[8:05PM, 7/16/2016
BABBAN KUSKEREN
DANA TAFKA
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
*®NWA.*
*Pg-214~216.*
Dai-dai lokacin sauran police d'in suka iso, bai bi ta kansu ba da gudu yayi mota da ita ya sanya ta a mota ya juyo ya ce"ku tabbatar da kunbi mutanenan kuma kun kamosu zan turo wasu motocin su biku". Bai jira amsansu ba ya juya ya shiga mota ya figeta da gudu ya nufi cikin gari. Gudu yakeyi sam ba nutsuwa a jikinsa wani wawan duka ya kaima sitiyari motar tare da furzar da wani isaka mai zafi zuciyarsa na masa rad'ad'i wai ace abunda yagama tanadi wani ya rigasa wasu zafafan hawayene suka zubo masa wata b'an gare na zuciyarsa ya ce"haba Haiydar duk da abin da ciwo kardai kace zaka guje ma Aishat don son da ka ke mata na gaskiya ne bawai jikinta kake so ba. A fili ya furta" Aishat a kowani hali ki ke ina k'aunarki ke ce SIRRI NA bazan gujeki ba". Wasu hawaye ne suka sake zubo masa, wayarsa ce tayi k'ara sunan Hajiya ya gano ya d'aga cikin muryan kuka ya ce"Hajiya an sameta amma sun mata fyad'e gata ko motsi batayi". Hannu a ka Hajiya ta d'aura ta saki salati ta ce"yanzu kuna ina ne Aliyu?". Ya ce"gani a hanya da ita zan wuce T.H". Hajiya ta ce"okay gamu zuwa da Abban ka yanzu shima ya dawo". Kashe wayar yayi ya k'ara gudu wanda kiris ya rage motar ta kwace a hannusa Allah ne ya kare. Bai dad'e ba ya isa Asibiti take a ka shiga da ita Emergency Haiydar ya gagara tsaye ya gagara zaune sai safa-da-marwa ya keyi a k'ofar idonsa na zubar da hawaye, Hajiya ne da Abba suka iso kalonsu kawai yayi ya fashe da kuka mai cin rai, Hajiya ma hawaye tafara don abun ya mata ciwo bana wasa ba.
Falmi ko gidansu ta nufa ita da Mum d'inta suka tafi gun boka ita duk a zatonta an gama da Indo dan haka ta ce"boka kaban maginda sai abunda na fad'a ma Haiydar zai yi ba kuma zai ki bin umarni na ba". Bokan ya bushe da wata mahaukaciyar dariya ya ce"anyi angama yarinya kinzo inda za'a share miki kukan ki hahahah". Kwarya ya d'aga sama saiga wasu magun-guna sun zuba a ciki nan ya mik'a mata ya ce"ga wannan turaren ki tabbatar kulum kinshafa a jikinki, sannan wannan maganin ki kuskure bakinki da shi kulum". Falmi cikin zud'i ta ce"anyi an gama boka". Bokan ya kara wata dariya kafin ya ce"maganin mu da doka kisani duk randa kika tsallake d'aya aciki asiri zai karye kuma zai miki wulakanci mummuna". Ta ce"zan kiyaye boka". Kud'i ta zuba masa suka tafi.
A can asibiti kuwa Dr ya bata taimakon gaggawa saida numfashinta ya dai-daita kafin suka duba kasanta asai ba fyad'e a ka mata ba kukkurjewa tayi acinya wanda ya janyo mata zuban jini. To ni Rash abun ya d'auremin kai bare masu karatu, amma bari mu wai-wayi baya, in baku manta ba na ce muku"ciwon da Aishat taji ya haddasa mata zuban jini sosai wanda haryasa idonta yin wani iri". Bayan da 'Yan iskan nan suka cigaba da tafiya da ita jininta ya zuba ga razana da tayi hakan ya sanya ta yanki jiki ta fad'i tayi dogon suma idanunta sun kafe, 'Yan iskan nan da suka ga haka sun d'auka mutuwa tayi, shiyasa Ogansu ya ce"kawai su yarda ita anan tunda ta mutu ba amfanin su fita da gawa karma a kamasu". Tundaga bakin hanyar da zai shigarda mutum dajin da aka sameta suke janta a kasa wanda yasa skirt d'inta kwayewa jikinta ya jijiciwo kunji dalilin zuban jinin bari mu koma labari. Ko da Dr ya gama dubata ya gito cikin hanzari Haiydar da Hajiya sukayi gunya a tare suka jefo masa tambaya "Dr ya jikinta?" Dr ya ce"da sauki Alhamdulilah kuma ba fyad'e aka mata ba kurjewa tayi, ga jini ya zuba da yawa don haka muna buk'atar jini cikin sauri Haiydar ya ce" Dr muje a d'ibi nawa a samata". Cikin ikon Allah jininsu yayi dai-dai aka samata Dr ya ce"ya kamata a canza mata kayan jikinta sun b'aci". Haiydar ya amsa da "to". Ya kalisu Hajiya ya ce"barinje gida na d'auko mata wasu kayan". Hajiya ta kalli agogo wayanta karfe biyu da rabi ta ce"to kaje Allah ya kareka". Ya amsa da "Ameen". Ya fita gudu yaringa shararawa har ya iso gida horn ya ringa yi Falmi cikin bacci taji horn d'in kafin da sauri ta leka taga Haiydar ne ke shigowa cikin sauri ta shafa turaren nan ta kuma shiga bayi ta kuskure bakinta da ruwan maganin ta nufi k'ofar falo.
*®NWA*
*DEDICATED TO*
*AISHAT MUHAMMAD*
*(MAMAN ABDUL SHAKUR)*
*RASH KARDAM*
0 comments:
Post a Comment