BABBAN KUSKEREN
DANA TAFKA
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-164~166.
Cikin hanzari Haiydar ya tura qofar d'akin. Cike da mamaki ga takaicin abunda ya gani, wai Hasna ke dukan Falmi. Kanta yayi ya bata lafiyayen mari, tukun Hasna ta koma gefe. Falmi ko ganinsa ta k'ara sautin kukanta. Cikin b'acin rai Haiydar yace"ke husna mai ya kawo ki gidan nan?.
"Wa ya baki daman dukan matata?.
Hasna tace" Yaya baka abu.....
"Ke ni sa'anki ne ina magana kina magana.
Ganin yanda ke huci, ya nufo kanta zai daketa, ta d'au wayarta da gudu, tayi bayi tasaka key.
Ganin ta gudu Haiydar ya dawo kan Indo yace" wato kece munafukar gidanan nan ko?.
Belt d'insa yasoma zarewa, nan Indo tasoma kuka tana basa hak'uri. Hasna jin Haiydar zai daki Indo, da sauri ta kira Hajiya ta saida mata ga Haiydar zai daki Indo.
Hajiya ta kira wayan Haiydar dai-dai lokacin da ya d'aga belt, zai zuba ma Indo wayarsa tayi k'ara, yana cirowa sunan Hajiya ya gani. Ya d'aga tare da fad'in "Assalamu'alaiku.
Hajiya ta amsa masa da"Ameen Wa'alaikumusalamu.
"Ali wallahi karka kuskura ka daka min 'ya'ya, mai suka maka ne haka?.
"Ka jirani ina zuwa yanzu, tunda Abba ku baya gari, bare yazo da kansa. Bata jira amsan shi ba ta kashe wayar, Hijab ta zara da waya ta fito driver ta kira, suka d'au hanyan gidan.
Haiydar ko wani takaici ne ya tokaresa, tabbas Hasna ne ta fad'a ma Hajiya, cikin zuciyarsa ko cewa yake"lalle duk randa na rike yarinyan nan, bansan wani irin duka zan mata ba.
Falmi ya d'auketa, tare da kaita falo. Itako ta wani sakan jiki, da baki tana kuka kamar yarinya.
Hajiya ne ya shigo da sallaman ta, Haiydar ya amsa mata, kalon tambaya ta tsaya masa, kai ya sunkuyar k'asa.
Hajiya tace"ina yarana?.
"Wallahi in ka duki d'aya a cikinsu, ranka sai yayi mumunan b'aci.
Bata jira amsansa ba ta nufi side d'in Indo, tana shiga taganta, ta had'a kai da gwiwa, tana kuka mai ban tausayi.
Hajiya da sauri ta yi gunta tana cewa"Indo ya dakeki ko?.
Hasna jin muryan Hajiya yasa ta bud'e qofa ta fito.
Hajiya tace"mai ya kaiki bayi?.
Hasna tace" Ya Haiydar ne ya tashi zai buge mu.
"Na gudu toilet.
Hajiyan tace" muje falo tukun inji komai.
Hasna ta kama hannu Indo suka nufi falo, Haiydar na ganin su Hajiya sun fito, ya sauka kasa ya zauna, Hajiya ta zauna a kujera, su Indo suka zauna a kasa suma, Falmi ko tana zaune a kujera taki saukowa.
*DEDICATED TO*
*AISHA MUHAMMAD*
*(MAMAN ABDUL SHAKUR)*
*RASH KARDAM*
[7/6/2016] Rash Kardam
BABBAN KUSKEREN
DANA TAFKA
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-167~169.
Hajiya ta kalli Haiydar tace"mai ke faruwa?. Cikin in ina Haiydar yace"Hajiya na dai dawo ne, naji muryan Falmi na ihu, ko dana shigo gida da gudu, sai naji sautin kukanta a side d'in Indo.
"Ina zuwa sai na samu Hasna tana dukanta.
Hajiya tace"shine ka tashi zaka da kamin yara?.
"Shin kayi bincike akan mai ya had'asu?.
Kai ya gir-giza alamar a'a,
Hajiya taci gaba da cewa"haka babba ya kamata ya yanke hukunci, ba tare da binkiken mai ya faru ba.
"Haiydar bana son ka da hakan ba adalci bane.
"Yanke hukunci batare da bincike ba.
Ta juya ta kalli Hasna tace"ke Hasna mai ya faru har kika daki matar wanki?.
Hasna ta fara basu bayani tundaga shigowarta, harda kiran da Falmi tayi ma Indo, bata rage ko wasali ba.
Hajiya ta saki salati tace"daman kuntata ma yar mutane kukeyi?.
"Matarka har tasamu daman dukan yata?.
"To bazaiyiwu ba.
Hasna tayi sauri cewa"Hajiya ina rokon alfarma da amayar da Indo makarantar boko da islamiya.
" Tayi karatunta taga ma, kuma hakan zai bata daman samun sakewa, da samun 'yancinta, da wayewa, batare da wata ta takura mata ba.
Hajiya tace"rufe mana baki manya na magana kina saka baki.
Hajiya ta musu fad'a tace"duk randa wani ya sake ya daki Indo a gidan.
"Tabbas zakuga bacin raina.
"Kuma daga yin aure, bazan so yata tafara yaji ba.
"Amma komawa makaranta yazama dole ta koma.
"Haiydar yanzu zan tafi da matarka, za'amata registration sai angama komai ta dawo.
"Inaso gobe kazo ka kaita, amma sai mun zab'i makarantar da zatayi karatu. Kafin Hajiya tak'ara magana Falmi tasaki ihu, tana fad'in Hajiya ki taimakeni karta koma makaranta.
Nayi alkawarin bazan daketa ba, gwara ta zauna a gida, In Har Indo ta koma makaranta to nakad'e nikam. Magana Falmi takeyi ba uwa k'wab'a.
Hajiya ta mata kalon bakida kunya.
Hajiya tace"Hasna kuje da Indo ta d'au hijab d'inta, da kayanta kala biyu, kuzo mu tafi. Hasna kamar jira take, da sauri ta kama hannu Indo suka nufi d'aki.
Basu dad'e ba suka fito, Hajiya tace"mun tafi.
Haiydar ya rako su, har gun mota suka tafi.
Haiydar yana dawowa ko kalon Falmi baiyi ba, ya wuce d'akinsa.
Hajiya suna zuwa tasaka Indo tayi wanka, ta bata abinci taci, sai da suka huta Hajiya tace"Hasna yanzu wani makaranta ne yakamata a yi registration ma Indo?.
Hasna tace"inaga *SABIL SUNLIGHT* za'a mata.
"Don makaratan yana da kyau ana karatu sosai.
"Kuma sabon skul ne.
Hajiya tace"to ba matsala gobe zamuje tare kawai.
"Tunda Haiydar na fita aiki.
Hasna suka shiga d'akin da Indo, suna hira, Hasna tace"kin san me aunty na?
Indo tace" a'a sai kin fad'a.
Hasna tace" ina rokon Allah yasa in anje registration d'in nan su baki science class.
"Kinsan sabida mai yasa nake son abaki science class.
Indo tace" a'a sai kin fad'a.
Hasna tace"sabida ina so Falmi tayi regret cos taki ya auro mai aikin asibiti.
"Ni kuma tun randa aka yi bikinku, na d'au alwashin da ikon Allah sai nayi hanyan da kika koma school.
"Sannan inaso ki waye ki zama kikakiyar likita ba nurse ba.
Indo tace"nima ina da burin karatu da, sai dai rashin mai taimaka min.
"Gaskiya nagode Allah ya barmu tare.
Hasna tace"Aunty Jiddah tana kirana a waya tana tambayarki.
"Wai tanaso inta dawo zatazo ta koya miki abubuwa dayawa.
"Basa k'asan ne ita da Yaya Ghali sun fita yin wani course a waje.
Indo tace"ayya ni ae suna burgeni da Ghalinta dukansu Doctors.
Hasna tace"wallahi kam ae sai kinji labarin soyayyan su gwanin burgewa wanda aurensu, yazo musu a *BAZATA*.
Haka sukayita hira a tsakaninsu.
Washe gari Hasna ta jasu a mota suka nufi *SABIL SUNLIGHT*. duk wani abunda ya dace suyi anyishi.
Anyi interview ma Indo ganin k'ok'arinta, yasaba suka bata Science class. SSS1 daman tayi JSCE ta.
SSS1A aka bata, nan suka bata uniform da komai hatta books, da text book suke bayarwa.
Malamin da kansa ya kaita ajin, ya kira wata Sadiya S Adam, bayan da Sadiya tazo yace"Sadeey ina k'awarki?.
Wacce aka kira da Sadeey tace"yau batazo ba, bata jin dad'i.
Uncle d'in yace"ga frd nan na muku.
"New comer ce gobe zata fara zuwa, inaso ku zauna tare da ita.
Sadeey tace"okay sir!.
Malamin yace"sunanta Aisha Muhammad.
Nan suka gaisa Sadeey ta koma aji.
Su Hajiya kuma suka dawo gida, Indo in banda murna ba'abinda takeyi, wai yau itace ta koma makaranta.
Masu karatu ku shirya yazu ne gurmin zai fara, don Indo zata shigo gari, zata kile.
Masu karatu ya kuke ganin Haiydar zai yi akan Indo nan gaba, k'iyayar zata ci gaba ko zai k'are?.
Shin Indo zata ci gaba da d'aukan rainin da suke mata?.
Shin ya rayuwan Falmi yake kasancewa nan gaba?.
Ku biyo yar *JARAWA* don ji yanda zata kaya.
*HAPPY SALLAH IN ADVANCE*
*DEDICATED TO*
*AISHA MUHAMMAD*
*(MAMAN ABDUL SHAKUR)*
*RASH KARDAM*
0 comments:
Post a Comment