Rash Kardam
BABBAN KUSKEREN
DANA TAFKA
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
*®NWA.*
*Pg-225~226.*
Ba kowa bane ya turo k'ofar illa Muhammad Lamid'o d'a d'aya tilo Namiji kuma magaji ga Sarkin Fulani Gombe cikin razana da firgici Hajiya k'arama ta mik'e don ba k'aramin kid'ima tayi da ganin sa ba nan take taji wani fitsari na shirin zubo mata sai zazzare ido takeyi jikinta sai b'ari ya farayi Sarkin Fulani da kansa ya taka ya je ya rik'o hannu Lamid'o yana hawaye bai san lokacin da ya rungume sa ba farin ciki ba'a cewa komai baran Aishat da ganin fuskan sa ba tam-tama ta gane Mahaifinta ne don yawan kalon sa da takeyi a hoto, Sarkin Fulani ya kamo hannu sa ya zaunar da shi Hajiya ma kukan murna takeyi ikon Allah kenan, sai da suka zauna Sarkin Fulani ya ce"Lamid'o kaine?". Lamid'o ya ce"eh nine Abba". Sarkin Fulani ya furta ikon Allah kenan ya wuci wasa". Ya kalli Hajiyan su Haiydar ya ce"kije d'akina ki had'a masa ruwan wanka tukun ya ci abinci don naga da gajiya a tattare da shi ga alamar yunwa". Haka ko akayi nan take ta kaisa d'akin Babansu ta dawo kitchen da ita da su Aishat suka had'a masa girki mai k'ayatarwa, yana fitowa a wanka ya tarar da sabbin kayan da aka ajiye masa ya sanya ya gyara jikinsa, falo ya fito ya tarar da su, sai a lokacin idonsa ya kai kan Aishat da ta k'ura masa ido shima kallonta ya farayi cikin zuciyar sa ya ce" wannan tamkar Safinatun sa, ayya ko dai ita ce yar cikin Safinatu da taho da shi?". Hannusa yaji an rike ko da ya duba Sarkin Fulani ne ya kama hannusa duka suka nufi dining, Hajiya da kanta ta sanya ma kowa abinci ta zauna Sarkin Fulani yana mak'ale da Lamid'on sa sai Hajiya da ke kusa dashi sai Aishat a kusa da Hajiya yayin da Haiydar ke kusada Lamid'o sai Hasna a kusa dashi. Haiydar yana kallon Aishat yana aika mata da wasu sak'on ninsa, gun shiru kowa yana fama da abinci fiskan kowanne su yana d'auke da murmushi don suna cikin farin ciki bana wasa ba.
Haiydar ne ya mik'ar da k'afan sa ta k'asan dining table d'in yanda zai na tab'a k'afar Aishat babban yatsan k'afarsa ya sanya a tafin k'afar Aishat ya fara mata tafiyan tsutsa a take taji wani yarrr! saurin d'ago fiskan ta tayi karaf su ka had'a ido wani lalalusar murmushi ya sakar mata ya kashe mata ido d'aya. Sai da ta d'an saci kalon su Hajiya taga kowa na ta kai da abincin sa ta murgud'a masa baki, Haiydar yayi murmushi ya sake sosa mata k'afa harda wuce wansa zuwa sawun k'afar ta da sauri ta kau da k'afar asai Hajiya tana lura dasu ta share ne kuma taji dad'in hakan suna kammala cin abinci suka koma babban falo suka zazzauna. Sarkin Fulani ya kalli Hajiya ya ce"wai ina Hajiya k'arama ne banganta ba har a gurin cin abinci kuma yanzu ma bata fito ba ko lafiya?". Hajiya ta ce"ina ga lafiya zata fito". Sarkin Fulani ya kalli Lamid'o ya ce" zaka iya gane wannan fuska kuma da wa ta ke maka kama?". Lamid'o ya kalli Aisha sosai ya ce"tun shogowata fuskanta ke min kama da fiskan Matata Safinatu". Sarkin Fulani ya murmusa ya ce"tabbas wannan d'iyarka ce da Safinatu". nan suka kwashe labarin komai suka fad'a masa sosai Lamid'o yayi kuka ya tausaya wa Matarsa da 'Yar sa tare da mik'o hannu ma Aishat tazo yana kuka ya rungumi d'iyarsa take Aisha taji sanyi dad'i na ratsa ta wai yau ita ce take tare da Mahaifin ta daman ita ba 'Yar shege bane da ake kiranta, zanso Falmi taga gatana taga Mahaifina asai mu 'Yan uwa ne da Haiydar nan tasaki sassanyan Ajiyar zuciya, Sarkin Fulani ya ce"zan so kabamu labarin bayan barin ka Gombe yanda al'amura suka kasance". Lami'o ya nisa tare da gyara zama ya ce"bayan da muka shiga mota munyi nisa sai da muk'a k'usa shiga Alkaleri Idi driver ya tsaya", ya ce" Lamid'o bazanso na kashe ka da hannuna ba don an bani kwangilan kasheka ne Hajiya k'arama amma sabida kirkin Hajiya babba bazan ci *AMANAN* ta ba ta rik'e mu da gaskiya" Lamid'o ya ci gaba da cebwa"kafin nayi wani magana kawai ya shafamin wani abu a hanci na tun daga lokacin ban san inda kaina yake ba sai a cikin wasu kauyukan Yola na samu kai na tare da wani mutumi wanda aka had'a ni dashi dan ya baro bauchi dani gudun kar Hajiya k'arama ta ganni, mutumin nan sai da ya tabbatar da na dawo cikin hayyacina shima ya zame ya barni, a tasha kauyen ribad'o na zauna nan yunwa ya fara damuna daga nan na fara aikin k'arfi ina kula da kaina kuma na samu wani Bafulatani mukayi dashi zanna tayasa kiyo yana biya na haka muka fara randa ba kiwo inje niman kud'ina da haka har na tara kud'ad'e na sai na sayi saniya ta mace nan muka fara kiwo cikin ikon Allah ya sanya ma saniyar nan albarka tayi ta haihuwa kuma inayi niman kud'ina na sai na sai wasu da haka Allah ya azurtani da garken shanu na kuma yi suna a cikin kauyukan da ke yanki don ba mai shanuna a haka har Allah yayi na auri Matana Safinatu muna zaman lafiyan mu wasu daga cikun yan kauyen suka fara adawa da dukiyata hakan yasa suke min barazanan kisa, a haka wasu daga cikin ranar laraba da bazan manta ba suka fara bina suna neman kashe ni cikin hanzari na taho gida na umurci matata da tazo mu gudu.
*®NWA*
*DEDICATED TO*
*AISHA MUHAMMAD*
*(MAMAN ABDUL SHAKUR)*
*RASH KARDAM*
0 comments:
Post a Comment