New Post

Wednesday, 16 August 2017

BABBAN KUSKURE.. 207-209

[7/16/2016]Rash Kardam ����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

               *®NWA.*

*Pg-207~209.*

Ogan gani tana da taurin kai kuma zata b'ata musu lokaci yazo dai-dai ita cikin muryan 'Yan iska ya ce"tun da ki kayi taurin kaikuma ki ka b'ata mana lokaci kafin mu aiwatar da aikin da'aka samu sai nida Yarana mun biya buk'ata dake, bakinsa ya lashe tare da kawo hannusa ya shafi k'irjinta ya saki mayen murmushi haka suka jata zuwa motarsu suka tayar su ka bar gurin. Gudu suke sharara wa Aishat ko sai hawaye takeyi tanaso ta basu hak'uri amma ina ba hali bakinta yana rufe gam da salatab Ogansu ko tasata yayi a gaba yana kalonta don ya rinyar ta matuk'ar masa kyau ji yake koma dai ya fasa aiwatar da abunda aka sasune kawai ya b'oyeta ya mayar da ita Matar sa kuma inda zai na hutawansa. Fatan bakinsa ya lashe tare da yin wani murmushin mugunta.
Falmi ko tana cikin wasu kawayenta wanda kalo d'aya zaka musu ka gane tattatun 'Yan bariki ne masu ji da bariki, wata kawar Falmi ta kaleta ta ce"Falmi gaskiya baki da kyau yanzu abunda ki ka sa ayi kenan niko kishiyarki kyau ta ke min". Wani mugun harara Falmi ta sakar mata ta ce"yanzu zamu b'ata da ke don duk wanda zai bi bayan Indi ko ya sota to tabbas makiyina ne ina adawa da shi". Gwantsi da ke gefe jin kalaman Falmi ta shek'e da dariya ta ce"har uwar Haiydar d'in kenan kina adawa da ita". Falmi ta ja tsaki"mtsss ita a su wa yanzu next harina ita ce daga nan ina fita gidan mu zaje gun Mummy na ne, dole mu koma gun Malamin nan inaga asirin nan ya karye ne". Gwantsi ta ce"ni ko in da ni ne ke Falmi bazan tayar da hankalina ba tunda gaki kintara kud'i kin dawo babbar mace, gaki da naira kuma ai Haiydar yana sonki da yawa tunda ke kikace da hannusa ke baki kud'in nan". Falmi ta ce"ke fa zabaki gane bane Haiydar nawa ne ni kadai da kinga abunda Indo ta min jiya sai kin bani goyan baya dari-bisa-dari". Wata Mama Zeey da ta ke gefe ta ce" ina bayanki karki ragar musu ko d'aya ai kishiya ba abin so bace kishiya! Kishiya!! Kishiya!!! ina bayanki a gama da ita kawai ki huta". Haka suka ci gaba da hiransu kowace da gur-guwan shawaran da take bata a gun.
Haiydar yana office duk ya ji hankalinsa ya tashi ya kasa zaune ya kasa tsaye zuciyarshi ba abunda take tunaso masa sai Aishat, haka kurun ya tsinci kansa da son ganin Aishat a wannan lokacin cikin hanzari ya tattara komai daman time d'in tashi ya kusa. Da sauri ya fito ya nufi motarsa ya shiga cikin sauri ya ke tuk'in sai da ya kusa shiga unguwamsu gabansa ya soma fad'uwa sai gumi ke ketomasa, k'ara gudun motarsa yayi ga gumi sai k'ara keto masa yakeyi duk da sanyin A.C da ke motar amma bai hana sa yin gumi ba. Tun daga nesa ya ke hango wani mota sak irin na Aishat amma sai wata zuciya ta ce masa" mai zai kawo Aishat nan kawai dai kalar motar ce d'aya, ko da ya iso gun k'ofofin motar a bud'e ya ke, ganin school bag d'in Aishat bai san lokacin da yatak wawan burki ba ya fito daga motarsa. Da gudu yayi gum motar baiga kowa ba sai ya lek'a ciki ba ta nan ga hijab d'in mak'arabtarta a gun da hularta, sai takalminta kafa d'aya ko da ya kali kasa nan yaga jinin da ya d'id'iga a hankali ya soma bin jinin har ya kaisa gun da 'Yan iskannan suka aje motarsu, nan ma yaga alamar kafa inda kayi kokawa da kuma alamar ta k'arfi aka d'auketa, ga tayar motarsu da yayi ribas da kuma yanda ya tashi. Haiydar baisan lokacin da yasaki k'ara ba ya na kiran"Aishat! Aishat!! Aishat! Kina inane?  Mai ya same ki? Wa ya tab'a min ke?". Fad'uwa yayi a kan gwiwarsa kamar mai (nil down) yana k'araji yana ihu ga hijab d'in Aishat a hannusa ya na kuka wi-wi kamar yaro. Da gudu ya tashi yayi gabar yana kiran Aishat! Da gudu ya dawo yayi yamma yana kiran Aishat!! Ya sake dawowa yayi Arewa yana kiran Aishat!!! Yazo ya sake yin kudu yana kiran sunanta, ya dawo kaman zarare.

Masu karatu sai kun gansa abun gwanin ban tausayi ni kaina Rash bansan lokacin da hawaye yasoma gan-garo min ba.


            *®NWA*

                 *DEDICATED TO*
           *AISHAT MUHAMMAD*
      *(MAMAN ABDUL SHAKUR)*

               *RASH KARDAM��*

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts