[7/8/2016] Rash Kardam
BABBAN KUSKEREN
DANA TAFKA
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM
®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION.
Pg-180~183.
Da k'yar Haiydar ya iya jan k'afarsa, zuwa gun motarsa ya shiga.
Yana shiga motar sai da ya d'an zauna, don gabad'aya ganin Aisha, ya haddasar masa da kasala a jikinsa.
Kansa ya d'an jingina a steering motar, ya lumshe idanunsa, ba abun da ke gani illa fuskan Aisha, da suran jikinta, suna masa gizo a idonsa.
Imagine ya farayi, wai ga Aisha tazo, cikin tafiyarta mai burgewa, kusa da shi tazo, tana masa k'wark'wasa, sai da ta matso kusa dashi, kiss ta manna masa a baki.
Shiko sai wani murmushi ya saki, tare da k'ara lumshe ido, wayarsa ce tayi k'ara, sai da yaja karamin tsaki, don bai so ya katse tunanin da yakeyi ba.
Ni ko Rash nace"da ka tafi sabgar gaban ka ne, da zaifi maka wanna kayan jaki da karan.
"Don yanzu Indo ta maka nisa, yanzu Indo matar manya ce.
Wayarsa ya zaro, sunan Falmi ya gani akan scream d'in wayan, tsaki yayi kafin ya d'aga wayar.
Cikin muryansa da ba yabo ba fallasa yace"hello ya akayine?.
Daga b'an garen Falmi tace"Haiydar pls ka turan kud'i a cikin account d'ina, ina..... Bai bari ta k'arasa ba ya katse kiran.
Ransa duk ya gama b'aci, sai huci yakeyi, cikin zuciyarsa ko cewa yake"wai ya rinyan nan tana da hankali kuwa?.
"Bata san hakki na da ke kanta, ta sauke ba amma ta iya tambayan kud'i?.
"Rabon da Falmi ta zo d'akina na manta, wai sai kasuwanci ta saka a gaba.
"Dole in d'au mataki akan ta.
Motarsa ya ja ya fice abunsa, zuciyarsa ko sai zafi take masa, don shi yanzu ya gaji da halin Falmi, ta soma hawan masa kai sosai.
Aisha ko tana fita daga gidan, gidan Hajiya ta wuce, tana shiga ta perker motar ta fito. Masu aikin gidan sai sannu suke mata, cikin girmamawa ta amsa musu.
Cikin falon ta nufa, da sallamarta ta shiga falon, Hasna da ke goge TV da gudu tazo ta rungumeta, tace"haba Aunty eeshat kinanan kwana biyu?.
Aisha tace"washhh nikam sakeni karki karyani, gwamma ke.
Hasna ta saki dariya.
Aisha tace"Hasna ina Hajiyata ban ganta ba?.
Hasna tace"ta tafi dubiyar maralafiy.
Aishat tace"Allah ya dawo da ita lafiya.
Hasna ta kalli Aisha sama da k'asa tace"Baby Eeshat irin wannan wanka haka?.
"Gaskiya zaki rikita Yayana.
"Hmm Aishat duk gayuna yanzu kin d'aramin sosai, sai dai mu biyo bayanku.
Wani lalalusar mirmushi Aishat ta saki tace"ke ban son iskanci fa.
Hasna tace"gaskiya ne ae, ko da yake hausawa sunyi gaskiya da sukace, bakauye bai iya wayewa ba. Cikin zolaya tayi maganan, dariya suka saka dukkansu.
Aishat tace"barin je gidansu Sanah suna jirana zamuje saloon ne.
Hasna tace"okay! To sai kin dawo.
Har jikin motarta Hasna ta rakata, tashiga ta ja motar ta bar gidan.
Hmm masu karatu kenan Indo mu na da ne tawaye.
Gidansu Sanah ta shiga, tana ajiye motar tashiga gidan, Sadeey tace"ae na d'auka bazakizo ba.
Rausayar da kai Aishat tayi, tare da had'a hannu alamar ban hakuri, tace"tuba nake amin afuwa.
Sanah ne tafito da gyale suka wuce, sai yamma suka dawo, sai da ta ajiyesu a gida ta nufi gidanta.
Tun a harabar gidan, taga motar Haiydar yadawo, cikin zuciyarta ta fara tsara irin rikitasa da zatayi yau.
Tana shiga gidan bakowa a falo, side d'inta ta nufa, kaya ta cire tukun tayi wanka, saida ta tsane jikinta, tukun ta zauna a gaban madubi, ta kusa d'aukan awa d'aya tana k'waliya.
Three quarter ta d'auko tare da wani riga marar hannu, irin wanda ake d'auresa a wuya, rigan kalar ja, sai ta d'auko ribom ja ta d'aure kanta, bak'aramin k'yau tayi ba.
Main falo ta fito, sai da ta kunna CD, ta d'auko kaset d'in waka tasaka, don niman magana ta k'ure speaker, don ta san Haiydar baya son hayaniya sosai.
Kitchen ta shiga ta had'a zob'o, daman tayi girki kafin ta fita, a plate tasako a binci ta fito falo, ta zauna abinci taci ta k'oshi, ta tattara plate da cups d'in ta mayar kitchen.
Falo ta dawo sai da ta huta, ta je gun speaker ta k'ara volume a hankali tafara rawanta, cikin salon k'warewa take gir-giza jinkita.
Haiydar ko na bacci ya ji kid'a na tashi, har sai da ya toshe kunnesa, cikin masifa ya nufo falon, ko da ya iso falon kasa motsi yayi, don gani irin rawan da Aishat takeyi.
Aishat kuwa ganin Haiydar da gan-gan tasoma matsowa kusa da shi tana rawa.
®NWA.
*DEDICATED TO*
*AISHA MUHAMMAD*
*(MAMAN ABDUL SHAKUR)*
*RASH KARDAM*
0 comments:
Post a Comment