New Post

Wednesday, 16 August 2017

BABBAN KUSKURE... 200-206

����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

               *®NWA.*

*Pg-200~203.*

Aishat da take ciki d'aki jin an kwan-kwasa k'ofa take cikinta ya bada sautin kululuuu! Wani fitsari ne ya taho mata bashiri ta sa hannu tana matse k'asan k'afarta duk a tunaninta Falmi ne, bata san lokacin da yanka bayi da mugun gudu ta kulle bayi sai ga fisari na gan-garowa ta k'asan k'afarta. Sai rarraba ido takeyi jin an kara buga k'ofar ae sai ga fitsari na zuba take idanunta suka soma ciko da kwalla addu'a ta fara karantowa duk wanda yaxo bakinta kawai yi takeyi.
Falmi  ko duk wani tugu da zata had'a ta had'a, bata soma shirin dawowa gida ba sai k'arfe tara da mintuna.
Haiydar jin shiru yayi yawa ba a bud'e ba da har zai tafi sai ya fasa, sunan Aishat ya kira sai da yayi baki uku. Aishat daga bayi taji muryan Haiydar da kamar bazata fito ba, amma sai ta daure tana d'an sand'a ta fito falo muryan shi taji, sai da ta tattara nutsuwarta ta amsa ta ce"gani ina zuwa". Bayi ta koma ta d'auraye jikinta ta fito zani ta d'aura kafin ta bud'e k'ofar. Haiydar ya ce"beauty ina kika shiga?". Sai da ta d'anyi jim kafin ta ce"na d'an shiga wanka ne shiyasa". Haiydar yayi murmushinsa mai k'ayatarwa ya ce"beauty shine bazaki kirani inzo na miki ba, bai kamata kina wahala da kanki alhalin gani a cikin gidan miye amfanina? Kin san bana so ki wahala da yawa". Haiydar ya karashe maganan tare da d'aga ma Aishat gira tare da kashe mata ido d'aya. Aishat ta kauda kanta gefe ta ce"bana bukatar hakan kuma da wake min wanka? Ko kaine kake min? Don haka bana bukatar hakan". Zai sake magana ta ce"wai lafiya kuwa? Ni fa zan rufe k'ofa don ina da abunyi". Haiydar ya san halinta da sauri ya mik'a mata ledar bata bari yayi magana ba ta ce"thanks you". (Nagode maka). K'ofar ta mayar ta rufe tare da sakin sassayan ajiyar zuciya ledar ta ajiye taje tayi wanka kafin tazo ta bud'e ledar sai da taci abinci dake ciki tayi hamdalah ta tattara kayan zata fitar waje nan fa ta tuna da abunda ya faru kamar zata koma ta ce"ai Haiydar yana gida ba zai bari ta bugen ba". A hankali ta bud'e k'ofar d'akin da sand'a ta ke tafiya, sai da tazo dai-dai falo ta d'an leka taga ba koma sai da ta leka hanyar d'akin Falmi taga ba kowa kafin ta fito sad'af-sad'af take tafiya har ta kai komai kitchen (madafi) tukun ta dawo nan ma sai da ta leka har tazo tsakiyar falo taji ance kee ba karanin razana tayi ba take kayan cikinta suka soma bada sauti shooky.

                 *®NWA*

               *DEDICATED TO*
         *AISHAT MUHAMMAD*
    *(MAMAN ABDUL SHAKUR)*

              *RASH KARDAM��*
[7/14/2016]Rash Kardam ����������������
����BABBAN KUSKEREN����
       ����DANA TAFKA ����
                 ������
                    ��������
                       
                       NA

©RASHEEDAH .A. KARDAM.

               *®NWA.*

*Pg-204~206.*

Kee taji ance bak'aramin razana tayi ba sai da kayan cikinta suka fara shooky. Duk ta gama d'auka Falmi ce harta had'a hannayenta biyu alamar zata bada hak'uri, a hankali ta juyo sai ganin Haiydar ne ke waya da alamar ransa na b'ace gashi kuma ya ganta ta rasa ya zatayi sai kawai ta wayance taci gaba da sand'ar sai ta d'an jiyo kamar mai wasa abinko sai ya mata kyau. Haiydar kasa d'auke idonsa yayi daga gareta harta shiga side d'inta. Aishat tana shiga ta sauk'e ajiyar zuciya bayi taje tayi brush tazo ta kashe wuta tayi addu'a ta kwanta.
Haiydr kasa tashi yayi a falon yana jiran yaga dawowar Falmi ransa ya gama b'aci sosai. Falmi ne tashigo da sallamarta ganin Haiydar ta b'ata rai itama tare da k'arasowa cikin falon, Haiydar cikin b'acin rai ya ce" kee daga ina kike?". Falmi bata tanka masa ba sai wani harare-harare takeyo, Haiydar ya ce"Falmi kinason ki b'atamin gidana don Aishat duk abunda taga kinayi shi zata koya wanda ni kuma bana so ko kad'an ta koyi munanan d'abi'unki". Wani harara Falmi ta b'alla masa tare da jan tsaki tayi d'akinta, da sauri ya bita ama kash! Ta sanya ma d'akin key(mabud'i). Ransa  ya gama b'aci bai san lokacin da ya fara safa-da-marwa a falo tare da dunkule hannusa ya bugi iska, da kyar yasamu ya koma d'aki ya kwanta zuciyarsa na masa suya.
Da safe da wuri Haiydàr ya fita Aishat ma ta shirya school bus yazo d'aukarta, ko da taje school da suka zauna da su Sanah ta basu labari abunda ya faru dariya sukayi sosai kafin suka bata shawarwari. Sai da aka tashi ta bi gidan Hajiya sai da tayi la'asar kafin ta d'au motar ta nufi gida daman a gidan ta bar motar. Tafe take tana tuk'i cikin nutsuwa tun daga unguwansu Haiydar taga kanar wata mota kirar jeep bak'a da glass bak'ak'e tana binta, sam bata kawo komai ba tayi ta tafiyanta sai da tazo hanyar shiga unguwansu bayan Airport taga wannan motar tazo da gudu tasha gabanta, gashi gurin bakowa shiru gurin wasu bak'ak'en mutane ne suka fito daga bak'ar  jeep d'in nan tare da zuwa dai-dai jikin motarta suka bud'e, cike da tsoro ta ce"lafiya mai na muku? Dan Allah kuyi hak'uri in motar kukeso in fita na baku amma kar kuyi min komai". Wani daga cikinsu ya wanka mata lafiyayen mari ya ce"zaki rufa min baki ko-ko sai kinji maza?". Take jikinta ya soma b'ari idonta sai ruwan hawaye ke zuba, d'aya daga cikin mutanen ya ce"yah! Oga zamu gama da ita a nanne?". Wani murmushi Ogan yayi ya ce" no zamu tafi da ita don naga ta min zata yi test(d'an-d'ano)dole sai na huta da ita kafin mu gama da ita. Aishat najin haka ta fara zatayi ihu d'ayan ya zaga ta bayanta ya mata kyakkyawan riko wani yazo manna mata salatab a baki, k'okarin janta suka somayi amma tana turjewa abunka da fatar mace mai samu hutu, garin janta taji ciwo a hannu sai ga jini yana zuba har saida ya d'idd'iga a gun. Ogan gani tana da taurin kai kuma zata b'ata musu lokaci yazo dai-dai ita cikin muryan 'Yan iska ya ce"tun da ki kayi taurin kaikuma ki ka b'ata mana lokaci kafin mu aiwatar da aikin da'aka samu sai nida Yarana mun biya buk'ata dake, bakinsa ya lashe tare da kawo hannusa ya shafi k'irjinta ya saki mayen murmushi haka suka jata zuwa motarsu suka tayar su ka bar gurin.

Ni Rash bansan lokaci da nasaki k'ara ina binsu ina kiran Haiydar amma ina sunyi nisa ba taimakon da zan iya bata a lokacin sai addu'a.

               *®NWA*

                *DEDICATED TO*
        *AISHAT MUHAMMAD*
   *(MAMAN ABDUL SHAKUR)*

 
               *RASH LUV��*

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts