New Post

Wednesday, 16 August 2017

BABBAN KUSKURE.. 174-176

[7/7/2016] Rash Kardam ����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

Pg-174~176.

Sanah da Sadeey suka nufi class da Indo, ni ko Rash ina biye da su.
Tun shigarsu class, yan aji suka fara tambayan Sanah da Sadeey wacece?.
Sanah suka sharesu ganin sunyi hanyar sit d'in da ke k'usa dana su, wani yaro yace"kai new comer ce fa.
"Jiya ina gani aka kawo ta.
Wasu sukafara cewa ke kizo nan ki zauna, wani yaro yace"kai gaskiya tana da kyau.
"Zamu zama frds ko?.
Wani kalo Sanah ta musu, wanda yasaka shi yin shiru yana dariya.
Sit d'aya aka bata kasancewa kowa da sit d'insa, had'e da kuma lokansa na ajiye wasu littafa.
Sanah ce a farko sai sit d'in Indo a tsakiya sai Sadeey a baya. Ana haka Uncle d'in Biology yazo, darasin da yamusu shine. *CELL* sai da ya gama darasi yayi bayani sosai, ko da yazo yin Evaluation, ya tambayesu kamar haka, "class what is cell?.
Shiru ba wanda ya d'aga hannu, sai Indo ta d'aga hannu, ya nuna ta, Indo ta mik'e tafara cewa"Cell is the fundamental total unit of life. Cikin salon da take karatun, abun burgewa ne, bare muryanta tamkar mai yin busa. Tana gamawa tun kafin malamin ya bada umurni a tafa mata, 'yan class suka d'au sowa da tafi. Jikake raf raf raf, sannan malamin yace"well done good girl clapp for her once again.
A haka har aka tashi. School bus ne ya maidata gidan Hajiya.
Washe gari ta koma gidanta, Haka rayuwa taci gaba da tafiya, kulum school bus ke zuwa d'aukan Indo ya dawo da ita.
Sannu a hankali sun shaku dasu Sanah da Sadeey, anan ne ma take sani asai Sanah yar gidan bababn Malaman nan ne mai wa'azin biki da gyaran Amare. Sai Sadeey kuma gurin gayu ba'a barta a baya ba. Niko Rash nace"lalle abun yayi wato kaya, ya tsinke a gaban mai kaba.
Aisha ta soma kilewa, duk da haka ita take aiki a gidan Falmi, ko kad'an bata nuna gajiyawarta, Haiydar ko ya saba da girkinta duk randa bata gida, ko ya je Hotel baya iya cin abincin su.
Indo ko mungun kama kanta take bata bari ma ya ganta bare ya nimi takura mata.
Falmi ko bala'in yau da ban nagobe da ban, Meesha lurv da Zarah BB sun bata shawaran ta kama kanta, ta fita hark'ar Indo tak'i, sabida duk randa Indo ta waye sai ta gane KUSKURENTA amma fir taki, tana bin shawaran mugayen k'awayenta, hakan yasaka suka zuba mata ido.

               *DEDICATED TO*
         *AISHA MUHAMMAD*
    *(MAMAN ABDUL SHAKUR)*

              *RASH KARDAM��*

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts