New Post

Wednesday, 16 August 2017

BABBAN KUSKURE... 217-220

[7/17/2016]Rash Kardam ����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

               *®NWA.*

*Pg-217~218.*

Dr ya ce"ya kamata a canza mata kayan jikinta sun b'aci". Haiydar ya amsa da "to". Ya kalisu Hajiya ya ce"barinje gida na d'auko mata wasu kayan". Hajiya ta kalli agogo wayan ta karfe biyu da rabi ta ce"to kaje Allah ya kareka". Ya amsa da "Ameen". Ya fita gudu yaringa shararawa har ya iso gida horn ya ringa yi Falmi cikin bacci taji horn d'in kafin da sauri ta leka taga Haiydar ne ke shigowa cikin sauri ta shafa turaren nan ta kuma shiga bayi ta kuskure bakinta da ruwan maganin ta nufi k'ofar falo. Cikin rashin sa'a kafin ta riskeshi har ya shiga d'akin Aishat ya d'ibi mata kaya kala biyu marasa nauyi ya fito kenan sukayi two eyes(ido biyu) da Falmi hannuta a kan k'ugunta cikin isa da gadara ta ce"kai daga ina kake a cikin wannan dare?". Haiydar duk sai ya ji komai ya kwance masa ya tsinci kansa da ba zai iya yi mata musu ko gardama bare yaki bin umurnin ta, sai da ya yayi jim kafin ya ce"daga Asibiti nake". Cikin hanzari ta ce"waye a Asibiti?" Haiydar ya kalleta ya ce"Aishat ce". Dammmm! k'irjin falmi ya bada sauti bata san lokacin da ta sanya hannu a k'irjinta ta dafe ba ta ce"mai ka ce?". Haiydar yasake mai-maita abunda ya fad'a nan take zuciyar Falmi yafara azal-zala ta ciji bakinta hannuta ta had'a ta buga tare da fara safa-da-marwa tana zagaya guri idonta ya kad'a yayi jajazur ta d'ago ta ce"yanzu a wani hali take?". Haiydar ya ce" jikin da sauki sosai". Ran Falmi in yayi dubu ya b'aci ta kalli Haiydar ta ce"maza kaje ka ajiye kayan nan ka wuce d'akinka". Da sauri ya amsa mata da "to". Amma wani bangare na zuciyarshi bataji dad'in haka ba yana so yaje amma ba halin yi mata musu. Haka Falmi ta tasashi gaba sai da yaje d'akinsa ya kwanta ta nufi d'akinta.
Acan Asibiti kuwa shiru-shiru hajiya suka ga bai dawo ba hankalinsu ya tashi sosai, da sassafe hasnat tazo musu da kayan tea da ruwan zafi har wajan bakwai Haiydar bai zoba, hakan yasa Abban da kansa ya ce"Hasna muje gidan Aliyu muga ko lafiya". Hasnat da sauri ta amsa suka nufi gidan a motan Abba suna zuwa mai gadi ya wan gale musu gate(gareji) suka shiga, Mai gadi yana ganin Abba ne ya gaidasu cikin mutunci da girmamawa, Hasnat ta bud'e falo taga bakowa ganin haka tayi magana ma Abba ya shigo kasancewar tsakanin Main falonsu da side d'in kowaccen su da taraza Abba na zama Hasna ta nufi k'ofar d'akin Haiydar ta kwan-kwasa kamar a kunne Falmi sai gata ta fito tana karairaya ganin Hasna ta ja tsaki ta ce"ke lafiya zaki zo kina tashin mutane da safen nan?". Hasna ta kalleta a wulakance ta ce" gun d'an uwana nazo ni da Mahaifinsa ke son ganinsa". Falmi tayi dariya kice min ke da tsoho kuka zo". Ran Hasna ya baci ta juya ta koma falo Falmi ta biyo bayanta ta ce"aa Tsoho ne haka a gidan mu". Abba yana jin ana bada labarin rashin kunyan Falmi bai tab'a gani ba sai yau ransa ya b'aci sai karairaya take tana fad'an banzan magana Haana cikin fushi ta kaiwa bakin duka wanda saida jini ya zuba, Abba kasa cewa komai yayi ila fitowa daga gidan Hasna ta kalleta ta ce" ki iya da bakin ki don bazaki tab'amin iyaye na kyaleki ba banza shasha". Fuuuu Hasna ta bi bayan Abba sai a lokacin suka ga motan Haiydar kenan yana gida. Ran Abba ya gama b'aci amma ya daure ya boye ya ce"Hasna muje gida ki d'auko ma Aishat wasu kaya acikin kayanki". Haka ko akayi suka dawo Asibiti da kayan Hasnat. Satin Aishat d'aya a Asibiti aka sallameta jiki yayi sauki, wanda duk kwanakin nan Haiydar bai tab'a tako k'afarsa ba abun yayi ma umma ciwo amma taki nunawa a b'an garen Aishat ma haka.
Falmi ko ta samu yanda takeso don juya Haiydar takeyi son ranta shiko duk da wani b'an gare na zuciyarsa baya kin dad'in abunda yakeyi amma ba yanda ya iya.

          *®NWA*.

                *DEDICATED TO*
          *AISHAT MUHAMMAD*
     *(MAMAN ABDIL SHAKUR)*

                *RASH KARDAM��*
[7/17/2016]Rash Kardam ����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

               *®NWA.*

*Pg-219~220.*

Hajiya tasa ka Hasna taje ta d'iba ma Aishat duk wasu abunda zata buk'ata ta koma gidan su da zama kulum tana cikin sanyaya mata zuciya akan halin Haiydar.
Falmi ko ta samu yanda takeso don juya Haiydar takeyi son ranta shiko duk da wani b'an gare na zuciyarsa baya jin dad'in abunda yakeyi amma ba yanda ya iya sai dai abun na damunsa a cikin zuciyarsa kulum yana cikin tagumi da damuwa.********************
   8months latter.
Cikin wa'yan nan watannin abubuwa da dama sun faru harda fara jaraban Aishat sunyi WAEC yanzu suna NECO har sun kusa gamawa, yanzu driver Hajiya ta samar mata shi ya ke kai ta ko ina, Hajiya kuma ta dage da addu'a akan halin da Haiydar ke ciki tanayi kullum bata daina ba.
Rayuwan Falmi da Haiydar ko abin tausayi don tana gasa masa aya a hannu bana wasa ba duk ya rame yayi baki kamar ba ASP A.K BABA ba. Kuma duk da tsareshi da Falmi keyi bata bashi hakkinsa wataran sai ya mata kuka kafin tasa ya ajiye mata kud'i tukun ta kulashi, a hakama sai ya sha masifa kafin ya samu.
Tabbas Allah baya bacci kuma shine maji rokon bawansa don shi ya ce mu rokesa zai amsa mana sai dai ya jinkirta don ya ga imanin bawansa. Haka abun ya faru a gun Hajiya don yau Haiydar yana office yaji kaman an tsikaresa take ya tuna abunda ya faru da irin rashin zuwa gun iyayensa har kuka sai da yayi, cikin hanzari ya mik'e ya nufi gida wanka yayi yasaka kaya mai kyau ya fesa turare yayi kyau amma ya rame yayi duhu amma kyansa nanan hancinsa ne yakara fitowa. Ya fito falo sai zuba k'amshi yakeyi dai-dai lokacin Falmi ta fito ganin wanka da yayi ranta ya b'aci da sauri ta nufosa sam yau ta manta bata shafa turare bare ta kuskure bakinta da magani ta ce"kai Haiydar ina zakaje harda yin wanka haka? Ko kamanta kana k'ark'ashin izini nane?".  Bai tanka mata ba don zuciyarshi na azal-zala ganin zai fita tazo tasha gaban sa daman yana cike da ita yanda da safe tayi ta masa tsawa kamar shi d'anta ne, kwalan rigan sa ta sha cikin hanzari ya bata kyawawan mari ya fara ball(kwallo) da ita saida ya jibgeta son ransa ya fita,  motarsa ya shiga sai gidan Hajiya masu gadi na ganinsa sai da sukayi mamaki da sauri ya ajiye motarsa ya nufi cikin gidan da sallamansa ya shiga, Aishat ya fara hangota tana jikin Hajiya Hasnat ma ta hango shi kasa d'auke idonsa yayi akan Aishat Hajiya na ganin sa tayi hamdalah amma ta d'aure fuska dole ta gwada masa kurensa duk da ba da sonsa bane. Hajita ta ce"Hasna Aisha maza tashi ku shiga d'aki da sauri suka mik'e Aishat duk da taji dad'in ganinsa amma zuciyarta na suya da abunda ya mata da sauri tayi d'akinsu da gudu ta fad'a kan gado ta fara kuka mik'ewa tayi ta d'au hoton Abban ta da Ummanta da na iyayen Abban ta tare da awarwaron zinari mai tsada da kyalli nan tasa a gaba tana kalon su tana kuka. Hajiya ta ce"lafiya dai ko? Amma b'atan kai kayi yau ko?" Ya russuna ya gaida ta ta amsa cikin sakin fuska san nan ta ce"yauwa da man kai nake jira tunda yau Allah ya kawo ka inaso ka ba ma 'Yata takardan sakinta don bazata koma gidan ka ba wannan shine hukunci dana yanke kuma umurni nake baka ba wai shawara ba". Haiydar ya durk'usa akan k'afarsa ya soma kuka yana bata hakuri. Hajiya ganin ita tsaya kallonsa zai sa ta kayara ta mik'e ta bashi guri d'akinta tashiga taga Hasna ita kad'ai ta ce" Hasna ina Aishat d'in?" Hasna ta ce" tana d'akin mu ina ga". Hajiya ta mik'e ta nufi d'akin su sam Aishat tayi nisa cikin tunanin iyayenta bata san da shigowar Hajiya ba. Hajiya kuma ganin Aishat na kuka ga hoto a hannuta yasa ta k'arso da sauri don ganin hoto  hannuta wannan Awarwaron gwal d'in tafara karo dashi tabbas ko a mafarki bazata manta da wannan a warwaron ba, tana duba ga hoto hannu Aishat damm! Gaban k'irjinta ya bada sauti take numfashinta yasoma d'aukewa hannun take nuna hoton dashi tana fad'in La....mi.....d bata k'arasa ba ta yanki jiki ta fad'i kasa sumamiya dai-dai da shigowar Hasna d'akin ta saki razananne k'ara tayi kanta.

Ni Rash  danake gefe na ce" to mai ke shirin faruwa kar dai ace......... Bari dai zamuji koma miye.

               *®NWA*

                  *DEDICATED TO*
            *AISHAT MUHAMMAD*
       *(MAMAN ABDUL SHAKUR)*


                *RASH KARDAM��*

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts