New Post

Wednesday, 16 August 2017

Babban Kuskure 81-95

����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

Pg-81~85.

Cikin hanzari ta soma sauk'owa daga step d'in, don ko makawa babu, wannan muryan Lamid'o ne. Jikinta har b'ari yakeyi, da sauri ta isa falon, sam su Indo basu san, hajiya ta isoba. Sabida karatun da ke tashi a falon, gashi hankalinsu gaba d'aya, yana kan hotuna. Hajiya ta dad'e tana kalon Indo, cikin zuciyarta ko cewa take, "tabbas wannan jinin Lamid'o ne.
"In kuma ba haka ba to kaman yayi kama.
"To tayama za'ayi ace jinin Lamid'o ne, bayan Lamid'o da'akace ya mutu, har anga tokan gawansa.
Jikinta duk ya mutu, da kyar ta iya jan kafarta, zuwa cikin falon tare da yin sallama. Indo a hankali ta d'ago kanta karaf suka had'a ido, take k'irjin Indo ya bada rass! Rass!, kasa d'auke fuskanta daga kan hajiya tayi.
Cikin zuciyarta ko cewa take"wannan kamar matan, dana ke gani a photo da Umma tace na Baba nane.
"Sai dai wannan ta tsufa wancan kum yarinya ne.
"Hmm to nida bayida yan uwa ma.
"Kai inaga kama ne, kawai sukayi da matar.
Ajiyar zuciya ta sauk'e a hankali, ta sunkuyar da kanta, cikin girmamawa tace"sannu Mama anyini lafiya?.
Hajiya da takasa b'oye mamakinta a fili, sai da Hasna tace"Hajiya ana gaidaki ne fa.
Firgit ta dawo daga duniyar tunanin da ta lula, cikin fara'a tace"lafiya Aishatu".
"Ya aikin dai?
Indo kanta a k'asa tace"Alhamdulilah!.
Can sukayi shiru, don Hajiya tana jin wani abu gameda Indo, ta dawo mata da abunda ya wuce, shekara ishirin da d'oriya. Cikin dauriya hajiya tace"Hasna taci abincin kuwa?.
Cike da girmamawa Hasna tace"eh hajiya.
Hajiya ta kali Indo tace"Aishatu nina aika ki zo keda Husna.
Kan Indo a k'asa tana wasa da yan yatsun hannuta, masu kyau gasu dogaye gwanin burgewa.
Hajiya taci gaba da cewa"Aisha ina son ki d'auken a matsayin Mahaifiyarki, kuma wacce zata baki umarni ki bi.
"Aishatu! Ta kira Indo, cikin girmamawa Indo ta d'ago, karaf suka gad'a ido, take taji wani qaunar Hajiya ya shiga jikinta, kuma ta hango tsananin soyayyan uwa da d'a acikin kwayar idon Hajiya.
Indo ta amsa da"Na'am Mama!.
Hajiya tace"Aisha ina rok'on wani alfarma a gunki, kuma ina so kimin alkawari. Zaki amince da duk abunda na fad'a miki.
Indo cikin sanyin murya tace"Mama ae ke uwace.
"Duk umurnin da kika ban zan kasance mai biyayya a gareki, matsawan bai sab'ama addini ba.
Hajiya tace"Alhamdulilah! Nagode Allah ya maki Abarka Aisha.
Indo ta amsa da"Ameen ya Allah.
Hajiya tacigaba da cewa"Aisha inason na had'a ki aure da d'ana Haiydar.
Cikin rud'ewa ta d'ago fiskanta, don ta gaskata mai kunneta ke jiyomata.

               DEDICATED TO
          AISHA MUHAMMAD
    (MAMAN ABDUL SHAKUR)

                ��RASH LUV✍��
[5/30/2016] Rash Kardam ����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

Pg-86~90.

Cikin rud'ewa ta d'ago fuskanta, tabbas Hajiya da gaske take maganan, hmm cikin zuciuarta kam cewa take"anya Hajiya tasan mugun tsanar da Haiydar yamin?.
"Taya ma zanyi na auri mijin Aunty Falmi.
"Ina bazan iya ba Hajiya ki canza. Tana wannan tunanine ta ji muryan Hajiya tana cewa"karki damu nasan tunaniki Fatima ce ko?.
"To ita da kanta ta zabi hakan.
"Kuma shi Haiydar d'in ma ya amince.
Indo sam gani take kamar ma farki abunke faruwa.
Hajiya tace" ina fatan bazakiyi min jayayaba.
Indo haka kurum ta tsinci kanta da d'aga ma Hajiya kai ta amince.
Hajiya albarka tayi ta sa mata, tukun ta mik'e tace"barin hau sama zan yi wani abu. Hasna ne ta amsa da"to Hajiya.
Hajiya na tafiya Indo ta fashe da kuka sosai, Hasna ta dawo kusa da ita tace"Aunty Aisha kiyi hak'uri nasan Hajiya bazata tab'a cutarki ba.
"Kuma wataran zakiyi alfahari da aurenku.
Indo cikin kuka tace"Hasna kin san yanda Yayanki ya tsaneni kuwa?.
"Sam baya k'aunar ganina ina numfashi.
"Bazan iya kishi da Auntyn Falmi ba Hasna.
Hasna tace"hak'uri zakiyi komai zai yi dai-dai.
"Kuma batun Ya Haiydar ke zaki ja ra'ayinsa da naki salon.
"Amma sai kin dage kin kuma daure.
"Tashi muje d'akina in miki make-up, don tare zaku koma in yazo.
"Zan kuma baki wasu kaya kina kwaliya sosai.
"Ki bar zama ba gayu pls.
Hannu ta takama suka haura sama, Hasna ta wanke ma Indo kanta ta gyara ta sosai kamar ba ita ba. Wasu sababin kayanta, da bata saba ta bama Indo, tare da had'a mata kayan kwaliya mai yawa.
Falmi ko ita da Haiydar kokuwa suka sha, da k'yar ya rabata da kayan jikinta, sarrafata yasomayi son ransa. Falmi ihu take masa tana cewa"tunda ka amince ma Hajiya sai kaje gun Indo ta baka kanta, banda ni Falmi, tana kuka tana dukansa. Shiko gogan bai masan tanayi ba, sha'aninsa kawai yakeyi. Falmi ta wahala kam, don taki tsayawa, sai da ya d'ibi 2 hours masu kyau, kafin ya koma gefe yana maida numfashi, a hankali ya matso kusa da ita, ya rungumota yace"Falmi ina matuk'ar sinki, amma ke kike jawomana duk abunda suke faruwa.
"Mai yasa kike guje ma shimfid'ata?.
"Ina kiraki bak'ya amsa min why Falmi?.
"Kuma kinsan ni na kasance mai yawan bukata Fatima.

               DEDICATED TO
           AISHA MUHAMMAD
       (MAMAN ABDUL SHAKIR)

              ��RASH LUV✍��
[5/30/2016] Rash Kardam ����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

Pg-91~95.

"Mtsss Falmi ta saki wani tsaki tare da mik'ewa tashiga wanka, sai da tayi wanka tana fitowa, kalo d'aya Haiydar ya mata, ya mik'e ya nufi bayi wanka yayi ya fito, yazo gunta yanyota jikinsa yayi, cikin salonsa na rikitarwa yake shafa bayanta, yace"haba my Falmi kinsan ba wata macen da zata tab'a sayen zuciyata.
"Ni nakine ke kad'ai kuma ina qaunarki.
Kalon banza ta masa cike da masifa tace' kai Haiydar kasani nayi danasanim aurenka ni Fatima.
"Gashi yanzu ka jamin kayan raini.
"Wacce nake gani a k'ark'ashina, wai ita zata dawo kishiyata.
"In sam ba zai yiwu ba ina.
Haiyadr cikin muryan lalashi yace"kinsan bazan tab'a had'aki da wata ba.
"Aure ai kamar an fasa tunda baki so.
Hararansa tayi tare da d'iban kayanta ta fita.
Haiydar ko mai ya sha, tare da saka kayansa, ya d'auki key d'in motarsa, don zuwa amsa kiran Hajiya da bata hak'uri ta janye k'udirinta na batun auren Indo.
A gidan su Hajiya kuwa, Hasna ta wanke ma Indo kai, ta gyaramata tare da busar mata shi da dryer, alwala sukayi suka gabayar da Sallah magriba, suka jira sai da akayi Isha'i nan ma sukayi, Hasna tace"Aunty na zo ki zauna gaban madubi kiga wani abu.
Ba musu Indo tazo ta zauna, Hasna ta gyara mata fuska, ta gyara giranta, ta fara mata kwaliya, ni dai Rash ina gefe ina kalon ikon Allah, don naga shafe-shafen da goga wancan yayi yawa. Indo tace"kai Hasna nikam abun ae zai min yawa.
Hasna ta k'yalk'yale da dariya, tace"Aunty na ki tsaya ke dai kiyi kalo kawai.
Murmushi Indo tayi. Hasna tayi kealiya ma Indo, tare da d'auko mata, wani atamfanta riga da skirt, mai kalan ja da bak'i. Indo ta karb'a ta shiga bayi ta saka, tana fitowa Hasna sai murmudhi take, Hasna tace"zauna ki gani.
Indo tace" oh ni kam Hasna har yanzu duk a make-up d'inne haka?.
"Ina zani da kwaliya bacin yanzu bacci zanje nayi.
Hasna tace"Aunty bazaki gane bane.
Hasna ta d'aura mata d'an kwali, ta mik'o mata flat shoe, shima kalan ja da bak'i, sai gyale shima ja da bak'in, yana da stone farare, sai haskawa sukeyi, ne sa kad'an Hasna takoma, tana kalon indo, cikin muryan farin ciki tace"wooow My Aunty na you look so beautiful. Muryan Hasna danaji yasa ni Rash na d'ago da sauri, bansan lokacin da wayata ta sub'uce ta fad'i ba. Ba abinda na furta sai kalman"tsarki ya tabbata ga Ubangiji daya k'agi wannan k'yak'yawan suran.
"Hmm masu karatu kuyi Imagine d'in Indo a cikin wannan shigan, ya kuke gani zata haska?.
Hasna ta fara yabon Indo, tare da d'auko wayarta tashiga d'aukarta photo.
Haiydar yana shigowa gidan su Hajiya, d'akinta ya nufa, da sallama ya shiga, ta amsa masa, bayan ya gaidata, Hajiya ta fara masa nasiha mai ratsa jiki, sanan tace"kar kuma naji kasake cewa kalman da za'a fasa aurenka da Indo.
"Wataran in Allah ya yarda zakayi alfahari da hakan.
Ta dad'e tana masa kalamai masu tsuma jiki, wanda dole yafasa abunda yaso fad'a mata.
Hajiya tace"katashi muje ku tafi, in Abba ka ya dawo duk yanda muka tsayar dashi zakaji.
"In zata dawo gidan nane kafin ayi aure to ko kuma ta zauna acan, duk sai in ya dawo zamu tattauna.
Jiki bak'wari Haiydar ya mik'e suka fito falo, Hajiya ta kira wayan Hasna tace"ku sauk'o k'asa ke da Aisha.
Bata jira amsansu ba ta kashe wayar, Hasna ta kama hannu Indo suka fito, suna saukowa kenan Haiydar ya d'aga kansa, dake yana kalon saitin step d'in. Daram! K'irjinsa ya buga, kasa d'auke fuskansa daga kalon Indo yayi, tun dayake da ita yaune rana ta farko da ya fara ganinta da kwaliya, kuma ta saka gyale, gashi shara-shara. Sai da suka iso falon, suka zauna Hasna ta gaida shi, haka Indoma.
Hajiya nasiha ta musu sosai tukun tace"ku tashi muje ku tafi kar dare yayi, duka suka mik'e Hajiya ta kama hannu Indo, da kanta tasakata a gaban motar, ta lek'o tace" Aunty na sai kin jini.
Wani mugun kalo Haiydar ya sakarmata, bashiri ta jabakinta ta bar gun, ta damotan dukayi yabar haraban gidan, sai da sukayi tafiya mai d'an nisa, kafin suka iso qofar gidansa, horn yayi mai gadi ya bud'e masa suka shiga. Indo ta bud'e qofar mota tafita, hartayi nisa Haiydar cikin tsawa yace" kee tsayawa tayi bata juyo ba, cikin zafin nama ya nufota yana huci kamar zaki, da k'arfi ya k'ara cewa"Kee bakiranki nakeyi ba. Cikin razana Indo ta juyo sam batasan Haiydar ya tahoba, aeko jiyowanda zatayi, sai a k'irjinshi tasamu mzauni, Falmi ko jin muryan Haiydar yasa tafito, hmm dai-dai lokacin kuma Indo ta fad'a jikin Gaiydar bisa tsautsayi, Falmi wani razananen k'ara tasaki, tare da yi kukan kura tayi kansu.
Ni ko Rash jin irin gurnanin da Falmi tayi yasa na arci na kare.

             DEDICATED TO
        AISHA MUHAMMAD
    (MAMAN ABDUL SHAKUR)

            ��RASH LUV✍��

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts