New Post

Wednesday, 16 August 2017

BABBAN KUSKURE..126-135

����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

Pg-126~130.

Haskene ya mamaye ko ina nacikin corridor d'in, da sauri ya kali fuskan Indo hawaye ke sauka, yana d'aga kai yaga Husna tsaye zata fito daga d'akin Hajiya. Take ya ji haushin kanshi, cikin zuciyarsa ko cewa yake"wai me ke shirin faruwa dani ne?.
Hannusa da ke rike da Indo yayi saurin tunkud'ata, sai data kai har kasa ya tsata mata yawu, Hasna kuwa wani mugun harara ya wurga mata, wanda yasata komawa d'aki bashiri jikinta harna b'ari, don ta san halin Haiydar in ransa ya b'aci bayida sauki.
Sai da taji ya banko qofa alamun ya fita, kafin ta fito da sauri tayi gun Indo, ta kamata ta d'agota tace"Aunty na dan Allah kiyi hak'uri da halin Ya Haiydar.
"Watarana sai labari kinji.
"Kuma ga dukkan alamu ya Haiydar na sonki amma shi kansa bai san haka ba.
Indo kam in banda hawaye ba abunda takeyi, haka har suka koma cikin d'akin, Indo kaya ta cire tasaka na bacci ta kwanta, amma sam ba bacin take ba, sai tunanin irin wulakancin da Haiydar ya mata.
Wata zuciya tace"Indo ina ke ina Haiydar.
"Inake ina iya kishi da Falmi ko kin manta suwaye Falmi?.
"Ke fa ba kowa bace face yar aikin gidansu.
"Marar asali bakida gatan ki sai Allah.
"Bakisan kowa ba.
Wani zuciya kuma yace"a kul d'inki Indo, guduwa ba naki bane.
"Kina d'iya mace kinsan inda zakije ne?.
"Ta iya yuwa kije gunda za'a b'ata miki rayuwanki.
"Kawai dai ki hak'ura har Haiydar ya gaji ya sakeki.
Ajiyar zuciya ta sauke tare da k'ara lumshe idonta, tare da tuna abunda ya faru dazu.
Washe gari da safe, aka tashi da aiki sosai, don ranane ran d'aurin aure. Abba saida ya yanka saniya, Hajiya ko baki har kuni, don murna.
K'arfe d'aya da rabi bayan Sallah jumma'a dubban mutane suka sai da d'aurin auren Aisha Muhammad da agonta Aliyu Khaleed Baba(AK Baba) da Amaryansa Aisha Muhammad(Indo). Akan sadaki naira dubu sitin 60k. Bayan d'aurin aure ne, jama'a suka wuce Sogiji Hotel don gudanar da Waliha, duk wanda yaje gun yaci ya sha, sai fatan Allah ya basu zaman lafiya, tare da k'azantan d'aki.
Haiydar tun daga nesa na hango shi, cikin fararen shadda da gare, ya matuk'ar yin kyau tamkar bashi ba, fiskan nan tashi ba yabo ba fallasa, duk yanda naso in gane wani abu, amma dul yanda naso na kasa tan-tace, yau farin ciki yakeyi ko bakin ciki. Haka suka kammala kowa ya kama gabansa. Ango ko ya nufi sabon gidansa, inda Falmi da kyar ta koma, don cewarta ita sai dai ya barta ita kad'ai, da kyar ya lallab'a ta takoma, sai da ya zuba mata kud'i masu yawa kafin ta yarda ta koma.

                 DEDICATED TO
           AISHA MUHAMMAD
     (MAMAN ABDUL SHAKUR)

               RASH LUV��
6/3/2016] Rash Kardam ����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

Pg-131~135.

Haiydar sai bayan la'asar ya nufi gida, tun a falon Falmi yaji muryan yan'uwanta, sai ya fasa shiga d'akinsa ya nufa ya cire manyan kayan, ya shiga bayi ya watsa ruwa, yana fitowa ya tsane jikinsa ya saka kaya maras nauyi don ba inda zai je. Kwanciya yayi ya d'auko wayarsa Falmi ya kira, wayar sai ringing takeyi amma taki dagawa, don wani masifan haushinsa takeji kamar tayi hauka. Nasiba tace"Falmi ki d'auka kiji mai ze ce miki, ai yanzu ne lokacin da zaki zuba mulkinki son ranki a gidan nan.
Kowa da kalan nata munanan shawaran, Falmi ta d'aga wayar tace"hello ina jinka. Cikin isa take maganar, Haiydar yace"My Luv bazakizo ki ga lafiyata ba?.
"Gani sai tunaninki nakeyi nakasa samun sukuni.
"Mtssss to mai zan maka bacin ga amaryanka ba sai kaje gunta ba.
"Ai tana da abunda kake buk'ata sai ta baka. Kawshe wayar tayi suka tafa tare da shewa, Nasiba tace"shawaran da zan baki duk yanda zakisan yanda zakiyi kar ki bari yaje gun dinner nan.
Falmi tace"Nasy taya zan hana shi zuwa gun dinner?.
"Mtsss haba Falmi sai kace ke ba mace ba.
"Kisan duk wani hanyan danzakibi ki hana sa zuwa.
Nuwairay tace"kin san mai zakiyi Falmi.
Cike da k'osawa tace a'a.
Nuwairat tace" yanzu in ya sake kiranki ki d'auka ki gwada masa kin sauko, amma kice kina tare da baki, ya d'an jiraki.
"Sai ki bari dab da magriba kiyi kwaliya ki tafi d'akinsa, kar ki bari ko sallah isha'i ya fita waje.
"Ki nuna masa salonki ki kuma nuna masa kina da buk'atarsa yanzu, ko da kunyi ki nuna bai ishe kiba, kin ga ai dole bai son bacin ranki dole ya hak'ura.
Shewa sukayi da tafawa Nasy tace"shegiyar kin kawo idea fa.
Ana haka ko sai ga kiran Haiydar haka Falmi ta d'auka ta rinka fad'amasa kalamai masu dad'i, tace"Honey ina tare da baki barin sallamesu zanzo mu gaisa. Ko da ankira magriba karka fita kayi a gida, ko in kaje ka dawo ka jiran zamuyi magana.
Haiydar cike da murna ya amsa mata da"ba komai ni yau ji nake kamar nafi kowa farin cikin, tunda kin bar fushi dani.
Haka sukayita hira daga k'arshe sukayi sallama.
A gidan Hajiya ko bayan d'aurin aure, da yamma walima suka shirya na gani na fad'a, komai cas-cas, akayi walima aka tashi, da daddare kuma zasuyi dinner.
Tun bayan sallah magriba suka soma shirin dinner, amarya na hango cikin fafaren net yayi matuk'ar yi mata kyau. Abun gwanin burgewa, ana kiran Sallah isha'i sukayi sallah suna jiran zuwan angwaye.
Falmi bayan sallah magriba wanka tayi na musamman ta sanya wani riga iya gwiwa, daga gefen cinyan a tsage yake, bata sanya bra ba, duk wani sassan jikinta kana gani. Kayan sun haska jikinta dake fara ne, dai-dai lokacin Haiydar ya fito daga wanka d'aure yake da towel, ganin falmi da sauri ya k'araso gunta, janta jikinsa yayi, yace"Honey nayi misin d'inki kwana biyu.
Hannuta tasa tafara wasa da sajensa da ya kwanta luf-luf gwanin burgewa, cakul-kuli tasoma masa, dariya yayi yace"wato yau tsokana kikeji ko?.
Hannu ta kai tasoma ware towel d'in da ke jikintsa, wasa yasoma yi da gashin kanta, ganin tsayuwa ba zai d'aukesuba ya d'auketa cak sai kan gado, yasoma mata wasani sai da abu yayi nisa Falmi tasoma jan jikinta, komai ta tuna ta tashi zata mik'e, ya kamo hannuta cikin dashashiyar murya yace"Honey miye haka?
"Kinsan ina tsananin buk'atarki a wannan lokacin.
Wani banzan kalo ta wurga masa da niyar mikewa ta fita, cikin azama ya diro tare da kaimata wani kyakyawan cafka.

               DEDICATED TO
           AISHA MUHAMMAD
     (MAMAN ABDUL SHAKUR).

          RASH KARDAM��

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts