[6:58PM, 7/18/2016] Kardawiya:
BABBAN KUSKEREN
DANA TAFKA
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
*®NWA.*
*Pg-221~222.*
Hajiya kuma ganin Aishat na kuka ga hoto a hannuta yasa ta k'arso da sauri don ganin hoto hannuta wannan Awarwaron gwal d'in tafara karo dashi tabbas ko a mafarki bazata manta da wannan a warwaron ba, tana duba ga hoto hannu Aishat damm! Gaban k'irjinta ya bada sauti take numfashinta yasoma d'aukewa hannun take nuna hoton dashi tana fad'in La....mi.....d bata k'arasa ba ta yanki jiki ta fad'i kasa sumamiya dai-dai da shigowar Hasna d'akin ta saki razananne k'ara tayi kanta. Hasna ta fara jijiga Hajiya amma ina ta sume Aishat ma da sauri ta sauko tazo ta k'ank'ame Hajiya tana kuka, Haiydar da ke falo jin k'aran Hasnat yasa ya hauro sama da gudu ya nazuwa yaga Hajiya a k'asa duk ya rud'e sai da ya jijigata da sauri ya mik'e yayi cikin bayin d'akin ya d'ibo ruwa yana zuwa ya watsa mata, ya k'ara watsa mata take ta saki sassanyan ajiyar zuciya gefen idonta hawaye ne ke zuba. Ta ja jikinta ta jin gina da jikin gado Haiydar da su Aishat sai sannu suke mata Haiydar ne ya bata ruwa mai sanyi tasha ta sauk'e ajiyar zuciya ta ce"Aishat ina son ki fad'amin gaskiya dan Allah ina kika samu wannan awarwaron da hoton d'an uwana k'anina Lamid'o wanda shekara da shekaru ya rasu?". Haiydar da Hasna sun zuba ma Hajiya da Aishat ido suna masu mamaki da rud'u a cikin al'amarin Aishat jiki a sanyaye ta ce"Hajiya wannan hoton Mama na ne da Baba na sai d'ayan kuma Mama na ta ce Baba na ya ce mata Kakan ni na ne suke d'ayan". Cikin hanzari Hajiya ta mik'a hannu zuwa inda hoton ya ke ta d'auko tabbas ko makawa babu Lamid'o ne d'aya hoton kuma ita ce a ciki tana budurwa sai Lamid'o yana k'arami ya dai girma ba sosai ba sai Iyayensu dukkansu sanye suke da alkyabba wanda taji ado da k'ayatarwa cikin rashin fahimta ta ce"Aishat ban fahimce ki ba kina so ki ce min Lamid'o shine Mahaifin kuma kenan bai mutuba?". A fili ta ce"Aliyu to kodai in mutum ya mutu yana dawowa ne?". Aliyu ya kalli Hajiya tabbas bata hankalinta don a rud'e take. Aliyu cikin sassanyar murya ya ce"ai duk wanda ya mutu baya dawowa sai dai in daman bai mutum ba". A hankali ta sauk'e ajiyar zuciya ta ce"Aishat ina so ki bani labarin ki iya yanda Mahaifiyarki ta sanar dake". Ba tare da b'ata lokaci ba Aishat ta basu labari ta harzuwan Mamanta garin Bauchi, idon Hajiya cike da kwalla ta ce"tabbas ke 'Yar Lamid'o ne ga saida nan wannan awarwaron da kuma cewa Mahaifiyarki ta je Gombe ta nimi 'Yan uwansa da hoton nan ya isa sai da bare wasu sassan jikinki duk irin na Mahaifinki ne shiyasa ko da yaushe nake jinki a jikina tamkar 'Yar dana Haifa, a sai da 'Yata nake tare nan Hajiya ta fashe da kuka wanda itama Aishat kukan farin ciki takeyi Hajiya ce ta mata alamar tazo kusa da ita tana zuwa suka rungumi juna suna kuka zuwa wani lokaci suka tsagaita Hajiya ta kali Aishat ta ce"ke ba 'Yar shege bane da ake fad'a miki haka ke 'Yar gatace kuma 'Yar dangi kafin muje gimbe ya kamata ki san ko ke wacece kuma waye shi Muhammad Lamid'o". Haiydar ko yafi kowa farin ciki da bayyanan iyayen Aishat asai 'Yar uwansa ce kanwan sa tabbas sai yanzu yake jin kunyan zagin shegen da yamata tabbas yasan dole yanzu Hajiya ta k'ara hura masa wuta a kan Aishat don yasan yanda Hajiya take tsananin son d'an uwata Lamid'o bare ace yarsa dole ya k'ara kwantar da kai. Hajiya ta ce"Kamar yanda ki ka gani a hoton nan Mahaifin mu Sarkin Fulani ya kasance shahararen mai kud'i a cikin garin Gombe tun asalin Kakan mu shine sarkin Gombe kinga kenan wannan Sarautan tana k'ofar gidan mu ne lokacin da Kakan mu ya rasu sai ya zamana Mahaifin mu Sarkin Fulani bazaiyu a bashi Sarauta ba, sai aka d'auka aka bama Wazirinsa kinga daganan Sarauta ta bar gidan mu kenan ko da Mahaifin mu ya girma ba halin k'arban Sarauta sai aka bashi Sarkin Fulanin Gombe wanda alokacin matan sa biyu ne sai nice 'Yarsa ta farko kuma bai kara haihuwa daga kaina ba sai bayan shekara biyar aka Haifi Muhammad wanda ake kira da Lamid'o kasancewan shine d'a namiji d'aya ma Sarkin Fulani ya d'auki son duniya ya d'aura masa wanda hakan ya ke kona ran Kishiyar Hajiyan mu tun yana k'arami take kai masa hari da niyar kasheshi Allah bai bata sa'a ba har yasoma tashi, ana haka akayi aurena da Baban su Aliyu muna zama a cikin garin Gombe lokacin a gun yake aiki kafin mu dawo Bauchi da zama kasancewar shi d'an k'aramar hukuman Katagun ne da ke Bauchi, bazan manta da ranar da Abban mu ya dawo daga saudi ba rannan nazo gida masa murna da dangi duk mun had'u a gida".
*®NWA*
*DEDICATED TO*
*AISHAT MUHAMMAD*
*(MAMAN ABDUL SHAKUR)*
*RASH KARDAM*
0 comments:
Post a Comment