New Post

Wednesday, 16 August 2017

BABBAN KUSKURE... 194-196

[7/11/2016]Rash Kardam ����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

               *®NWA.*

*Pg-194~196*

Ba k'aramin razana tayi da ganinsu cikin wannan yanayi, Aishat ta razana amma shirin ko ta kwana da tayi, hakan yasa ta shanye damuwarta, ta juya sai murgud'a jiki takeyi, ta kama hanyan komawa falo, Haiydar ko yanuna damuwarsa, shima ya juya da niyar komawa cikin falon. Falmi da sauri tasha gabansa, cike da masifa ta fara ce wa"Haiydar asai baka da mutunci? A sai kai d'an iska ne? Maciyi *AMANA*. To asirinka ya tonu, karasa wacce zakana bi sai Yar aiki na?". Wani mugun kalo ya sakarmata, bai tanka mata ba yabi gefe zai wuce, da sauri ta sha gabansa tare da shan kwalar rigansa. Hannunsa yasa ya b'amb'are hannuta daga jikin rigarsa, da sauri tasake tare gabansa, Haiydar ya ce" Falmi ki bini a hankali duk wani rashin kunyar da kike take, tsaf zanyi maganinsa, karkiga na kyaleki kina yanda kikeso, kice zaki takani son ranki, a k'ark'ashina kike". Wuceta yayi ya nufi d'akinsa, sam shi baya son hayaniya. Falmi ganin ya tafi, ta juya gun Aishat daniyar mata rashin mutunci. Aishat ko ta d'aura kafa d'aya akan d'aya, Falmi ganin irin zaman da tayi gashi k'ananan kaya ne ajikinta, don duk suran jikinta ya bayyana, hakan ya k'ara b'ata mata rai, ta iso gaban Aishat ta ce"ke Yar aiki kuma Yar shege wa ya baki daman saka wa 'yannan kayan?". Aishat tayi banza da ita bata amsa mata ba, hakan yak'ara kub'ular da ita. Ta sa ke ce wa"ke k'aramar 'Yar iska da e fa nake magana". Aishat ta saki lallausar murmushi, ta mik'e tare da gir-giza jikinta ta tak'o har gaban Falmi, sai da tamata kalon ido cikin ido, ta sake k'ara taku biyu zuwa uku, kafin ta juyo ta ce"Fatima kike ko Falmi? Ko ma dai wa kike duk ba damuwa ta insan sunan bane". Falmi kasake tayi don tsananin mamaki, ko motsi ta kasa, sai bakin da ta sake tana kallon Aishat. Aishat ta ci gaba da cewa" ina sane da duk wani wulakancin da kika min tun daga tasowa ta, harda cin mutuncin da kukayi ma uwata, kin wulak'anta ni wulak'ancin da ko kare baza'a masa ba. Falmi ki sani da da yanzu ba d'aya yake ba, ki sani biyu yafi d'aya, kamar yanda uku tafi biyu. Ki sani wutsiyar rak'umi tai nesa da k'asa, kamar yanda na tsere miki yanzu. Ki sani a da kin taka Indo ta kyaleki, a yanzu na canza daga Indo zuwa Aishat, kuma Aishat bata juran wani raini da wargi. Samun kwanciyar hankaliki da zaman lafiyanki a gidan nan, shine kiyi sabgarki, banda shiga hark'an Ashanty baby, domin bana juran wani wargi. A hankali tasoma takawa tana sarrafa mazaunanta da k'irjinta, taku uku ta k'ara ta juyo ta ce"oh! Na manta ban sanar da ke, ko da gigin wasa karki ce zaki ne mi Aishat da fad'a, don bana had'a k'irji da kishiya kuma banga wannan kishiyarba, kuma ina fatan kinji duk abunda na fad'a miki?.  Ta juya idonta ta ce" na manta ban miki godiya da karamcin da kika min, gaskiya kin can-canci in gode miki, kin had'a ni aure da gwarzon Mijiki Haiydar kuma kin iya had'i sosai, don ni kaina na san, nasamu mijin nuna wa sa'a gashi kyakyawa, jarumi a kowanne fage nagode". Hannu Aishat tasaka akan bakinta tare da yin kiss ta hura ma Falmi, ta saki wani murmushin mugunta, don yanda taga Falmi ta dawo, juyawa tayi ta nufi d'akinta tana rangwad'a. Falmi batan lokacin da ta d'aura hannu aka ta fara ihu tana cewa"lalle yau nasan na *TAFKA BABBAN KUSKURE* wato d'an hakin da na raina...... Na raina Indo sai ita ce zata gasa min aya a hannu".

Ni ko Rash ina gefe na ce"gaskiya wannan show d'in yayi Aishat ta burgeni. Lalle wannan shi ake kira da *BABBAN KUSKUREN DA KI KA TAFKA* Falmi". Gyara zama nayi don inci gaba da kalon wannan gurmi mai k'ayatarwa, kashh! Sai ga wayata tana nuna battery low.

  
                *®NWA.*

               *DEDICATED TO*
        *AISHAT MUHAMMAD*
   *(MAMAN ABDUL SHAKUR)*

            *RASH KARDAM��*

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts