New Post

Thursday, 17 August 2017

BABBAN KUSKURE....231-232

[3:18PM, 7/22/2016] Rash Kardam��: ����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

               *®NWA.*

*Pg-231~232.*

Tuni ya fara rikita ta da salon soyayyan sa wanda ganin yafi k'arfin idona yasa na tattara 'yan matan k'afana nayi gaba, ina daga k'ofar d'aki ina jiyo kukan Aisha wanda ba halin na kai mata taimako haka na zauna jigum, sai kusan k'arfe uku Haiydar ya saurara mata, Aisha in banda hawaye ba abunda takeyi ni ko Rash ina gefe na ce"yau Ashanty anji maza bakin tsiwa ya mutu.....lol..". Haiydar ruwan zafi ya had'amata sai da yayi wanka kafin yazo ya taimaka mata sam tak'i yarda su had'a ido da kanshi ya mata wanka tukun ya barta tayi wankan tsarki, sai da tafito ya mik'a mata wasu kaya kafin ta sanya harda hijab a ciki tayi sallah kafin ya kawo musu abinci suka ci. Haiydar ya kalli Aisha ita duk kunyansa takeji sabida in ta tuna irin sambatun da yayi jiya sam bata son su had'a ido, hab'arta ya kama ya d'ago fiskanta ido ta lumshe cikin sanyin murya Haiydar ya ce"Aisha Allah yayi miki albarka na rasa kalman da zan gode miki ila wannan yukurci". wani d'an k'aramin a kwati yaciro mai kyalli ya bud'e tare da zaro wani zobe white gold mai kyalli da haske wanda ni kaina Rash sai dana kare fuskata da tafin hannuna sabida hasken yana kashe min ido, ko da na duba da kyau jikin zoben naga ansa A&A forever, yana sanya mata yayi kiss d'in zoben don bak'aramin kyau yayi mata ba hannu ya rike yana murzasu tare da janyota jikinsa yana mata wasu kalamu masu dad'i acikin kunnenta wanda duk sonjin gulmata ban jiyo mai ya ce ba.
Hajiya ko ganin sak'on sai da hankalinta ya tashi tabbas tasan Haiydar yayi hak'uri sosai, dole ta bashi matarsa don taga ya nitsu sosai kuma ya damu da Aisha, ganin matarsa ce bata kawo komai ba amma zuciyarta na d'ar-d'ar. Basu bar gidan ba sai bayan magriba suka d'au hanya sai da yabiya da ita super market ya mata sayya masu yawa suna isa harabar gidan sai da yaga tashiga falo ya juya ya tafi sabida yasan bai da gaskiya shiyasa bai shiga ba. Aisha tana shiga sai da ta d'an lek'a bata ga kowa ba hakan yasa ta fara tafiya a hankali, Hajiya da tafito daga kitchen ta hangota ganin tafiyar da takeyi tuni ta d'ago abunda ya faru a zuciyar ta ta ce"lalle Haiydar ya gwada min shi d'an yau ne ai ban isa ba tun kafin ya sanya na fara jin kunya gwara ya d'au matarsa su k'ara gaba". Tana fitowa dai-dai Aisha na hawa matakala Hajiya ta ce"ah! Aisha har kun dawo", cikin jin kunya ta sun kuryar da kanta ta amsa da "eh mun dawo". Hajiya ta ce"to yayi kyau kije d'aki Hasna zata kawo". Miki abinci, Aisha ta ce"Hajiya a k'oshe nake naci abinci a can"  Hajiya ta ce" to shikenan". Aisha ta wuce d'akinta sai da tasha maganin  Haiydar ya bata kafin ta kwanta sai ido ta lumshe tana mai tuna abunda ya faru tsakanin su da nan wani tunani ya fad'o mata yanzu fa in da rabo hala ciki ya shigeki, murmushi tayi kafin ta shafa cikinta haka har bacci ya d'auketa.
Yau Aisha ta kammala jarabarwata wanda aka shirya musu liyafa nagani na fad'a Sarkin Fulani da shi da Lamid'o sun halarci bikin walimar abun dai sai wanda ya gani walima akayi na gani na fad'a, bayan walima da kwana biyu Hajiya ta shirya 'Yarta da kanta ta mayar ta gidan Haiydar tare da mata nasihu masu sayaya jiki. Da dadare Haiydar da wuri ya dawo Falmi ya samu a falo tayi d'aurin rashin mutunci sai kad'a k'afa takeyi. Ganin ko kallonta bai yi ba zai shiga d'akin sa tazo tasha gabansa ta ce"to muna fuki wai mai kake nufi ne kasani lokaci yayi da zaka saki Indo, ko ka manta kai da bakin ka kace baka sonta sai yanzu kuna neman ku kareta wai tasamu ubanta mtss zaku raina min Hankali ai 'Yar shehe 'Yar she......". Wani kyawawan mari Haiydar ya bata nan tafara shirin kama sa da kokuwa shi kuma bai son yawan dukar mace kawai ya jata zuwa d'akinta ya kulleta ta baya, d'akin sa yaje yayi wanka kafin yasaka kayan bacci d'akin Aisha ya shiga ya ganta cikin wasu mayun kayan bacci wanda dashi da babu duk d'aya.

                 *®NWA*

                  *DEDICATED TO*
            *AISHA MUHAMMAD*
      *(MAMAN ABDUL SHAKUR)*

                 *RASH KARDAM��*

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts