[7/9/2016] Rash Kardam
BABBAN KUSKEREN
DANA TAFKA
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
*®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*.
Pg-187~189.
K'ofa ta ru fe, ta ju ya za ta hau kan gado ke nan, ta ga mutum a kwan ce, ba k'aramin razana ta yi ba, ci kin sauri ta ju ya za ta fita, Haiydar ya yi saurin dirowa da ga kan gado, ya kai ma ta cafka, amma kash! Ka fin ya iso, cikin za fin na ma ta fita. 'Dakin da ke kusa da na ta, ta shi ga, key da ke ji kin k'ofar ta murd'e, cikin sa'a ya kullu. Haiydar ya na zu wa, ya sa mu har ta sa key, ya tsa ya ci za, sam bai so ha ka ba, d'akin ta ya ko ma ya kwan ta. Rigan baccin ta ya ga ni, hannu ya sa ka ya d'auko, kan hancin sa ya kai, ya na shin-shinan dadda d'an kamshin da ke jikin rigan. A haka har bacci b'arawo ya d'au ke sa. Aishat ko duk illahirin jikinta rawa ya ke yi, sai da ta kusa awa d'aya, ta zauna a bakin gadon, sai da ta yi addu'a kafin ta kwanta. Asuban fari ta mik'e tayi sallah, sai da ta ji Haiydar ya fita, kafin ta lallab'a ta koma d'akinta ta kulle. Wanka ta shi ga sai da ta ga ma ta fito, sama-sama ta shirya, uniform ta sa ka, ta d'au bag d'in ta, ko karyawa ba ta tsaya yi ba, ta fito bakin gate, Napep ta tare sai gidan Hajiya, da sallama ta tura k'ofar falon ta shi ga, da Hasna su ka fara karo, ci ke da mamaki Hasna ta ce"lafiya dai na gan ki da sassafe nan?. Murmushi Aishat ta yi ta ce"lafiya lau wallahi, yau sauri na ke yi shi ya sa ko ka yan breakfast, ban tsaya had'a wa ba". Hasna ta ce" ina Bros d'ina fa?". Aishat ta ce"ke barni yau ina sauri ne, yi ki had'a ma na breakfast ka wai, Hasna Hajiya fa? Tana ciki ne?". Hasna ta ce"eh! Ta na d'aki". "Okay! Barin shi ga gun ta, na gaida ta". Da d'an gudunta ta haura step d'in, da sallama ta shiga d'akin Hajiya, ta samu tana karatu, a gefenta ta zauna, sai da Hajiya ta idar da karatun, Aishat ta ce"Hajiya an ta shi lafiya?". Hajiya ta ce"lafiya lau, ya karatu?". Aishat ta ce"Alhamdulilah! Mu na kai". Hajiya ta ce" ya Haiydar d'in? Ina fatan ba ku na zaman lafiya, bai ta ku ra mi ki?". Aishat ta ce"lafiya mu ke zaune ba wata matsala". Hajiya ta ce"Alhamdulilah!". Aishat ta ce" barinje na karya don zan wuce school daga nan". Hajiya ta ce"to in kin gama karyawan ki min magana". Aishat ta amsa mata tare da fita falo. Ita da Hasna su ka karasa aikin, su na hira har Aishat ta karya, lokacin Hajiya ta sauko, kud'i ta mika ma Aishat ta ce"ga shi ki rik'e ki na b'atarwa". Aishat ta yi godiya ta fita. Driver ne ya kaita makaranta.
Haiydar na dawowa da ga masallaci, ya ko ma side d'in Aishat ya na tura k'ofan d'akin da tashiga, sai ganin k'ofar ya bud'u, sa kai ya yi cikin d'akin amma me?. Sai ganin d'akin empty bakowa, d'akinta ya sa ke zu wa shi ma k'ofar a bud'e, sai ya d'auka ko wanka tashiga, kan gadon ta ya sa ke kwanciya, ya na za man jiran fitowarta. Shiru-shiru ba bai ji Aishat ta fito ba, bare ya ji karan ruwan wanka, tashi ya yi ya nufi bayin, k'ofar bayin ya tura, nan ma ya ga empty bakowa a ciki, tsoro ne ya kama Haiydar to ina Aishat ta je?. Ko dai ta na kitchen ne?. Da sauri ya yi hanyar kitchen, ko da ya je nan ma ba kowa. Ba karamin razana ya yi ba, ga shi time d'in fitar sa aiki ya yi, da sauri ya koma d'akinsa ko wanka bai tsaya yi ba, ya saka kaya, ya fito mota ya d'auka ya nufi gidan Hajiya, Ko da ya shiga a falo ya sa me su a falo, ya rusuna ya gaida Hajiya, Hasna ma ta gaida shi, Hasna ta sa ma sa abinci, sam kasa cin abincin ya yi, hankalinsa ya tashi, tunani ya ke, kardai ace Aishat ta gudu ne?. Tabbas da ya yi hauka, don yanda ya ke jin sonta a cikin zuciyarsa ba zai iya hakuri da rashinta ba, mikewa ya yi, ya mu su sallama ya nufi gun aiki. Ko da ya shiga office, bai iya tab'uka komai ba, key d'in motarsa ya dauka, ya nufi hanyan makarantarsu Aishat, ya na zuwa, bai wani samu matsala da mai gadi ba, don kakin police ne ajinsa. Ya na shiga harabar makarantar, ya ga mu da abokinsa Malami ne a makarantar, suna zuwa office ya masa bayanin Aishat Malamin ya ce"oh! Head girl ka ke fad'a?". Haiydar ya ce" eh ita ce". Malamin ya aika aka kirata, bata dad'e ba ta zo. Malamin ya basu guri a office d'in, Aishat wani mugun kalo ta masa, ta ce"lafiya Malam mai ya kawoka makarantar mu?. Miye alakarka da 'Yar aiki, kuma 'Yar shege?. Haiydar ba na son ganinka, i hate you". Nan ta ke ya ji zuciyarsa na tafarfasa, don jin kalamanta ya ke, har cikin kwakwalwan kansa, cikin tsawa ya ce"ya isa haka!, Aishat mai ya sa bakya tausayina ne?. Aishat in kinji yanda zuciyata ke bugawa a kan k'aunarki. Please ki taimaka ma rayuwata, ki yi kahuri da abunda ya faru, ki manta komai dan Allah!". Wani kalon banza ta sama nai nuna alamar baka da wayo, juyawa tayi za ta fita, cikin hanzari ya sha gabanta, matsawa ta soma yi, shima ya na binta, cikin dakiyar zuciya tace"wai lafiyanka kuwa? Wannan wani irin iskanci ne haka?". Haiydar ya yi wa ni murmushi, ya ce"Aishat ko kin manta matsayina a gunki? Ni fa mijinki ne na sunnah, kuma ina son inji d'umin jikin matana a tare da ni". Cikin tsiwa Aishat ta ce"Allah ya sauwake wa ye za ta had'a jiki da kai? Wai ko ka manta Aishat 'yar aiki ce? Cikin zafin na ma Haiydar ya matso kusa da ita, hab'arta ya kamo.
Kuyi hakuri da wanna ba yawa, yau ina bussy ne.
*®NWA*
*DEDICATED TO*
*AISHA MUHAMMAD*
*(MAMAN ABDUL SHAKUR)*
*RASH KARDAM*
0 comments:
Post a Comment