BABBAN KUSKEREN
DANA TAFKA
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-56~60.
Haiydar ya rairaice mata, yana had'a ta da Allah, bata yarda dashi ba sai da ta yamata Alkawarin 100k tukun ta yarda tabashi kanta.
Tun daga wannan rana Falmi tadawo galfa Haiydar son ranta, tana sati na hud'u, Indo ta dawo gidan da zama, duk wani aiki Indo keyi hatta gyaran d'akin Haiydar, abincinsa da wankin kayansa duk itatakeyi.
Bayan kwana biyu, Hasna ta shirya tace"hajiya zanje gidan Yaya indaidasu".
Hajiya tace"ki gaidasu sai kin dawo.
Mota ta d'akua sai New GRA, tana zuwa horn tayi ma gadi ya bud'e mata. Sai da ta ajiye motarta, a ma'ajiyin mota, tafito cikin nutsuwa tashiga cikin gidan.
"Assalamu'alaikum"
Falmi da ke zaune taji sallama, amma tsaban iskanci taki amsawa, Hasna tasake mai-maitawa, Indo da tafito daga kitchen ta amsa, Hasna tashigo cikin falon.
Falmi tana ganin Hasna ta ganeta don tun kafin biki sunjemata, amma dan iskanci tawani yatsina fuska, cikin zuciyarta ko cewa take"mtss wannan dangin miji daga gani zanyi fama daku?.
"Wata d'aya da sati biyu da biki, amma ace har sun fara sintiri wa mutu.
Hasna da murna ta k'araso gun Falmi, tace"Aunty na sannu da gi....
Wani kalon da Falmi ta aika mata dashi, yasata kasa k'arasa maganta. Falmi bata tanka mata ba, sai da ta mik'e tsaban iskanci tace"daga ina haka?.
"Wacece ke naji har kina cemin Aunty.
Husna ta danne zuciyarta tace"lah! Baki ganeni bane ai k'anwar Haiydar ne Husna.
"Oh! Haka fa yana da kwanwa ko?.
"Sanuki da zuwa, Indo! Indo!". Da sauri Indo tazo ta rusuna, tace"gani Aunty".
Falmi tace"ga wannan yarinya, ki bata ruwa tasha, in kin gama girki, sai ki samata".
Falmi ta juya ta kali Hasna tace"kya iya zama anan kafin Yayanki ya dawi.
Ta wuce d'aki tana wani karairaya, Hasna baki tasaki tana kalon ikon Allah.
Indo tace"Hasna sunaki ko, sannu da zuwa ya gida?.
Hasna cikin raha ta amsa, nan suka fara hira tana taya Indo aiki har suka gama.
Hasna taji dad'i zamansu da Indo, haka kurum takejin ta kamar yar'uwata, duk da Indo zata ba ma hassna kamar shekara d'aya haka.
Da yamma Haiydar ya dawo, ganin Hasna ya saki fara'a, a falo ya zauna suna hira, tukun ya mik'e yaje yayi wanka, yafito zaici abinci, yaga Hasna da Indo suna hira, wani mugun kalo ya sakar ma, Indo sum-sum tamik'e tayi d'akinta.
Duk abunda yakeyi Hasna tana lura dashi, abinci yasa Hasna tayi serving d'insa yaci. Sai can Falmi tafito cike da isa tace"kadawo shine bazaka zo ka fad'an ka dawo ba. Haiydar yace"tayi hak'uri.
Hasna da yamma tayi musu sallama ta tafi.
Ko da takoma gida, tabama Hajiya labarin Indo da kirkinta. Ta kuma yaba da hankalinta, Hajiya hartaji tana son ganin Indon nan.
Bayan kwanaki Haiydar yace"Falmi ki shirya zamuje gaida Hajiya na. Da farko Falmi taki ganin Haiydar ya dawo Aliyu na da dole ta shirya sukaje, ranan kam Hajiya taga rashin kunya ayinin da sukayi, nan Hasna ta bata labarin abunda ya faru, nan Hajiya tagane anyi ma Aliyi asiri don ba haka yake ba, sam bayason raini. Hajiya tace "Don haka dole na mik'e da addu'a.
Haka su Falmi suka dawo gida.
DEDICATED TO
AISHA MUHAMMAD
(MAMAN ABDUL SHAKUR)
RASH LUV✍
[5/28/2016] Rash Kardam
BABBAN KUSKEREN
DANA TAFKA
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-61~65.
Falmi kulum da kalan tsiyar da take tsula ma Haiydar, Haiydar sam baida hak'uri, wani sa'in da dambe yake kusantanta. Kuma dole sai ya biya Haiydar ya rame sosai, har d'an bak'i yayi.
Hajiya ko ta dage da Addu'a, har masallatai ta aika ana tayata da addu'a, Allah maji rokon bawansa.
Haiydar ne zaune a office d'insa, ga tarin takardu, amma ya kasa tab'uka komai, a hankali yake tariyo komai na rayuwansa, duk lokacin da yatuno Falmi, sai ya rintse ido don wani matsanacin sha'awan dayakeji, ajiyar zuciya yayi. Surar Falmi ne ke yawo a Indonsa, a hankali ya mik'e ya d'au key d'in motarsa.
Gida ya nufa don ji yake in bai samu biyan buk'ata ba, komai ma zau iya faruwa.
A gida ko Falmi tayi wanka, bata aikin komai sai chatt, ga iya taunan chewing gum kamar tsohuwar karuwa. Ita kad'ai tana murmushi, ga k'aran shigiwan massage na Whatsapp kamar me, duk ta cika mana kunne. Indo ko tanata aiki, don karta makara in Haiydar, ya dawo bata gama ba tasan sauran.
Haiydar ko gudu yake sosai, don yanda yake jinsa ba k'alau ba. Yana zuwa gida horn ya dinga yi, kamar zai tashi sama, mai gadi ya bud'e masa gate ya shigo, da gudu yaje yayi parking, ya fito cikin sauri ya nufi cikin gidan, yana shiga falo ya hangota, da sauri ya nufi inda take. Yana zuwa ya janyota jikinsa, ya fara shin-shinata, cikin tsawa tace"Malam lafiyarka kuwa?.
"Wani irin iskanci ne haka?.
"Mutum na zamansa zaka zo kawani damesa.
"Ko kamanta da dokanda na kafa maka ne?.
Sake matsowa yayi kusa da ita, ta matsa ya biyota, nan suka fara kokawa, ganin yafi k'arfinta tasoma dukansa, d'aukarta yayi kamar yarinya, yanufi bedroom d'insa da ita, yana ajiye ta ta mike tace"Makam anawa zan baka kaina?.
Cike da mamaki yace"kamar yaya?.
"Bayan kud'in sadakin dana akwai wani kud'in da zan sake biya ne?.
"Oh kamanta ko?.
Hanyar fita tayi, kafa ya samata ta fad'i ya mayar da qofar ya rufe. Hmmm ranan Falmi taji jiki dan sai da kusan magriba Haiydar ya kyaleta, yace"kuma kisa ma ranki kulum da dadre sau uku ko hud'u, da safe biyu kafin na fita, in nadawo uku in ba ida zanje.
"Kinga ina kyaleki ko to daga yau ba sasauci, in kuma kinki to nasan matakin da zan d'auka.
"Don bazan saka miki ido nayita kalonki ba.
Ya shiga wanka ya fita masallaci abunsa.
Ranan Falmi tayi kuka sosai, don taji jiki, kuma ta gane maganin da suka masa yanzu baya aiki
Haiydar tun daga wannan ranan ya mayar da Falmi kamar engine sa. Tunda tagane suka shiga wasan b'uya, gashi ya hanata zuwa gidansu.
Falmi ko tayi planning, na 5yrs, bazata haihu ba. Haiydar abun duniya ya ishesa, yanzu kusan shekara 3yrs da aurensu, ba abunda ya canza, a halin Falmi, ga shi ba tatab'a koda b'atan wata ba, kuma shi ya kasance mai son yara. Ganin ba zai juri iskancin Falmi ba ya yanke hukuncin k'ara aure.
Amma sai ya fuba mai hankali da nutsuwa tukun, ana haka aka kawo wani case, wani mutumi sunyi fad'a da barayi har sunjimasa ciwo, ga jini na zuna asibiti suki k'arbansa, key motarsa ya d'auka yanufi asibiti, duk wani abunda za'ayi yayi aka k'arb'i mutumin. Nan ya had'u da wata nurse sunanta Amrah tana da hankali, hakan yasa ya k'arbi number ta. Tundaga ranna soyya tashiga tsakaninsu mai k'arfi.
DEDICATED TO
AISHA MUHAMMAD
(MAMAN ABDUL SHAKUR)
RASH LUV✍
[5/28/2016] Rash Karda
BABBAN KUSKEREN
DANA TAFKA
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-66~70.
Haiydar ya samu Hajiya ya mata bayani, yace"ta fad'a ma Dad, Hasna kam tafi kowa murna.
Falmi tun dataga take-taken Haiydar tasaka, aka fara bibiyarsa nan tasamu labarin, yana neman Aure nan hankalinta ya tashi, baran da taji ma'aikaciyar asibiti, take ta kira Mum, tana kuka ta sanar mata. Hajiya Fiddausi tace"karyane dole yau naje gun Malam kiyi shiru.
"Ki bar komai a hannuna.
Hajiya Fiddaisi tana tashi sai gun malamin dake mata duba, ko da ya buga k'asa yayi wasu surkulensa. Yayi shiru can ya d'ago yace"Hajiya sai dai hak'uri fa, dole mijin yarki zai k'ara aure, sai dai shawaran da zan baku shine.
"Zamuyi aiki a kai ku sai ku zab'a masa mata.
"Don Mahaifiyar yaron ta dage masa da addu'a.
"Aikin mu bazaiyi wani tasiri akansa ba.
Hajiya jiki ba kwari ta dawo gida nan ta sanar da Falmi kimai.
Hankalin Falmi ya tashi ta rasa mai ke mata dad'i, don hatta indo bata barta ba bare Haiydar, kulum cikin fad'a suke.
Haiydar ya tsayar da ranan jumma'a magabatansa zasuje, gidansu Amrah.
Falmi ta fito zatayi d'akinsa taji yana waya da Amrah ya na sai damata ran Friday, magabatansa zasuzo, Falmi tayi kukan kura tace"kwace wayar nan ta kamashi da fad'a, farko Haiydar ya kyaleta, ya dawo falo tafiyosa. Nan tasha kwalansa, suna kokuwa saiga Hasna ta iso, ganin halin da ake ciki, yasa takiya Hajiya ta fad'a mata. Hajiya ta sanar da Abbansu Haiydar, ta sa driver ya kawota. Zuwan Hajiya tasa Haiydar ya bar dukan Falmi, Hajiya ta musu nasiha sosai, bud'an bakin Falmi tace"Hajiya nifa aure ne bana so ya k'ara.
"Yin hak'uri da k'ara aure shine zaman lafiya a gidan nan. Nan tafara rashin kunya son ranta, Haiydar ya taso zai daketa Hajiya ta hanasa.
Hajiya tace"kee Fatima aure kam ba fashi sai anyi dole.
Falmi tace"to ya auri wata ba wannan ma'aikaciyar ba.
"Ai da ya aureta gwara ya aura min Indo a matsayin kishiya.
Hasna da ke gefe tace"Hajiya ae gwara Indo sau dubu tana da hankali.
Hajiya tace"kee wayasa ka bakinki a ciki.
Hasna tace"yi hak'uri Hajiya.
Hajiya tace"ke da bakinki kikace haka ko?.
"To zan gwada miki na isa da d'ana.
"Kuma ina Indon mutum ce?.
"Kuma macece?.
"To zai aureta in Allah ya yarda.
Cikin sauri Haiydar yace"Hajiya ina bana son Indo gwanda ke kini momin wata daban na tsani Indi.
Hajiya tace"hukuncin dana yanke kenan.
"Fatima ta raina Indo ne tace haka ko?.
"Watarana d'an hakin da ka raina shi zai tsole maka ido.
"Aliyu! Haiydar da sauri ya d'ago don tunda suke da Hajiya bata tab'a kiran suma ba. Hajiya tace"in nina haifeka to ina si kamin biyya.
"Indo ita na zab'amaka kuma wataran zakayi alfahari da ita, amatsayin mata.
Hajiya tace"Fatima ina Indon take?.
Falmi cikin muryan kuka duk ra rud'e tace"bata nan na aiketa gidan mu.
"Ok! In ta dawo Hasna zata zauna sutaho tare. Hajiya ta mik'e tace"ni na tafi kaiku ma kazo dadaddare ina son ganinka.
Hajiya tana fita Haiydar ya mik'e sai jiri yakeji ya nufi d'aki, wannan wani irin al'amarine?.
"Naike shirin faruwa dani.
Hasna abun ya mata dad'i hawan kan kujera ta mik'e, tana jiran dawowan Indo du tafi.
Falmi ko ta d'aura hannu aka tana cewa"shikenan naja ma kaina tabbas NA TAFKA BABBAN KUSKURE. "Mai ya kaini furta haka ya akayi na ambaci sunan Indo?.
"Wannan shine BABBAN KUSKUREN DANA TAFKA.
"YAR AIKINA ZATA DAWO KISHIYATA.
"KUMA YAR CIKIN SHEGE.
Nima Rash daga gefe nace Falmi gaskiya kinyi KUSKURE BABBA. Bari dai muga ya wannan gurmin zai k'are don nikam banso abarni a baya.
DEDICATED TO
AISHA MUHAMMAD
(MAMAN ABDUL SHAKUR)
RASH LUV✍
0 comments:
Post a Comment