New Post

Wednesday, 16 August 2017

BABBAN KUSKURE... 116-125

����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

Pg-116~120.

Falmi ba kalan rashin mutuncin da basuyi masu Aunty Rahma ba, amma suka kyalesu suka fita a gidan, batare da sun d'au kayan fad'ar kishiyan ba.
Indo ko tun tana d'ari-d'ari da Hajiya har tazo ta sake da ita, sam Hajiya bata d'auketa matsayin surkaba, sai dai matsayin d'iyarta.
Hasna ko sai rawan kai aketayi, duk wani d'inkunan da Indo zata saka, ita ta kaita gun telan ta, ya ciremata mayun d'inkuna, masu kyau sosai.
Hasna ta gayyato k'wayenta Pinky lady da Cutie, sabida Indo bata da k'awa ko d'aya. Hasna ta samu Sadiq shiya basu kud'in events d'in da zasuyi. Walima suka shirya sai kamu, da fulani day. Sadiq kuma dinner da kuma bikin paret d'in police.
Tun daga ran laraba aka fara Fulani Day sun tsara gurin yanda ya kamata, su Hasna da Cutie tare da Amarya sun sanya kayan Fulani, sunsha kyau ba kad'an ba, bare daman fulanin asali ka., ae ba'a cewa komai sai wanda ya gani.
Duk wanda ke gurin ya girgije, an raba k'warya masu kyau da ado, sai ludaya da bulogari, da nono kindirmo mai kyau yaji fura, hmm masu karatu ko ni Rash danaje gurin sai dana shaida hakan, ga rawan fulani da yan sandunan su kaika d'auka wani k'aramin rugan Fulani ne. Haka taro ya watse kowa cike yake da murna, bayan sun dawo gida Hasna ke kalon photo da ta d'aukesu a waya, tana yaba kyan da sukayi.
Yan'uwan Hajiya na Gombe sunzo duk wanda yaga Indo to sai ya tuna da Lamid'o, dan tabbas baza su mantashi ba sunyi rashi a family d'insu, don duk irin dukiyar da Sarkin Fulani ya tara ace baya da magajinsa namiji, sai Hajiyar su Haiydar kad'ai ta rage masa, wannan abun yasa baya yawan magana da mutane, sabida rashin Lamid'o don duk cikkin 'ya'yansa yafi sonsa fiye da kowa.
Falmi ta kaici ya isheta, da k'yar ta kira su Meesha ta sanar musu halin da take ciki, Meesha ta jin-jina al'amarin nan tace"zanzo sai ran yini don yanzu bana gari na tafi Kaduna. Haka sukayi sallama, Falmi duk ta rame sosai, abunci ma bata iya cinsa mai kyau sosai, baran in ta tuna cewa Yar'aikinta ne zata zama kishiyanta, nan take zuciyanta ya d'au suya da k'una.

                 DEDICATED TO
            AISHA MUHAMMAD
      (MAMAN ABDUL SHAKUR).

            RASH KARDAM��
[6/2/2016] Rash Karda ����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

Pg-121~125.

Nan take Falmi zataji zuciyarta ya d'au k'una yana mata rad'ad'i. Gashi Hajiya Firdausi tace"ta hak'ura boka yace, suna da nasara tunda yar aiki ce.
"Kuma Haiydar ya tsaneta Falmi yake matuk'ar qauna, a zuciyansa.
"Kuma bazai tab'a sin Indo ba.
A gidan Hajiya kuwa yau akaje akayi jere ma Indo, d'an kayan rufin asiri suka mata bak'arya, side d'inta ita d'aya da d'aki biyu, sai kitchen da store. Komai yaji dai-dai, gidam kam ya tsaru ba laifi, don a tsakar gidan ga swimming pool, ga garden, da wajan wasani abun gwanin nurgewa.
Yautake Alhamis duk inda ka leka a gidan su Haiydar, anata kamu ne, kawayen amarya sunsha kyau, suna sanye cikin wani material baki da ash colour, sunyi kyau sosai, sai da aka debi mutane tukun aka kawo wata k'atuwar Jeep ciki za'a d'au amarya. Niko Rash zuba ido nake inga fitowar wannan amarya mai ji da kyau.
Mutane naga suna ta d'aukar hoto, da sauri na mik'e, ina zuwa kuwa na hango amarya cikin kayanta, less ne dark ash da silver colour, ohohoho masu k'aratu, gaskiya in baku ga Indo a wannan rana ba, to kalo ya wuceku, don da kyar na iya gane cewa Indo ne, yar wanke-wanke da shara, don yau inda Falmi zata ganta, inaga sai zuciyarta ya buga. Cikin takun nutsuwa su Hasna da Pinky suka rike hannuta, yayin da Cutie ke gabansu, har suka isa mota. Larema hotel sukaje, gurin ya tsaru sai wanda ya gani, a cikin kwanciyan hankali aka gudanar da komai, Sadiq wasu abikan ango suka kirasa suna yabamasa irin tsabin da su Hajiya suka masa, gaskiya tayi bana wasa bace. Shiko haushi suka basa ma, ana haka har aka kammala kamu, suka dawo gida cike da murna, kasancewan gidansu Haiydar na da girma side guda aka bama yan biki, basa ta cikin gidan side d'insu daban.
Hajiya ce ta kira Haiydar, bayan yazo ta masa nasiha sosai, gameda rike mata biyu, Hajiya tace"Haiydar na sanka da zafin zuciya ka k'ara hak'uri da halin Fatima.
"Don rashin kunya da kishi suna damunta, amma dan Allah kayi hak'uri.
Sai da sukayi hira sosai yace"zai tafi a kwai wanda suke jiransa, ya mik'e ya fito.
Hasna ko sun dawo sallah sukayi nan suka soma hiran yanda biki ya kasance, Hasna ta mik'e barinje na karbo mana sakon da Aunty Rahma ta bari. Shiru-shiru Hasna bata dawo ba, hakan ya sa Falmi ta mik'e don taje gun Hajiya taji ko tananan, kanta ko d'an kwali babu, gashi yasha gyara, gashinan yazubo har gadon bayanta, cikin karai-raiya take tafiya mai d'aukan hankali. Tazo dai-dai corridor d'akin Hajiya aka d'auke wuta, laluben hanya ta fara tana kiran sunan Hasna, sam bata lura da mutum yana tahowa ba, sai ji tayi ta rungumi mutum, cikin tsoro da ta gudu, Haiydar dake ya ganeta, sai ya tsinci kansa da kara rungumeta, harda sakin ahiyan zuciya. Duk jikin Indo ya d'au bari, ga k'amshin turarensa ta cikata, da sauri da sauri k'irjin Haiydar ke bugawa, hannusa d'aya, ya sanya cikin gashinta yana wasa dashi, cikin zuciyarsa ko cewa yake"duk da gashin Falmi amma Indo ta fita sosai. Sunkuyo da kansa yayi dai-dai hab'arta, ya tallabo, yana mai kalon fiskanta duk da duhun da ke gun, d'an k'aramin bakinta nan ne ya burgesa, bakinsa ya kai kusa danata kenan, Nepa ne suka kawo wuta dai-dai lokacin take wajan ya gauraye da haske, ni Rash ina d'aga kaina wa zan gani........
Sai kunji ni gobe in dama tasamu, in kuma bansamu yin typing ba, sai bayan Sallah in Allah ya kaimu.

Taku a kulum mai qaunarku Rasheedah Abdullahi Kardam

                DEDICATED TO
          AISHA MUHAMMAD
    (MAMAN ABDUL SHAKUR)

            RASH KARDAM��

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts