[10:16PM, 7/18/2016] Kardawiya:
BABBAN KUSKEREN
DANA TAFKA
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
*®NWA.*
*Pg-223~224.*
Abban mu ya dawo daga Saudi na zo gida masa sannu da dawowa da wasu dangi bayan ya huta ya ciro tsara ba ya bai ma 'Yan uwa da abokan arziki ya raba musu su Hajiyar mu ko wanna awarwaron ya sayo musu wanda kud'insa bana wasa bane anan yaraba musu ana bama Hajiyar mu nata Lamid'o yasa kuka shidai sai dai abasa wannan awarwaron ne na zinari ya masa kyau ba irin rarrashin da ba'a masa ba yaki nan Hajiya ta d'auka ta bashi kyauta. Haka rayuwa yaci gaba da tafiya Sarkin Fulani na gwada mana gata kasancewar mukad'ai ya haifa 'Ya'ya biyu bayan wasu shekaru Lamid'o ya girma a kwai ranar da bazan manta ba ranar da muka masa ganin k'arshe ranarda kishiyar Hajiyar mu ta aiki driver (mai tuk'a mota) garinsu Lamid'o naji zasu tafi ya ce shi sai ya je Alkaleri kasancewar ita 'Yar garin ne nan Lamid'o ya d'au yar jakarsa yasa kaya kala 2 kasancewarsa mai tsafta ne kuma sai washe gari zasu dawo, kuma duk inda ya ke baya rabuwa da hoton iyayen mu wanda mukayi tare don shima ya shaku da baban mu sosai, suka tafi da driver(mai tuk'a mota) can kusan yamma sai ga wasu mutane da kukan su wai Lamid'o sunyi hatsari harshi kamma ya kone k'urmus sai tokan sa akà gani to kinji labarin rabuwan mu da Lamid'o wanda sanadin rasuwarsa yasa hawan jini ya kama Hajiyar mu itama bata dad'e ba Allah ya mata rasuwa. Aishat wacce take hawaye ta sauke ajiyar zuciya Hajiya ko ta ce"Hasnat je d'aki ki d'auko waya na kira Abba na in sanar masa don na san zaifi kowa farin cikin ganin 'Yar Lamid'on sa" Hasna ta d'auko waya Hajiya ta kira Sarkin Fulani ta koro masa bayani cike da murna wanda sai da yayi kwalla harda sujudu shukur yayi nan take yasa aka bama Aishat suka gai sa. Hajiya ta karb'i wayar Sarkin Fulani ya ce" Gobe ku biyo jirgi da wuri kuzo naga jikata don bana jin dad'i ne ni da yau nazo". Hajiya ta saida masa suna zuwa, take Hajiya ta sanar ma Babansu Haiydar shima yayi murna ya ce"in Allah ya yarda cikin satin nan shima zai dawo". Haiydar shi ya je ya musu komai harda shi a tafiyan, ranan Aishat kasa bacci tayi dan farin ciki da murna harda yi nafiloli ta gode ma Allah tare da addu'a Allah ya jikan mamanta.
Washe gari da safe suka shirya sai gombe, tun daga Airport suka ga jerin dogaraye suna jiransu ga wata rantsaysiyar lemozine k'atuwa da akaje d'aukarsu a cikin ta. Aishat kam in banda kalo ta dawo kamar 'Yar k'auye sai kale-kale takeyi har suka zo wani k'aton katafaren gida wanda in aka bar Aishat sai ta ce wannan shine white house da ake fad'a na Abuja. Suna sauka nan dogaraye suka fara gaishesu har suka shiga falo, Sarkin Fulani dake Falon idonsa nakan Aishat tabbas wanan jinin sa ne take idonsa ya kawo kwalla duk da yana daurewa hannu yamata alamar tazo ya rike hannuta tare da dafa kanta yana hawaye ji yake kamar Lamid'o ya rike sai da suka zauna kowa ka gani fuskan sa d'auke da fara'a da farin ciki in ka d'auke Hajiya k'arama da ko dariya batayi nan Sarkin Fulani ya sake niman jin k'arin bayani Hajiya ta basa labari Aishat ma ta d'aura da iya sanin ta nan ya rungumi jikarsa yana kuka itama tanayi. Ana haka sukaji an turo k'ofa tare da sallama dukkansu suka d'ago kai tare da kallon k'ofar ko ni ma Rash dana kalli k'ofar wani farin bafulatani dogo mai karan hacci kyakyawane wanda za'a kwatanta a gurin kyau amma ya d'an girma amma kuma girman ta had'u da wahala fuskan sa ta cika da k'asun ba da alamar dai yana cikin wahala cikin sauri Hajiya ta mik'e a razane Sarkin Fulani da k'afarsa ke ciwo bai san lokacin da ya mik'e ba murtsuk'e idonsa yasoma yi don yaga ko mafarki ne yakeyi amma ina ba mafarki bane wannan zahiri ne tabbas wanna ko ba makawa babu tam-tama.........
*®NWA*
*DEDICATED TO*
*AISHAT MUHAMMAD*
*(MAMAN ABDUL SHAKUR)*
*RASH KARDAM*
0 comments:
Post a Comment