. Hajiya ta saka ruwa a murhu, tare da lalle da magarya ya dahu sosai, sanna tasaka ruwa daban wanda ba komai aciki, ta juye farin ruwan a bokiti ta surka ta kai bayi. Kafin ta d'au wani bokitin ta tace ruwan lallen nan, da rariyan ta, sannan ta d'auko madaran turaruka kala-kala tasaka mata madaran turaren wanka acikin ruwan lallen. (Shi ruwan lallen ba'a cika ruwa da yawa sosai, d'an dai-dai za'a saka). Ta kai bayi tace"Aisha tashi kiyi wanka zaki ga ruwan biyu ne, kiyi wankan sabulu da farin, ki tabbatar ki dirje ko ina. Bayan kingama wankan sabulu, sai ki d'auki ruwan lallen nan zakiga ba yawa, ki tabbatar kin game jikinki dashi ta ko'ian.
Aisha Indo ta amsa da"to Hajiya nagode. Saukowa tayi tashiga bayi, wanka sosai tayi kafin ta yiwankan lallennan. Tun daga bayi k'amshi ke tashi har falo.
Hajiya ta taho da kasko k'arami, Indo na fitowa tace"zo nan.
Fallen zani ta bata, ta lulub'u dashi kafin ta samata kasko tare da zuba turarukan wuta aciki masu kamshi.(masu k'aratu amfanin wannan wankan lallen, da turare yana saka jikin mutun yayi k'amshi, sannan k'amshin yana kama jiki, yana sa mutum kara haske da kyau. Sannan a zuba turare aciki zaki ringa kamshi ne sosai. Idan mutum ya fito daga wanka, bazai bari jikinsa ya tsan-tsame ba. Da ruwan zaki saka turaren wuta a kasko ki luluba jikinki, sannan ki tabbatar kamshin turaren na bin jikinki, in turaren ya k'are ki k'ara sakawa har sai kin tsan-tsame.zakiji k'amshin ya kama jikinki).
Hajiya ta d'auko atamfa riga da zani, acikin a kayan Indo ta d'auko kwalban turare yar mai duguri, ta juje akan kayan, hatta ina wears d'inta saida suka sha turare masu sanyin kamshi, wanda duk namiji lafiyaye in ya shaki kamshi, sai ya yaba. Hasna ne ta turo qofa tashigo, ita ta tsara ma Indo kwaliya, kafin tasaka kayan. Masu k'aratu tundaga haraban  gidan zaku iya jiyo kamshin da indo takeyi.
Waya hajiya ta d'auko lokacin tara da rabi, Haiydar takira tace"kazo yanzu ina son ganinka.
Cikin girmamawa yace"to Hajiya gani zuwa.
Bai dad'e ba ko sai gashi, cikin shaddarsa ja sai maik'o takeyi. Ko da yazo Main falo, bak'ine aciki sai tsokanarsa sukeyi, murmushi ya musu ya nufi cikin d'akin Hajiya. Qofar tura tare da yin  sallama. Tsayawa yayi cak dan ganin Indo a bakin madubi tana saka sarka. Sam ya kasa d'auke kansa daga gareta, ji yake kamar yaje ya rungumeta, amma jinkai da girman kai bazai barshi ba. Wata zuciya tace"to mai zakayi da bak'ar mace ma.
Wata zuciyar ko cewa take"ai kuma duk randa tayi gayu sai ta fi falmi kyau.
"Mtss  kai k'aryane, yama za'ayi tafi Falmi kyau. Yana wannan tunani Hajiya tashigo da sallama tace"yauwa Babana ka iso.
Sosa keya ya fara tare da rusunawa ya gaidata, Hajiya ta zauna abakin gado, Haiydar ya zauna akan dadduman dake kasan d'akin. Hajiya tace"Aisha zo nan.
Cikin nutsuwa Indo ta tako zuwa kusa da k'afar Hajiya ta zauna.
Hajiya tayi gyaran murya, tare da fara musu nasiha mai shiga jiki. Harda yan ayoyinta takawo musu, wanda yake nuni hakkin miji akan matarsa, tare da hakkin mata akan miji. Bayan ta gama tace"Aliyu!". Kansa asunkuye yace"na'am Hajiya.
Taci gaba da cewa"ga *AMANA* Aisha na baka, ban yarda matarka ta takura mata ba.
"Itama matarka ce kamar yarda Fatima take matsayin matarka. Ko da tagama musu nasiha ta sanya musu Albarka tare da cewa Indo d'auko gyalenki. Hajiya ta d'auko Hijab tace"tashi muje da kaina zan kaiki d'akinki. Hannuta hajiya ta riko suka fito falo, sai tsokanar su akeyi.
Haiydar shi ya jasu har zuwa gidansa, ko da suka shiga duk yan biki sun watse sai Falmi da taci riga da wando, tayi shirin ko ta kwana, don yau a shirye take da in dakuwa ne ma suyi a gidan. Ganim Hajiya yasa ta rusuna,, bata ko gaida ta ba sai wani hararan da ta aika musu.
Hajiya ta shigar da Indo d'akinta kafin ta fito Haiydar yazo ya rakata yace"zai maidata gida. Hajiya tace"a'a na yafe driver ya maida ni. Sai da suka bar gidan, sannan ya nufi gida.
Yana shiga Falmi ta ja ta tsaya a dai-dai qofar shiga side d'in Indo. Dake shi ba ma niyayar sa shiga gun bane ko kalonta baiyiba yanufi side d'insa. A dai-dai bakin qofarsa ta kwanta, wai dan karyazo ya wuce d'akin Indo bata sani ba, a haka har bacci ya d'auketa.
Haiydar ko yana shiga d'aki kayansa ya cire ya watsa ruwa, ya sanya kayan bacci ya kwanta. Ko da ya rufe idonsa photon suran Indo ke masa yawo a idonsa. Da duk al'amuran dasuka faru a tsakaninsu. Sai juyi yakeyi gashi duk yana hannu, amma yasan in ya tink'ari Falmi, bala'i zai ne mo ma kansa haka yayita juyi har bacci b'arawo ya d'aukesa.

                *DEDICATED TO*
          *AISHA MUHAMMAD*
     *(MAMAN ABDUL SHAKUR)*

                   *RASH KARDAM��*
[7/5/2016] Rash Kardam ����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

Pg-161~163.

Gari na wayewa Falmi ta tura d'akin tasamu Indo tana bacci. A fili tace"eyeh lalle fa kin samu kanki acikin bak'ak'en labarawa.
"Har wani lokacin bacci kika samu.
"Lalle ko zanyi maganinki yanzunan. Cikin hanzari ta juya zuwa kitchen d'inta, ruwa mai sanyi ta d'auko a fridge, in kunga ruwan har wani tururi yakeyi na sanyi. Tana zuwa tasamu har yanzu Indo bata farka ba, cikin zafin nama cike da masifa Falmi ta shek'a mata ruwan sanyi a jiki. Cikin razana indo ta farka, sai wuk'i-wuk'i take da ido.
Falmi tace"ke waya baki damar yin bacci a gidan nan ko kin manta matsayinki ne.
"Na yar shege kuma yar aiki maras amfani ke da babu duk d'aya kuke a gidan nan.
"Maza sauk'o ki had'a mana breakfast. Indo ji take kamar ta kurma ihu, ba wai watsa mata ruwa, da masifan da Falmi ke ta mata bane ya dameta ba, ila cemata da tayi yar shege, wannan maganan ya na k'ona mata zuciya. In dai zagi ne kam inda sabo ya kamata tasaba. Tsawa Falmi ta sake mata wanda yasata dirk'owa daga kan gado, da sauri ta nufi hanyan falo.
Kitchen d'in dake baban falo ta shiga ta had'a musu breakfast, sai da ta jera komai kafin ta d'ibi na ta, cikin d'akinta ta koma, tayi wanka tare da yin brush kafin ta karya.
Hajiya sai da tabari Indo tayi 3 days tasaka driver ya kaimata ak'watunanta.
Rayuwan Indo ya canza a gidan ba'abinda ta ke fuskanta ila tsangwama da tsana daga gun Falmi da Haiydar. Tun da ta fahimci duk ranar da sukayi karo da Haiydar sai ta gane kurenta. Hakan yasa indai taji yana falo to bata fitowa sai ya fita.
Kwanaki sun tafi yau ki manin 2 month da yin bikinsu.
Hajiya ce ta had'a goma na arziki tasaka Hasna ta zo duba lafiyar d'iyarta Indo.  Hasna tana zuwa ta wuce d'akin Indo tasamu tayi tagumi. Ta rame ga wani bak'in da ta k'ara, cikin hanzari hasna ta yar da jakanta, taje tace"Aunty na mai ya sameki haka?.
"Kinyi rashin lafiya ne?.
Cikin dauriya Indo ta k'ak'alo murmushi tace"lau na d'anyi zazab'ine amma na warke yanzu.
Sam Hasna bata gamsu da maganarta ba, suna cikin haka, sai ga Falmi ta shigo tana kiran Indo harda ashar d'inta.
Sam bata san da zuwan Hasna ba kasancewar daga yawonta ta fito. Hasna ne tace"kar ki amsa wannan kiran yan tashan.
Falmi jin Indo bata amsa ba tasan kuma tana jinta, abun sai ya kular da ita. Har zata tura qofar ta fasa ta koma d'akinta, zuk'ek'iyar bulala ta d'auko, ganin jikin bulalan yasata sakin wani murmushi, don tasan wannan bulalan in har yashiga jikin Indo zata gane shayi ruwa ne. Cike da isa da gadara, tana wani wawwaina bulalan a hannuta. Ta iso falon Indo, Kiran yantasha ta sakeyi.
Hasna kuwa ta hanna Indo amsawa harda tushe ma Indo baki. Falmi a harzuke tashigo falon, sam bata lura da Hasna ba tayi kan Indo da bulala. Cikin sa'a ta tsula mata na d'aya, ta kai na biyu kenan Hasna tayi saurin shiga tsakaninsu. Falmi ganin Hasna ta razana amma sai ta dake tace"kee bani guri inyi abunda nayi niya.
Hasna tace"ke Fatima kike kowa, kar ki kuskura tsautsayi ya gifta miki kice zaki sake dukan Indo.
Falmi cikin fushi tace"ke ce mai tare mata ko.
Cike da gadara Hasna tace"eh da abunda zakiyi ne..
Tsautsayi yasa Falmi ta d'aga bulala wai zata zuba ma Hasna. Amma kash ina ae ta makara Hasna tayi saurin k'wace bulalan tashiga tsula ma Falmi, iya karfinta, Kan kuce mai ta cika gida da ihu.
Sai da Hasna ta mata lilis sai ihu take, karar motan Haiydar ne ya dawo gida, hakan baisa Hasna ta daina ba, Haiydar jin ihun Falmi ko mota bai rufe ba ya shigo gidan da gudunsa.
Falon Indo yaji muryanta cike da mamaki yayi side d'in da gudu.

Masu karatu bari mu huta a nan, ina muku murna da zagowan k'aramar sallah. Allah ya amsa mana ibadun mu ya kumasa muna daga cikin wa'yanda aka 'yanta daga wuta zuwa aljannah ameen.
  *HAPPY SALLAH IN ADVANCE*

                  *DEDICATED TO*
            *AISHA MUHAMMAD*
      *(MAMAN ABDUL SHAKUR)*

                 *RASH KARDAM��*

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts